• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, May 12, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

GOBARA DAGA KOGI: ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Fadar Gwamnatin Amurka

• Sun Harbe Sojoji Biyu

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
November 27, 2025
in Babban Labari
0
GOBARA DAGA KOGI: ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Fadar Gwamnatin Amurka

Dakarun National Guard a bakin aiki

28
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

GOBARA DAGA KOGI: ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Fadar Gwamnatin Amurka

• Sun Harbe Sojoji Biyu

Related posts

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

May 9, 2026
Yan ta’addan Daji Kafirai Ne  – Sarkin Musulmi

Yan ta’addan Daji Kafirai Ne – Sarkin Musulmi

May 8, 2026

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Dakarun National Guard a bakin aiki


                       __________
An rufe Fadar Gwamnatin Amurka (White House), a yayin da wasu ‘yan bindiga suka farmaki fadar, suka yi ta musayar harbi da sojojin da ke gadi, inda har wasu jami’an soja biyu na Rundunar National Guard aka yi zargin sun rasa ransu.

Gwamna Patrick Morrisey a farko ya bayyana cewa sojojin sun rasu, amma daga baya ya ce yana samun “bayanan da ke karo da juna” game da yanayin lafiyar dakarun biyu, inda ya ƙara da cewa, za a fitar da ƙarin bayani idan an tabbatar.

Gwamnan, a shafinsa na X ya bayyana cewa: “Yanzu muna samun bayanai masu karo da juna game da halin da dakarun sojojinmu biyu suke ciki kuma za mu bayar da ƙarin bayani idan mun samu cikakkar hujja.

“Muna addu’a ga waɗannan jaruman dakaru, iyalansu da al’ummar Rundunar National Guard baki ɗaya.”

Rahotanni sun nuna cewa Shugaba Donald Trump yana gidansa na Mar-a-Lago da ke Palm Beach, Florida, a lokacin faruwar lamarin.

A wata sanarwa, sakatariyar yaɗa labaran Fadar White House, Caroline Leavitt, ta ce: “Fadar White House ta samu labari, tana kuma bibiyar wannan mummunan lamari. An yi wa Shugaban Ƙasa bayani.”

’Yan sandan Metropolitan na DC sun ce an kama wanda ake zargi da haddasa harbe-harben.

Dakarun National Guard sun shafe watanni a Washington DC a wani yunƙuri na Trump na ƙarfafa yaƙi da laifuka a babban birnin ƙasar. A shafinsa na Truth Social, Trump ya ce: “Dabban nan da ya harbi sojojin National Guard biyu, waɗanda duk suna cikin hali mai tsanani, suna kwance a mabanbantan asibitoci; shi dabban ya jikkata sosai kuma duk da haka, zai fuskanci mummunan hukunci.”

Sharhi:
Wannan lamari, shi ake kira gobara daga kogi, wai maganinta Allah. Kuma hakan ke nuna mana cewa ashe lamarin taɓarɓarewar tsaro ba ga Najeriya ne kaɗai ba, har da manyan ƙasashe, irin Amurka, wacce ake gani kamar giwar duniya.

Wannan lamari ya faru ne fa, a daidai lokacin da Shugaba Donald Trump yake bugun ƙirji da barazanar cewar zai farmaki Najeriya, saboda taɓarbarewar tsaro. Kodayake shi a nasa batun, akwai son zuciya a ciki, inda ya yi ƙazafin cewa Kiristoci kaɗai ake yi wa kisan-ƙare-dangi a Najeriya. Kowa kuma ya san ba haka ba ne.

A yanzu da balahirar guguwar rashin tsaro ta farmaki Fadar Amurka, to yaya ke nan! Anya kuwa mai bunu a gindi, yana da zarafin kai wa wani gudunmawar kashe gobara?

Gare ku jama’a: Yaya kuke kallon wannan lamari? Ku bayyana a Comment Section.
__________

Previous Post

SHEIKH ƊAHIRU USMAN BAUCHI: Babban Bangon Musulunci Ya Faɗi

Next Post

Jama’a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban

Related Posts

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi
Babban Labari

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

May 9, 2026
Yan ta’addan Daji Kafirai Ne  – Sarkin Musulmi
Babban Labari

Yan ta’addan Daji Kafirai Ne – Sarkin Musulmi

May 8, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Babban Labari

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Next Post
Jama’a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban

Jama'a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Army Chiefs Issue Strong Warning to Sahara Reporters Over Allegations

Zargin Tallafa Wa Ta’addanci: Hafsoshin Soja Sun Aika Kakkausan Gargaɗi Ga Sahara Reporters

December 8, 2025
BATUN SULHU DA ‘YAN TA’ADDA A JIHAR KATSINA: Abin Da Ya Kamata A Fahimta

BATUN SULHU DA ‘YAN TA’ADDA A JIHAR KATSINA: Abin Da Ya Kamata A Fahimta

September 19, 2023
Nigeria 2027: The Best Way to Defeat President Tinubu

Nigeria 2027: The Best Way to Defeat President Tinubu

August 10, 2025
Barkwancin Ƙarshen Mako

Barkwancin Ƙarshen Mako

July 30, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)
  • Malumfashi An Yi Babban Rashi
  • Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (12)

May 12, 2026
Malumfashi An Yi Babban Rashi

Malumfashi An Yi Babban Rashi

May 11, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.