Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Najeriya ta daɗe tana fuskantar matsalolin tsaro, ta yadda a kullum al’amarin yake ƙara ta’azzara kuma daga dukkan alamu, lamarin ya gagari kundila.
A yankin Arewa, inda lamarin ya fi ta’azzara, an daɗe cikin masifar ‘yan Boko Haram, musamman a jihohin Arewa maso gabas, da suka haɗa da Borno, Yobe da sauransu.
A jihohin Arewa maso yamma kuwa, ‘yan bindigar daji sun daɗe suna satar mutane domin amsar kuɗin fansa da satar dabbobi da lalata amfanin gona.
A jihohin Arewa ta tsakiya ma, lamarin taɓarɓarewar tsaro ya ta’azzara. An daɗe ana samun rikice-rikicen da suka danganci na ƙabilanci, addini, makiyaya da manoma da ma na ‘yan bindiga masu satar mutane domin amsar kuɗin fansa.
A jihohin Kudu ma akwai matsalolin tsaro iri-iri, wannan kuwa sun haɗa da masu tada ƙayar baya, domin kafa ƙasar Biyafara da masu satar ɗanyen mai da ma masu satar mutane domin kuɗin fansa da sauransu.
Gwamnati a kullum tana kashe maƙudan kuɗaɗe, domin magance matsalolin tsaron amma kamar tana saran ruwa. To, ta yaya za a magance wannan babbar matsala ta tsaro da ta addabi al’ummar ƙasa? Sanata mai wakiltar Kudancin Borno, Mohammed Ali Ndume, a yayin tattaunawa da BBC Hausa a ƙarshen makon da ya gabata, ya bayyana wasu hanyoyi, waɗanda ya ce idan aka bi su, za a magance wannan matsala.
Sanata Ndume, a matsayinsa na jigon siyasa, wanda kuma ya fito daga Jihar Borno, inda aka daɗe ana fuskantar matsalar ‘yan Boko Haram ya bayyana hanyoyi huɗu kacal, waɗanda ya ce idan aka bi su, za a magance matsalolin tsaro a ƙasar nan.

Ya kawo kalmar Turanci ta “TEAM” a matsayin ƙunshiyar maganin matsalar tsaro a Najeriya. “T-Training (Horarwa), E-Equipment (Kayan Aiki), A-Ammunition (Makami) da kuma M-Motivation (Kyautatawa) su ne hanyoyi huɗu da ya kamata gwamnati ta bi, domin magance matsalolin tsaro da suka daɗe suna addabar ƙasarmu,” in ji Sanata Ndume.
Da yake ƙarin bayani dalla-dalla game da waɗannan hanyoyi huɗu, Sanatan ya ce, hanya ta farko ita ce, gwamnati ta dage sosai wajen horar da jami’an tsaro, domin su samu ƙwarewa sosai wajen hikimomi da dabarun daƙile aniyar masu laifi da gano su.
“Hanya ta biyu, ita ce gwamnati ta samar wa jami’an tsaro kayan aiki na zamani. Waɗannan sun haɗa da ingantattun motocin sufuri, na’urorin bincike na zamani da sauransu.” Sanatan ya ƙara da cewa, samar da kayan aiki na zamani ita ce hanya mafi sauƙi ta magance tsaro, wacce ta dogara da kimiyya da fasaha.
Hanya ta uku kuwa, Sanata Ndume ya ce, gwamnati ta zage damtse ta samar wa jami’an tsaro makaman yaƙi na zamani kuma wadatattu.
“Hanya ta huɗu kuwa,” in ji shi “ita ce a kula tare da kyautata rayuwar jami’an tsaro. Gwamnati ta tanadar wa jami’an tsaro da ingantacce kuma wadataccen albashi da alawus-alawus. A kula da lafiyarsu, ilimi da muhallinsu da na iyalansu.”
Sanatan ya sha alwashin cewa zai ci gaba da aikinsa na shawartar gwamnati da shugabannin tsaro, domin ganin an samar da ingantaccen tsaro a ƙasar nan.
__________











