• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, March 5, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Bayanan Gaskiya Game Da Najeriya: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga Shugaba Donald Trump

BUƊAƊƊIYAR WASIƘA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
November 2, 2025
in Gizago
0
No, Mr. President: An Open Letter to Donald J. Trump

Shugaban Amurka, Donald J. Trump

47
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Bayanan Gaskiya Game Da Najeriya: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga Shugaba Donald Trump

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

March 1, 2026
#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

February 23, 2026
Shugaban Amurka, Donald J. Trump


                            •••••••
Ya mai girma Shugaban Ƙasar Amurka, Donald J. Trump, na rubuto maka wannan wasiƙa ce a madadin miliyoyin ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da suka damu da makomar ƙasarmu da al’ummarmu, da ma dangantakar da muke da ita da Amurka.

Mun karanta maganganunka da ka ambaci cewa ana zaluntar Kiristoci a Najeriya, kuma ka ayyana cewa ka saka ƙasar tamu cikin jerin ƙasashen da Amurka ta sanya wa ido. Wannan batu ya girgiza zukatanmu saboda ya bijiro da batun ƙage, domin ya jirkita ainihin gaskiyar halin da ƙasarmu take ciki.

Ya Shugaba, ba gaskiya ba ne cewa matsalar Najeriya ita ce faɗa tsakanin Kirista da Musulmi. A mafi yawan lokuta, Musulmi da Kiristoci suna rayuwa tare cikin zaman lafiya, suna kasuwanci tare, suna auratayya da juna, suna kuma raba makoma ɗaya. Matsalar Najeriya ba ta addini ba ce, matsalar rashin shugabanci ne mai nagarta da kuma lalatacciyar siyasa wacce ta mamaye ƙasa tun bayan samun ‘yancin kai.

Manyan shugabanninmu sun gaza wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Suna karkatar da albarkatun ƙasa zuwa aljihunsu, sun bar jama’a cikin tsananin talauci, rashin ilimi, yunwa da cututtuka. Wannan ita ce babbar musiba da muke fuskanta, ba rikicin addini ba amma rashin shugabanni masu gaskiya, adalci da tausayi ga talaka.

Game da matsalar tsaro kuwa, Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ta’addanci kamar ‘yan bindiga a Arewa suna kashe dubban mutane, mafi yawansu Musulmi ne a jihohin Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma. Sukan kai hare-hare a masallatai, kasuwanni, makarantu da ƙauyukan da ba su da kariya. Rashin tsaro ya fi shafar Musulmi a ƙasar, fiye da Kiristoci, akasin yadda ake yayatawa a kafofin labarai na waje.

Haka nan, Kiristoci ma suna fuskantar wannan tashin hankali, ba don ana kai musu hari saboda addininsu ba amma saboda rikice-rikicen da suka samo asali daga tsaro, talauci, rashin kulawar gwamnati da ta rashin kula da rayuwar jama’a. Don haka, ayyana wannan lamari da cewa ana “kashe Kiristoci” kawai zai ƙara rikita al’amura ne, ya raba kan mutane kuma ya haifar da ƙiyayya tsakanin al’ummar ƙasa.

Annobar ta’addanci ta samo asali ne daga rashin aikin yi, cin hanci da rashawa, rashin ilimi da kuma sakacin gwamnati wajen kare rayukan jama’a. Wannan matsala ce da ta daɗe tana faruwa, ba wai rikicin Musulmi da Kiristoci ba ne. Talaka bai damu da addinin maƙwabcinsa ba amma yana damuwa da yunwa, rashin lafiya, rashin tsaro da rashin adalci daga masu mulki.

Ya Shugaba Trump, abin da ‘yan Najeriya ke buƙata daga Amurka ba wai tsangwama ko hukunci ba ne amma muna buƙatar taimako wajen gina dimokuraɗiyya mai ƙarfi da tallafa wa shugabanci nagari da samar da shugabanni masu gaskiya da kuma horar da matasa da sana’o’i da sama masu kayan aikin da za su raya ƙasarsu. Wannan shi ne ainihin taimakon da zai kawo zaman lafiya da bunƙasar Najeriya da Afirka da ma duniya baki ɗaya.

Muna kira ga Amurka da ta yi amfani da tasirinta wajen ɗora shugabanninmu kan turbar gaskiya da adalci, ta hanyar tilasta tsarin da zai inganta zaɓe, ya yaƙi rashawa, ya kare haƙƙin jama’a kuma ya buɗe ƙofofin tattalin arziki ga talakawa, maimakon ‘yan tsirarun masu mulki. Idan aka samu shugabanci nagari, bambancin addini, ƙabila ko yanki ba za su ƙara zama matsala ba a cikin al’ummar ƙasa.

Ya Shugaba, Najeriya ƙasa ce mai cike da ɗimbin albarkatu, kama daga man fetur, noma da yawan jama’a masu fasaha da kuzari. Abin da muke buƙata shi ne abokantaka wacce ta dogara kan gaskiya da fahimta, ba kan jita-jita ko labaran da ke ƙara raba kan jama’a ba. Duniya za ta fi zama wuri mai aminci idan manyan ƙasashe kamar Amurka suka tallafi adalci maimakon ɓangaranci.

A wannan gaɓa ta ƙarshe, muna roƙon Shugaba Trump da ya saurari muradin talakawan Najeriya, ba wai kawai muryar ‘yan siyasa ko ta wasu karkatattun malaman addinai ba. Ka duba tare da nazarin haƙiƙanin gaskiyar abin da ke faruwa a Najeriya. Ka fahimci cewa burinmu shi ne zaman lafiya, ci gaba da haɗin kai tsakanin addinai da ƙabilu na kowane ɓangare ko shiyya. Allah ya sa ka fahimci gaskiya kuma ya ba ka ikon yin adalci ga ƙasarmu da ma duniya baki ɗaya.

Na gode sosai da lokacinka na sauraren wannan saƙo nawa. Ka zama lafiya.
_______________
Malam Yahuza Malumfashi, marubuci, sha’iri, shi ne mawallafin Mujallar Taskar Gizago a intanet

Previous Post

No, Mr. President: An Open Letter to Donald J. Trump

Next Post

Ta’aziyyar Malam Nata’ala Mai Sittin Goma

Related Posts

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)
Gizago

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

March 1, 2026
#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI
Gizago

#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

February 23, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (13)
Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (13)

February 20, 2026
Next Post
Ta’aziyyar Malam Nata’ala Mai Sittin Goma

Ta'aziyyar Malam Nata'ala Mai Sittin Goma

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

TSOKACINMU NA YAU (24)

TSOKACINMU NA YAU (24)

March 24, 2025
GWAMNA MALAM DIKKO YA YI RASHIN MAHAIFIYA

GWAMNA MALAM DIKKO YA YI RASHIN MAHAIFIYA

March 23, 2025
TSOKACINMU NA YAU – 01

TSOKACINMU NA YAU – 01

March 1, 2025
RAMADAN KARIM: 04-1447

RAMADAN KARIM: 04-1447

February 21, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Injiniya Tukur Hassan Tingilin (1978-2026)
  • RAMADAN KARIM: 16-1447
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (7)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

RAMADAN KARIM: 16-1447

Injiniya Tukur Hassan Tingilin (1978-2026)

March 5, 2026
RAMADAN KARIM: 16-1447

RAMADAN KARIM: 16-1447

March 5, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.