• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, May 3, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Ta'aziyya

Ta’aziyyar Malam Nata’ala Mai Sittin Goma

TA'AZIYYA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
November 3, 2025
in Ta'aziyya
0
Ta’aziyyar Malam Nata’ala Mai Sittin Goma

Marigayi Malam Nata'ala

11
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Ta’aziyyar Malam Nata’ala Mai Sittin Goma

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Malumfashi Mun Yi Babban Rashi

Malumfashi Mun Yi Babban Rashi

March 26, 2026
RAMADAN KARIM: 16-1447

Injiniya Tukur Hassan Tingilin (1978-2026)

March 5, 2026
Marigayi Malam Nata’ala


                     _______________
Babu shakka, kowane mai rai mamaci ne kuma ajali ba ya taɓa wuce ranarsa. Bisa ga wannan ƙauli, a jiya Lahadi, 11-05-1447 (Hijiriyya), 02-11-2025 (Miladiyya), na samu rahoton cewa Allah ya amshi ran bawansa, Mato Yakubu, wanda aka fi sani da Malam Nata’ala Mai Sittin Goma.

Wane ne Malam Nata’ala? Kamar yadda aka bayyana a gabatarwa, sunansa Mato Yakubu kuma an haife shi a ranar 15 Agusta 1967 a garin Dambuwa Rijiya, Ƙaramar Hukumar Potiskum, Jihar Yobe.

Ya fara harkar fim ko kuma wasan kwaikwayo da daɗewa, tun ma kafin bayyanar finafinan Kannywood. Ya yi wasan kwaikwayo a garin Jimeta da ke Jihar Adamawa. Daga bisani ne ya koma Kano da sana’arsa ta fim.

Kasancewar ya fi ƙwarewa a finafinan barkwanci, a can shekarun baya, ya yi finafinai masu tarin yawa tare da marigayi Labiru Musa, wanda aka fi sani da Ɗan Ibro. Kodayake ya fi shahara a fim mai dogon zango na Daɗin Kowa, wanda gidan talabijin na Arewa24 yake haskawa. Hasali ma, a cikin wannan fim ne ya samu wannan suna na Malam Nata’ala.

Baya ga Daɗin Kowa, Malam Nata’ala ya taka rawa mai burgewa a fim ɗin A Duniya, inda nan ma ya fito a matsayin malamin tsangaya, mai almajirai.

Malam Nata’ala ya ɗan jima yana jinya, amma a watan Agustan bana ne rahoton rashin lafiyarsa ya bayyana sosai, inda ya yi fama da ciwon daji. A wani faifan bidiyo, an nuno marigayin yana maganar cewa: “Ina buƙatar taimakon addu’a da kuɗi saboda jinya ce mai hatsari kuma ƙarfina ya gaza, duk sati uku zan yi allurar Naira 250,000 har na wata shida, ban da magunguna da kuɗin gado.”

Ya samu tausayawa daga mutane daga sassa daban-daban na Najeriya. Ya kuma samu tallafi daga fitattun abokan sana’arsa ‘yan fim amma babban tallafin kuɗin da ya samu daga Shugaban Ƙasar Nijar, Janar Abdulrahman Tchani, su suka fi faranta masa rai.

Muna roƙon Allah ya ji ƙan shi da rahama, ya sa ya huta. Mu kuma da muke nan, Allah ya kyautata tamu mutuwar, idan lokacinmu ya zo. Amin-Summa-Amin.
_______________

Previous Post

Bayanan Gaskiya Game Da Najeriya: Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga Shugaba Donald Trump

Next Post

Ba Mu Da Wata Ƙasa Kamar Najeriya

Related Posts

Malumfashi Mun Yi Babban Rashi
Ta'aziyya

Malumfashi Mun Yi Babban Rashi

March 26, 2026
RAMADAN KARIM: 16-1447
Ta'aziyya

Injiniya Tukur Hassan Tingilin (1978-2026)

March 5, 2026
ALLAH JI ƘAN INJINIYA TUKUR
Ta'aziyya

ALLAH JI ƘAN INJINIYA TUKUR

February 27, 2026
Next Post
Ba Mu Da Wata Ƙasa Kamar Najeriya

Ba Mu Da Wata Ƙasa Kamar Najeriya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

THE MAN B. Y. M.

THE MAN B. Y. M.

June 28, 2024
Haramta Koyarwa Da Harshen Uwa: Koma Baya Ko Cigaba?

Haramta Koyarwa Da Harshen Uwa: Koma Baya Ko Cigaba?

November 16, 2025
BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (4)

BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (4)

January 14, 2024
RAMADAN KARIM: 13-1447

RAMADAN KARIM: 13-1447

March 2, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)
  • General Buratai (A Poem)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

April 27, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.