• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, January 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Sharhi A Kan Sharhi: Nazari da Sharhin Ayyukan Adabin Bukar Usman

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

webmaster by webmaster
May 29, 2023
in Adabi, Sharhi
0
Sharhi A Kan Sharhi: Nazari da Sharhin Ayyukan Adabin Bukar Usman
65
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Sunan Littafi: My Literary Works: Reviews and Reports (Ayyukan Adabina: Sharhi, Nazari da Rahotanni Game Da Rubuce-Rubucena)
Marubuci: Bukar Usman
Kamfanin Wallafa: Klamidas Communications Ltd. Abuja
Shekarar Wallafa: 2022
Yawan Shafuka: 1,126
Farashi: Ba A Bayyana Ba

A tarihin duniya gaba ɗaya, babu wani lokacin da aka saka littafi a baya. Ma’ana, a kowane zamani kuma a kowane lokaci, al’umma na saka karatu da karantarwa a sahun gaba, domin kuwa da ilimi ne ake tafiyar da kowane al’amari na rayuwa. Dalilin ke nan a yau, bayan samuwar wannan littafi na My Literary Works: Reviews and Reports (Ayyukan Adabina: Sharhi, Nazari da Rahotanni Game Da Rubuce-Rubucena), muka ga ya dace mu yi nazarinsa tare da gabatar da bunƙasasshen sharhi, domin fayyace namijin ƙoƙarin da Dokta Bukar Usman ya yi, wajen taskace ɗimbin ilimin da ya shafi falsafa, adabi da fasahohin al’ummomin wannan shiyya, domin haskaka da ƙara ilimantar da al’umma na wannan zamani da ma masu zuwa nan gaba a kusa da can nesa.

Related posts

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

December 6, 2025

Wannan bunƙasasshen littafi, kamar yadda takensa ya nuna, yana ƙunshe ne da nazarce-nazarce, tsokace-tsokace da sharhe-sharhe a kan littattafai kimanin 40, waɗanda Dokta Bukar Usman OON ya wallafa a tsawon shekaru 24, littattafan da suka shafi adabi, sha’anin mulki, sha’anin aikin gwamnati, siyasa da falsafar rayuwa da sauransu. Haka kuma waɗannan nazarce-nazarce sun fito ne daga masana na fannononin ilimi daban-daban, waɗanda suka haɗa da malaman jami’a, manyan jami’an gwamnati, ƙwararrun ma’aikatan kamfanoni, ’yan jarida da sauransu, waɗanda suka nazarci littattafan na Dokta Bukar.

 

Dakta Bukar Usman, Mawallafin Littafin My Literary Works: Reviews and Reports

Babu mamaki shi ya sanya ma marubucin ya sadaukar da littafin ga ɗaukacin “dukkan waɗanda suka taimaka ta kowace hanya wajen ganin samuwa da tabbatauwar katafanin littattafaina,” kamar yadda marubucin ya bayyana a shafi na 7.
Wani babban al’amari da ya ɗauki hankalina dangane da littafin nan shi ne, wata kyakkyawar halayya da tawali’u na marubucinsa, Dokta Bukar Usman. Ya nuna haka ƙarara a shafi na 17 zuwa na 19, a yayin da yake godiya ga ɗaukacin dukkan waɗanda suka taimaka ko suka ba da gudunmowa domin samun nasarar rubuce-rubucensa. Waɗannan kuwa sun haɗa da manyan malaman jami’a da manyan ma’aikatan gwamnati da kamfanonin ɗab’i da ‘yan jarida da marubuta, kai har zuwa ga masinjojin da yake aike nan da can, sai da ya kama sunayensu, ya yi masu godiya. Wannan halayya ce ta mutumin ƙwarai, wanda ya san mutuncin mutane kuma ya san ƙimar ilimi.

Idan ka ɗebe gabatarwar da shi kansa marubucin littafin ya yi a shafi na 21 zuwa na 22, ka tsallaka zuwa shafi na 23 zuwa na 26, inda shahararren masani, tsohon Jakadan Najeriya a Canada, Farfesa Iyorwuese Harry Hagher, OON, ya yi tsokaci game da muhimmanci da ɗimbin darajar littafin nan; lallai mai karatu zai fahimci inda littafin ya sa gaba kuma zai gane irin gagarumin aikin da aka yi wa al’umma a cikinsa.

Daga ƙarshen tsokacin nasa, ga abin da yake cewa: “Ya kamata a rarraba littafin nan na sharhi ɗakunan karatu, cibiyoyin kula da littattafai da ɗakunan binciken ilimi a ko’ina cikin duniya. Haka kuma baya ga wannan, mutum ya sanya wa zuciyarsa ta aminta da cewa wajibi ne ya nazarci littattafan Bukar Usman, musamman ma ga ɗaukacin ɗaliban ilimi a Najeriya. Sannan kuma lallai ne a saka su cikin tsarin koyo da koyarwa a makarantu da kwalejoji. Abin kunya ne a ce wasu ƙasashen Afirka ne ke tseren cin gajiyar littattafansa fiye da Najeriya. Don haka lokaci ya yi da Najeriya za ta farka daga barci, tun kafin lokaci ya ƙure mata.”
Littafin nan fa shaƙundum ne, domin tun daga shafukan gabatarwa mai karatun zai fara amfana da mulamulan ilimi. Ɗauki misalin shafi na 27 zuwa na 38, inda shugaban kamfanin wallafa na Klamidas, Duve Nakolisa ya baje kolinsa a matsayin gabatarwa. Masanin yi dogon tambihi, ya shayar da ɗaliban adabi madarar ilimi. Abubuwan da ya tattauna sun haɗa da muhimmancin sharhin littafi da tasirin taskace littafi a kimiyance. Ya sanar da dalilin ma da ya sanya ake yin sharhin littafi da kuma hikimomin da ake kimsawa a cikin nazari da sharhin littafi. Shin ko kun san abubuwan da mai sharhin littafi ke dubawa idan ya tashi yin sharhi ko nazarin littafi? Masanin ya kawo su dalla-dalla.

Baya ga wannan, ya kuma zayyana ire-iren sharhe-sharhen da ke akwai a fagen nazarin littafi, waɗanda suka haɗa da taƙaitaccen sharhi, sharhin ƙwaƙwaf, sharhin da’irar ilimantarwa da sauransu. Haka kuma a matsayinsa na shugaban kamfanin da ya yi aikin wallafa littafin nan, bai yi ƙasa a gwiwa ba, sai da ya kawo dalilan da suka sanya aka samar da wannan littafi na nazarce-nazarcen ayyukan adabi na Dokta Bukar.
Wata fasaha da marubucin littafin nan ya samar, ita ce dubararsa ta karkasa ƙunshiyarsa zuwa kashi 4, sannan ya sake karkasa kowane kashi zuwa sassa daban-daban. Yin wannan ya sauƙaƙa wa mai karatu ko nazari, yadda zai zaɓi darasi ko sashin da yake son nazarta, kasancewar kowane kashi ko sashi na ɗauke da maudu’ai da suka dace da shi.

Kashi na farko yana ƙunshe da sassa 7 kuma ya faro daga shafi na 42, ya ƙarƙare a na 538. Bisa ga wannan tsari, sashi na farko yana ɗauke da sharhi da nazarce-nazarcen masana dangane da littafin tarihin rayuwar Dokta Bukar Usman mai suna Hatching Hopes (Cikar Buri). Sai kuma ayarin sharhi da nazarce-nazarcen littafinsa da ya yi bayanin tarihin fara rubuce-rubucensa, mai taken, My Literary Journey suka biyo baya. Haka kuma sai rukunin sharhohin littafinsa na My Public Service Journey, wanda ya fayyace tarihin aikinsa na gwamnati tun daga farko har zuwa lokacin da ya aje aiki.

A sashi na biyu kuwa, an samar da sharhi da nazarce-nazarcen waɗannan littattafai: Voices in a Choir da Public Policy Formulation in Nigeria: Challenges and Prospects da littafin Issues and Challenges of National Security da Restructuring Nigeria: An Overview. Sauran sun haɗa da Press, Policy and Responsibility. Dukkan waɗannan littattafai na Dokta Bukar suna ƙunshe ne da bayanan da suka shafi al’amuran mulki, zamantakewar al’umma, aikin gwamnati, aikin jarida da siyasa da sauransu.

Idan muka matsa zuwa sashi na uku kuwa, za mu yi tozali ne da nazarce-nazarce da sharhohin waɗannan littattafai na Dokta Bukar: Girl-Child Education in Nation Building: The Early Years da Language Disappearance and Cultural Diversity in Biu Emirate da kuma The History of Biu. Waɗannan littattafai suna bayani ne gaba ɗaya dangane da al’amura da tarihin Biu – mahaifar Dokta Bukar Usman, marubucin littattafan.

Sashi na huɗu kuwa yana ɗauke ne da nazarin littattafan da Bukar ya rubuta, waɗanda suka ta’allaƙa ga bayani kan al’adu da fasahohin al’umma da kuma dimokuraɗiyya. Waɗannan kuwa su ne Folklore and History: Twin Rivers of World Heritage da kuma Language, Technology and Democratic Culture.
Idan muka matsa zuwa sashi na biyar a littafin nan, za mu ga yadda aka yi fashin baƙin littattafan Bukar Usman da suka jiɓinci tatsuniyoyi a harshen Ingilishi. Waɗannan kuwa sun haɗa da The Bride Without Scars and Other Stories da The Stick of Fortune da kuma littafin Girls in Search of Husbands.

Shi kuma sashi na shida na littafin nan, ya maida hankali ne a kan jerin littattafan da Dokta Bukar ya rubuta, waɗanda suka shafi tatsuniyoyi, al’amara da hikayoyin ƙabilun Najeriya. Littattafan da masana suka yi wa sharhi a wannan sashi su ne: A Selection of Nigerian Folktales da People, Animals, Spirits and Objects: 1000 Folk Stories of Nigeria da Gods and Ancestors: Mythic Tales of Nigeria.
Sai kuma sashi na bakwai kuma na ƙarshe a kashi na farko na littafin nan, inda aka maida hankali kan littattafan da Bukar ya rubuta cikin Hausa da Ajami. Duk da cewa sharhohin da nazarce-nazarcen littattafan an wallafa su ne da Hausa da Ajami a jaridu da mujallun Hausa daban-daban amma a littafin nan, an kawo su ne cikin Ingilishi. Littattafan kuwa sun haɗa da Marainiya Da Wasu Labarai, Jarumin Sarki, Yarima Da Labi, Tsurondi, Sandar Arziki da kuma Ɗankutungayya. Sauran sun haɗa da Gwaidayara, Ɗan Agwai Da Kura, Marainiya Da Muguwar Kishiya, Taskar Tatsuniyoyi da kuma littafin Taskar Tatsuniyoyi Cikin Ajami.
Kamar yadda aka bayyana a baya, kashi huɗu aka raba littafin nan, don haka kashi na biyu ya faro ne daga shafi na 539 kuma ya ƙarƙare a 598. A wannan gida, Dokta Bukar Usman ya tabbatar da irin kaifin basira, ilimi da baiwar rubutu da Allah Ya ba shi. Domin kuwa shi ma ya rikiɗe zuwa mai sharhi da fashin baƙin littattafai. Kan haka ya baje kolin nazari, sharhi da tsokacin da ya gabatar a kan wasu muhimman littattafai guda tara, waɗanda akasarinsu suke ƙunshe da tarihin rayuwar wasu muhimman mutane ‘yan kishin ƙasa, waɗanda su ma, kamar yadda shi ya kasance, sun hidimta wa al’umma a rayuwarsu, don haka rayuwar tasu ta kasance jagora kuma abin koyi ga al’umma na yanzu da ma masu zuwa nan gaba.

Na farko a jerin litattafan guda tara shi ne, Profile in Courage, na tarihin rayuwar muzakkarin soja, Manjo-Janar Paul Chabri Tarfa, mai ɗauke da shafuka 438. Wannan jarumin soja, an haife shi a watan Agusta na shekarar 1941, kuma ya zuwa rubuta sharhin nan (20-5-2023) yana raye.
Littafi na biyu shi ne Sunday Awoniyi: Selected Speeches & Writings, wanda yake ƙunshe da wasu zaɓaɓɓun jawabai da rubuce-rubucen shahararren ɗan Arewa, Sakataren Sardauna Ahmadu Bello, Sunday Awoniyi. A sharhin ne Bukar ya fito da kyawawan halaye da himma da kishin ƙasar wannan gwarzo, wanda ya rayu cikin hidima ga al’umma, wanda ya zo duniya a ranar 30-4-1932, ya rasu a 28-11-2007.

Littafi na uku a ragayar sharhin Dokta Bukar, shi ne For God and Country, wanda ke ƙunshe da muhimman jawabai da laccocin fitaccen ma’aikacin gwamnati, Cif A.K. Horsfall, wanda shi da kansa ya rubuta shi, aka wallafa domin taya shi murnar cika shekara 70 a duniya.

Littafi na huɗu shi ne mai taken Floreat Collegium: 100 Years of King’s College, Lagos. Littafi ne da ke ƙunshe da bayanan shahararrar Kwalejin King’s da ke Legas, wacce ta shekara 100 da kafuwa kuma ƙungiyar tsofaffin ɗalibanta ne suka samar da littafin, shi kuma Bukar a matsayinsa na ɗaya daga ɗalibanta, ya rubuta wannan sharhi.

Sai kuma na biyar, Third Edition of Baka Songs Anthology. Dokta Bukar ya rubuta wannan sharhi ne dangane da littafin Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, mai taken Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i na Uku.
Littafi na shida shi ne, Humility and Service: The Life of Alh. Ibrahim Biu, Wazirin Biu. Shi kuwa littafi ne da aka rubuta a kan rayuwar fitaccen ɗan kishin ƙasa, Alhaji Ibrahim Biu. Littafin mai shafuka 212, Hon. Haruna Yerima ne ya rubuta shi.

Sai kuma littafi na bakwai da Bukar ya yi wa sharhi, mai suna A Life of Service with Integrity. Shi ma littafi ne game da tarihin rayuwar fitaccen ɗan Najeriya, Dokta Abraham Aderemi Alo.
Na takwas, shi ne littafi mai taken Politics, Law and Diplomacy, wanda Alabama Ogunsanwo ya rubuta kuma ya sadaukar da shi ga tsohon Ambasadan Najeriya, Edward Olusola Sanu. Littafin yana qunshe da ilimi mai yawa dangane da al’amuran hulɗar jakadanci da dokokin ƙasa da ƙasa da suka danganci Najeriya da sauran ƙasashen duniya.
Sai kuma littafi na tara da ya samu sharhi daga alƙalamin Bukar Usman, mai taken The Trial and Other Stories, wanda ke ƙunshe da gajerun ƙirƙirarrun labarai da Ifeoma Okoye ta rubuta. Littafi ne da ke ƙunshe da labaru masu ban al’ajabi da takaici dangane da matan da suka rasa mazajensu na aure a yankin al’ummar Igbo.
Dukkan sharhohi da nazarce-nazarcen nan kan littattafai guda tara, an wallafa su a jaridu da mujallu daban-daban na Najeriya, na Ingilishi da na Hausa.

Kamar yadda tarihi ya nuna, an haifi Bukar Usman a ranar 10 ga watan Disamba, 1942. Don haka a shekarar 2012, lokacin da ya cika shekara 70 daidai a duniya, bisa la’akari da gagarumar hidimar da ya yi wa al’umma a fagagen rayuwa; tun daga aikin gwamnati da fagen rubuce-rubuce da sauransu, an samu masana da ‘yan jarida da marubuta daban-daban da suka yi rubutun yabo a kansa. Haka abin ya kasance a shekarun da suka biyo baya, har zuwa bana, lokacin da ya cika shekara 80 cur a duniya. Don haka, sai Dokta Bukar ya ware kashi na uku na wannan littafi, wanda ya faro daga shafi na 601 zuwa na 662, ya tattara irin waɗannan rubuce-rubuce na yabo da jinjina, ya zuba su a ciki.

An samu muƙaloli guda 16 daga mabanbantan masana a Najeriya, da suka yi irin waɗannan rubuce-rubuce a matsayin jinjina ga ƙwararren marubucin. A yayin da wasu suka karkata alƙalumansu ga rayuwarsa, wasu kuwa sun karkata zuwa ga yabon littattafansa. Waɗannan kuwa sun haɗa da, Hussaini Tukur da Samuel Odaudu da Obinna F. Nwachukwu da Khalid Imam da Okechukwu Uwaezuoke da Musa A. Tijjani da Yemi Adebisi. Sauran sun haɗa Owei Lakemfa da Ijapari Gyang da Faith Olokpo Ochekwu. Haka kuma akwai Henry Akubuiro da sauransu.
Kashi na huɗu kuma na ƙarshe a littafin nan, ya faro ne daga shafi na 663 kuma ya ƙarƙare a 876. Wannan kashi ƙunshe yake da ɗimbin ra’ayoyin makaranta littattafan Dokta Bukar Usman. Waɗansu a jaridu da mujallu suka aika ra’ayoyin nasu, bayan sun karanta maƙalolin da aka wallafa ko kuma suka aiko kai tsaye ta hanyar waya ko imel da sauransu. Taskance waɗannan ra’ayoyi a littafin nan ya ƙara masa armashi kuma ya zama tamkar hisabi ko gejin nuna gamsuwa ko akasin haka ga rubuce-rubuce Dokta Bukar. Hakan kuma zai zama tamkar jagora ga mai nazari.

An inganta littafin nan da Rataye/Manazarta, waɗanda suka kasance a shafi na 877 zuwa na 1126. Wannan sashi shi ma ya tattara muhimman al’amura da suka shafi rubuce-rubucen Bukar da kuma rayuwarsa, kamar yadda aka samar da bunƙasasshiyar Manazarta da ta tattara sunayen kundaye, littattafai, jaridu da mujallun da aka nazarta yayin samar da wannan kandamin littafi.

Game da marubucin kuwa, Dokta Bukar Usman, D.Litt, M.IoD, OON, an haife shi a garin Biu, Jihar Borno a ranar 10 ga watan Disamba, 1942. Ya yi karatun zamani tun daga Firamare har zuwa Digirin-Digirgir (PhD) a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. Ya yi aikin gwamnati tun daga ƙaramin ma’aikaci daga 1965, har zuwa ya kai muƙamin Babban-Sakare a Fadar Shugaban Ƙasa, inda ya kammala aiki a shekarar 1999. Ya rubuta littattafai sama da guda 40 a fagagen ilimi daban-daban. Shi ne Shugaban Gidauniyar Bukar Usman, wacce ya kafa domin jin ƙan raunana, bunƙasa ilimi da sauransu. Haka kuma shi ne Shugaban Ƙungiyar Nazarin Al’adun Gargajiya ta Najeriya (NFS).

Littafin nan babbar taska ce ga ɗaliban ilimi da ma masana domin nazari da zurfafa bincike a fagagen rayuwar ɗan Adam a ko’ina yake a duniya. Babu wani shafi da mutum zai buɗa ya karanta a littafin nan, ba tare da ya ƙaru da wani ilimi ba. Don haka ina kira da babbar murya ga hukumomin ilmi a ƙasar nan da ma duniya baki ɗaya, da su tanadi wannan littafi, su yaɗa shi a ɗakunan karatu, cibiyoyin ilimi, jami’o’i da kwalejojin ilimi, domin amfanin al’umma gaba ɗaya.

Bashir Yahuza Malumfashi, shi ne mawallafin jaridar Taskar Gizago a intanet. Za a iya tuntuɓar shi a bashiryahuza47@gmail.com ko kuma ta 08065576011. 

Previous Post

Rigakafi Ne Babban Jagoran Yaƙi Da Sankarar Mahaifa – Janar Buratai

Next Post

Gwamnati Ta Kula Da Mu

Related Posts

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)
Adabi

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine
Adabi

Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

December 6, 2025
Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu
Adabi

Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu

December 5, 2025
Next Post
Gwamnati Ta Kula Da Mu

Gwamnati Ta Kula Da Mu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

TASKAR GIZAGO Adds category

TASKAR GIZAGO Adds category

September 8, 2023
Tambayoyin Neman Sani A Kan Littafin: JAWAHIRUL MA’ANI

Tambayoyin Neman Sani A Kan Littafin: JAWAHIRUL MA’ANI

October 5, 2025
Ali Nuhu Sarki A Kannywood

Ali Nuhu Sarki A Kannywood

June 29, 2023
Majalisar Dattijai Ta Samu Shugabanni

Majalisar Dattijai Ta Samu Shugabanni

July 4, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation
  • Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco
  • Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.