• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, September 21, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Gobara Daga Kogi: Malamin Islamiyya Ya Lalata Ɗalibansa 9 Da Luwaɗi

BABBAN LABARI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
December 14, 2025
in Babban Labari
0
Gobara Daga Kogi: Malamin Islamiyya Ya Lalata Ɗalibansa 9 Da Luwaɗi

Allah ka kiyashe mu da mugun ji da mugun gani!

57
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Gobara Daga Kogi: Malamin Islamiyya Ya Lalata Ɗalibansa 9 Da Luwaɗi

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
Sanarwar: Wannan hoto samfoto ne aka ƙirƙira da Fasahar AI. Allah ka kiyashe mu da mugun ji da mugun gani!


                              •••••••
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!
A makon da ya gabata ne aka samu wani mummunan lamari da ya faru a Abuja, inda aka samu wani malamin Islamiyya da tuhumar lalata ɗalibansa guda tara da luwaɗi.

Lamarin, wanda za mu danganta shi da gobara daga kogi, maganinta Allah, Ordinary President, Dokta Ahmad Isah tare da ma’aikatansa ne suka gudanar da bincikensu, a sashen Hausa na gidan rediyon Human Rights Radio, Abuja.

A shirin, an gabatar da yaran su 9, waɗanga suka kasance ‘yan shekara 10, 11 zuwa 12 kuma kowannensu ya yi bayani dalla-dalla, ya fayyace yadda malamin ya riƙa yaudara da tsorata su, ya riƙa kai su gidansa yana wannan aika-aika, har zuwa wannan lokaci da asirinsa ya tonu.

Babu shakka wannan lamari ya yi muni matuƙa, domin kuwa wasu daga cikin yaran, ana zargin sun kamu da cuta, domin suna wahala wajen zama da mazaunansu. Akwai ƙunci da ciwo ga iyayen yara, su tura ‘ya’yansu wurin da suke zaton aminci da tarbiyya da addini, amma wurin ya rikiɗe zuwa inda za a lalata masu rayuwa!

A Musulunci, luwaɗi babban zunubi ne mai muni, wanda ya saɓa wa halittar da Allah ya yi wa ɗan Adam. Wannan abu da mutumin nan ya aikata ga waɗannan ƙananan yara, laifi ne, zalunci ne kuma cin amana ne da ba za a taɓa yarda da shi ba. Wannan mummunar ɗabi’a tana lalata tarbiyya, tana ɓata rayuwar yara, tana kuma iya ɓarar da rayuwar al’umma gaba ɗaya.

Alƙur’ani ya yi bayani a fili game da munin wannan aiki. A cikin Suratul A’araf, aya ta 81, Allah Maɗaukakin Sarki ya ce game da mutanen Annabi Luɗ (AS): “Kun zo wa maza domin sha’awa maimakon mata. A’a, ku mutane ne masu wuce gona da iri.”

Haka kuma Manzon Allah (SAW), a hadisin Tirmizi da Ibn Majah ya ce: “Ku kashe mai aikata luwaɗi da wanda aka yi wa.” Wannan ya nuna irin girman zunubin, domin babu wani laifi da aka yi bayani da tsanani irin haka face kaɗan.

Game da illolin da ke tattare da luwaɗi ga al’umma kuwa, laifi irin wannan ba wai kawai yana ɓata tarbiyya da mutunci ba ne, yana kuma iya haddasa cututtuka, lalata ƙwaƙwalwa da tsarin tunani. Yana kuma jawo tsanar iyaye da rashin kwanciyar hankali a cikin gida. Yaran da aka zalunta da wannan mummunan aiki, sukan girma cikin tsoro, damuwa ko rikicewar ɗabi’a. Munin wannan aiki babba ne kuma abin tsana ne ga al’umma musulma. Ya zama dole mu tsare amanar `ya’yanmu da mutuncinsu.

Musulunci ya umurci jama’a su riƙa hana juna masha’a, su zama masu tsare ‘ya’ya, tsarkake muhalli da kula da ƙananan yara. A wani hadisi da Bukhari da Muslim suka ruwaito, Manzon Allah (SAW) ya ce: “Dukkanku makiyaya ne kuma kowane mutum za a tambaye shi kan abin da yake kiyayewa.” Wajibi ne a wayar da kai cikin makarantu, masallatai da gidaje domin ceton ‘ya’ya daga hannun masu mugun nufi irin wannan malami na Islamiyya.

Ya zama wajibi ga hukumomi watau ‘yan sanda, kotuna, lauyoyi da ma’aikatar jin ƙai da kariyar yara, su tabbatar da cewa an hukunta mutumin da ya aikata wannan mummunan laifi. Hakan zai zama izina kuma domin kare al’umma, koya darasi da tabbatar da cewa irin wannan ƙazamar ɗabi’a ba ta sake samun gindin zama a cikin al’ummar Musulmi ba.

Ya Allah ka kare ‘ya’yanmu, ka tsare al’ummarmu daga fitina. Ka kuma shiryar da masu aikata irin waɗannan munanan ayyuka zuwa turba ta gaskiya. Amin.
_______________

Previous Post

Dokta T.S SAULAWA: Hadimin Al’umma A Koyaushe

Next Post

Philip Chikwuedo Asiodu: A Legacy of Dedication and Service

Related Posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?
Babban Labari

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta
Babban Labari

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya
Babban Labari

KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya

August 29, 2026
Next Post
Philip Chikwuedo Asiodu: A Legacy of Dedication and Service

Philip Chikwuedo Asiodu: A Legacy of Dedication and Service

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Kishin Ƙasa Ne Tubalin Farko Na Gina Rayuwar Al’umma (2)

Barkwancin Ƙarshen Mako

July 22, 2023
KIRA NA MUSAMMAN GA JAMI’AN TSARO A MALUMFASHI

KIRA NA MUSAMMAN GA JAMI’AN TSARO A MALUMFASHI

August 3, 2024
Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

February 13, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.