• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

MATSALAR TSARO: Sakkwatawa Mu Aje Siyasa Don Fuskantar Wannan Babbar Matsala

Yusuf Dingyaɗi by Yusuf Dingyaɗi
October 4, 2023
in Gizago
0
MATSALAR TSARO: Sakkwatawa Mu Aje Siyasa Don Fuskantar Wannan Babbar Matsala

Malam Yusuf Dingyaɗi

7
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

MATSALAR TSARO: Sakkwatawa Mu Aje Siyasa Don Fuskantar Wannan Babbar Matsala

~~~~~~~

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026

A can baya, lokacin mulkin Gwamnatin Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, na yi ta fitowa a kafafen watsa labarai na gida da na waje, ina yi wa ‘yan uwanmu al’ummar jihar nan ta Sakkwato, mussaman ‘yan siyasa bayani a kan mu daina haɗa lamarin siyasa da sha’anin tsaro; mussaman a kan makomar al’ummarmu da ke a karkara, don bai wa gwamnati goyon baya ga matsalar nan.

Babu irin zagi da habaici da cin fuska da wasu ƙananan yaran ‘yan siyasa ba su yi a kaina ba, musamman ma dai a soshiyalmidiya. Wasu ma a gidan rediyo suke mayar da martani a kan cewa ban damu da abin da ke faruwa ba, ina yi wa gwamnati kariya ne.

Abin takaici, har da wasu masana da ke da ilmin sanin abin da yake faruwa na daga cikinsu, waɗanda ke da kusanci da ‘yan siyasa sun yi zambo da shaguɓe.

Zuwa yau, lamarin nan ya yi tsamari, ba a nan jiharmu ta Sakkwato kaɗai ba, abin ya ta’azzara a jihohin Zamfara, Kebbi da Katsina, inda a kusan koyaushe da rana da dare sai an samu kai farmaki na ‘yan ta’adda.
Abin ya tafi har zuwa Niger, Kogi da wani yanki na Jihar Jigawa da Bauchi; inda ake samun rahotanni masu ban tausayi da tsoro a kan lamarin nan na tsaro da kisan jama’a.

Hakan na faruwa. Wasu daga cikin muryoyin sun ɓace, sun yi shiru sun zuba hajar mujiya. Babu bayani, duk da yake abin jiya ya dawo, fiye ma da irin yadda ake ganin sa a baya.

Don haka ƙauyanci da rashin hankali ne na ƙarshen zance, mutum ya yi gum da bakinsa saboda bambancin siyasa, ya riƙa murna a kan faruwar ayyukan ta’addanci ga jama’a, don wai ba su ne a kan gwamnati ba.

Akwai takaici, idan har ɗan Jam’iyyar APC ya yi murna da abin da yake faruwa a Jhar Zamfara, ko ɗan PDP na jin daɗi a kan lamarin da ke faruwa a Jihar Sakkwato ko ma akasin wasu jihohi.

Lokaci ya yi mai muhimmanci na aje siyasa ko adawa ko wani tunani; a kan kowa, don haɗa kanmu, mu fuskanci wannan bala’in da ke ƙara dosowa zuwa gare mu. Mu sani fa, idan har an gama da karkara, sai birni.

Biranenmu ba za su tsira ba saboda ‘yan karkara za su yo mana ambaliya don neman mafaka da abinci, kamar yadda muke gani a yau idan ta kai ƙarshe.

Mu yi wa gwamnati tun daga jiha har tarayya uzuri da fatan alheri, don su samu nasara. Sa’ilin nan mu bayar da tamu gudumuwa, ba tare da siyasa ko wani ra’ayi ba, don jami’an tsaro su cin ma nasara a kan wannan lamarin.

Mahukunta masu riƙe da madafun iko, su aje siyasa, su sanya kishi da tsoron Allah, su fuskanci wannan lamarin da zuciya mai kyau ta gyara.
Saboda abin ya ɓaci fiye da ƙima, mussaman a yankunan karkara da talauci da rashin aikin yi suka addabi al’umma.

‘Yan siyasarmu da suka je can Abuja suka tare, mussaman na PDP da APC, su sani fa har yanzu waɗannan al’umma da suka tsallake suka bari a cikin wahalhalu na rayuwa, suna cikin ƙunci da rashin tsaro. Don Allah su dawo gida, su ziyarci gida da jama’a, don ganin halin da ake ciki, don jaje da yi musu tanzanko da taimako.

Ku sani fa, duk jaririn da ya hana uwarsa barci, tabbata babu barci gare shi, shi ma.

Ku sani, ba ku da wata daraja da ƙimar da ta kai kulawa da lamarin jama’a, koda bayan zaɓe ne.

Ku waigo don taimaka wa al’umma da ke fama da waɗannan bala’oin na rayuwa, ku bar ɗaukar hotuna da yaɗa ƙarairayi, na cewa kun kai ƙarshen matsalar tsaro, kuna bayar da tallafin shinkafa ko kuɗaɗe. Ku zo gida ku fuskanci matsalar jama’ar da kuka roƙa su zabe ku, don ganin halin da suke ciki.

Jiran rahotani daga yaranku ‘yan soshiyalmidiya da masu ba ku shawara, ku yi zaman ku a can, yana da illa sosai. Hakan ba zai taimaka wa al’ummar da suka ba ku amana ba.

Allah Ya kawo mana mafita, Amin.

~~~~~~~
Yusuf Dingyaɗi, marubuci, ɗan siyasa kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, ya rubuto daga Sakkwato.
~~~~~~~

Previous Post

TALAUCI: Yadda Matasan Arewa Ke Gararamba A Legas A Wulaƙance

Next Post

Yadda Za A Farfaɗo Da Martabar Najeriya

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
Yadda Za A Farfaɗo Da Martabar Najeriya

Yadda Za A Farfaɗo Da Martabar Najeriya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

KANO 2024: Tattaunawa Da Zakaran Gasar Marubuta Balannaji

KANO 2024: Tattaunawa Da Zakaran Gasar Marubuta Balannaji

January 3, 2025
Jan Hankali Ga Shugabanni

Jan Hankali Ga Shugabanni

December 9, 2025
SANA’AR NOMA: Ya Dace Attajirai Su Tallafa Wa Matasan Arewa – Dokta Sharif Almuhajir

SANA’AR NOMA: Ya Dace Attajirai Su Tallafa Wa Matasan Arewa – Dokta Sharif Almuhajir

September 17, 2023
Yaƙi Da Ta’addanci: Gwamnatin Tarayya Za Ta Saka Son Ƙasa A Zukatan Al’umma  – Minista

Yaƙi Da Ta’addanci: Gwamnatin Tarayya Za Ta Saka Son Ƙasa A Zukatan Al’umma  – Minista

December 23, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.