• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, May 12, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Dokta T.S SAULAWA: Hadimin Al’umma A Koyaushe

TSOKACINMU NA MAKO

Aliyu Adamu by Aliyu Adamu
December 13, 2025
in Gizago
0
Dokta T.S SAULAWA: Hadimin Al’umma A Koyaushe

Dokta Tasi'u Salisu Saulawa

27
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Dokta T.S SAULAWA: Hadimin Al’umma A Koyaushe

Daga Aliyu Adamu

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Dokta Tasi’u Salisu Saulawa


                       _______________
Fitaccen marubucin wasan kwaikwayo kuma jigon adabi na duniya, William Shakespeare, a cikin ɗaya daga littattafansa, ya kwatanta duniya da tamkar wani mataki ne da jarumi ke taka rawarsa ya gama, ya bar wa wani. Haka kuma, a cikin wannan littafi, marubucin ya ƙara da cewa: “Jarumi ba ya ɗanɗana mutuwa, kuma idan ma ya dandana, sau ɗaya ne kacal a rayuwa.”

Wani fitaccen marubucin kuma masanin falsafa, Robert Green, a cikin littafinsa, 48 Laws of Power (Dokokin Mulki 48), ya fayyace doka ta tara da cewa: “Ka nemi samun nasara ta ayyukanka, ba ta gardama ba.” Marubucin ya ƙara da cewa, duk wata nasarar da ka samu ta hanyar gardama, nasara ce gajere, wacce ba ta ɗorewa. Dalili kuwa shi ne, wannan nasara za ta haifar da fushi da baƙin ciki mai girma ga mutane, musamman waɗanda ka kasa ta hanyar gardama.

Abin nufi dai shi ne, ya fi tasiri idan ka samu nasara, mutane suka yarda da kai ta ayyukanka kai tsaye, ba tare da cacar baki ba. Ma’ana dai, aikinka ya nuna, ba magana ba.

A gefe guda, a kowace al’umma ko gari, ana samun mutane waɗanda suka fi amfanar al’ummarsu. Sau da yawa akan gano cewa wasu mutane suna da rawar da suke takawa wajen gina al’ummarsu ta hanyar ayyukansu na yau da kullum ko na lokaci-lokaci.

A nan ne asalin wannan rubutu yake son mayar da hankali – ga wani mashahurin mutum mai ingantattar hallayyar kyautata wa al’umma. Wannan taliki, za mu iya kiran shi da ‘Matashin Dattijo.’ Domin kuwa duk da cewa da kaɗan ya wuce shekara 40 amma halayensa da ɗabi’unsa sun yi kama da na mutumin da ya zarce shekaru 60 zuwa 70. Mutum mai sanin ya kamata, mai kyautata wa al’umma da yi masu hidima ba tare da neman wata ijara ba. Shi ne mai ƙoƙarin inganta rayuwar mabuƙata, marayu da raunana a cikin al’umma.

Muna magana ne dangane da abubuwan burgewa da farin ciki da Mataimakin Kwanturola na Hukumar Kwastam ta Najeriya, Dokta Tasi’u Sanusi Saulawa ya jima yana gabatarwa a tsawon shekaru. Mutum ne da ya jajirce wajen kyautata wa al’umma ba tare da gajiyawa ba. Shi ne mai zumunci da inganta rayuwar abokansa, abokan aikinsa, abokan hulɗarsa, ‘yan uwa da abokan arziƙi. Ya kasance na sahun gaba ta fannoni mabambanta na alheri kuma yana aikata haka ba tare da wata shakka ko gajiyawa ba.

A haƙiƙanin gaskiya, Dokta Saulawa ya ɗauki nauyin marayu fiye da sittin da kuma inganta rayuwar matasa da marasa galihu da dama a faɗin Katsina da kewaye. Wani babban abin farin ciki shi ne, da dama daga cikin waɗannan matasa sun samu kammala karatun Diploma da NCE. Bugu da ƙari, wannan gwarzo mai taimakon jama’a, ya gyara, inganta da tallafa wa tsohuwar makarantarsa ta Nagogo Model Primary School Katsina; inda ya samar da kwamfutoci guda ɗari ɗaya da kayan haɗinsu da kayan koyarwa masu daraja na dubban nairori.

Wani muhimmin tallafi na musamman da Dokta Saulawa ke bayarwa, shi ne ta ɓangaren ƙarfafa matasa da mata, inda da dama a faɗin Katsina suke amfana da tallafin jari daga gare shi, domin su samu kafar dogaro da kansu; su zama masu amfani ga al’umma, su kuma inganta rayuwarsu.

Baya ga haka, Mataimakin Kwanturola Dokta Saulawa ya yi ƙoƙari tare da jajircewa wajen kafa ƙungiyar haɗin kai da tallafa wa matasa. Ta wannan ƙungiya, fiye da matasa 110 sun samu tallafi da ci gaba a shekarar 2024, suka zama masu dogaro da kansu. Wannan ya yi daidai da hikimar da ke cewa “Idan ka ƙarfafa matasa a yau, ka ƙarfafa gobensu ke nan.”

A taƙaice, Dr. T.S. Saulawa ya zama mai mutunci da karimci kuma abin koyi a idon al’umma da dama. Duk wanda ya samu mu’amala da shi, ta nesa ko ta kusa, za ka ji ya ba da shaida ta alheri a kansa. Babu shakka Katsina da al’ummarta suna buƙatar muhimmin mutum irin Dokta Saulawa, domin amanarsa da burinsa na yi wa al’umma hidima.

A yayin da muke wa Dokta Saulawa fatan alheri a kowane lokaci, muna addu’ar Allah Madaukakin Sarki da ya ƙara masa tsawon rai, yalwar arziki da lafiya kuma ya ba shi ikon cigaba da yi wa al’umma hidima a faɗin Jihar Katsina, a duk matsayi ko muƙamin da Allah ya nufa a gare shi.
_______________

Previous Post

Dr. T.S Saulawa: Beckons to Serve

Next Post

Gobara Daga Kogi: Malamin Islamiyya Ya Lalata Ɗalibansa 9 Da Luwaɗi

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
Gobara Daga Kogi: Malamin Islamiyya Ya Lalata Ɗalibansa 9 Da Luwaɗi

Gobara Daga Kogi: Malamin Islamiyya Ya Lalata Ɗalibansa 9 Da Luwaɗi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Review of AJN Tremearne’s Publication   Hausa Superstitions and Customs

Review of AJN Tremearne’s Publication  Hausa Superstitions and Customs

February 21, 2026
THE CONCEPT OF CHRISTIANITY According to Reno Omokri

THE CONCEPT OF CHRISTIANITY According to Reno Omokri

September 23, 2023
Literature in Northern Nigeria: Past, Present and the Future

Literature in Northern Nigeria: Past, Present and the Future

November 2, 2023
FAUZIYYA ƊANLADI SULEIMAN: Tattaunawa Da Uwar Marayu Da Raunana

FAUZIYYA ƊANLADI SULEIMAN: Tattaunawa Da Uwar Marayu Da Raunana

September 3, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)
  • Malumfashi An Yi Babban Rashi
  • Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)

May 12, 2026
Malumfashi An Yi Babban Rashi

Malumfashi An Yi Babban Rashi

May 11, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.