• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, January 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Sarauta

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

SARAUTA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
October 26, 2025
in Sarauta
0
Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

Wazirin Galadiman Katsina, Alhaji Shehu Musa Ɗankano

51
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa
– Waziri Shehu Musa

Wazirin Galadiman Katsina, Alhaji Shehu Musa Ɗankano


                           __________
A jiya Asabar, 03-05-1447 (Hijiriyya), 25-10-2025 (Miladiyya), Galadiman Katsina, Hakimin Malumfashi, Mai Shari’a Sadiƙ Abdullahi Mahuta, OFR ya naɗa sabon Wazirin Galadiman Katsina, Alhaji Shehu Musa Ɗankano. Bashir Yahuza Malumfashi, Fasihin Galadiman Katsina-I ya tattauna da sabon Wazirin, a gidansa da ke Malumfashi; inda ya bayyana cewa wannan sarauta, karramawa ce gare shi daga Galadiman Katsina. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
                         __________
TG: Ga shi a yau Allah ya tabbatar da naɗinka a sarautar Wazirin Galadiman Katsina, ko yaya kake ji a ranka a yau?

Related posts

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

October 22, 2025
Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’

Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’

October 17, 2023

Waziri: Alhamdu lillah. Babu shakka zan fara da godiya ga Allah (swt) da wannan ni’ima da ya yi mani. Haka kuma ina godiya ga mai girma Galadiman Katsina, Mai Shari’a Sadiƙ Abdullahi Mahuta, OFR da wannan sarauta da ya ba ni ta Wazirin Galadiman Katsina. Babu shakka wannan sarauta, babbar karramawa ce a gare ni. Lallai kuma ina farin ciki matuƙa a yau. Allah saka da alheri.

Wazirin Galadiman Katsina, Alhaji Shehu Musa Ɗankano, tare da Fasihin Galadiman Katsina-I, Bashir Yahuza Malumfashi

TG: Yanzu ka tashi daga Ɗan Iyan Galadiman Katsina ke nan?

Waziri: Wannan gaskiya ne, daga yau na zama Wazirin Galadiman Katsina. Da ma a zamanin marigayi Galadiman Katsina na 10, Jastis Mamman Nasir ne Ya naɗa ni Sarautar Ɗan Iyan Galadiman Katsina. A yau wannan sarauta ta Ɗan Iya ta koma kan babban ɗan Galadima Sadiƙ Abdullahi Mahuta. Wannan sarauta ta Waziri, ita ce mafi girma daga Galadima. Wato daga shi Ubanƙasa Galadima, sai kuma ni Waziri.

A dama, Waziri ne, tare da Lawal Nababa

TG: Ko kai ne na farko da aka taɓa ba wannan sarauta ta Waziri a Masarautar Galadiman Katsina?

Waziri: A’a, ba ni ne na farko ba. A can baya, an taɓa naɗa kawunmu, Bello Adamu a sarautar Wazirin Galadiman Katsina. Ya rasu kimanin watanni biyar da suka gabata. Ke nan, ni ne na biyu a wannan sarauta da aka naɗa a yau, bisa hukuncin Allah.

Wazirin Galadima tare da wasu danginsa

TG: Waɗanne irin ayyuka ne suka jiɓinci wannan sarauta ta Wazirin Galadiman Katsina?

Waziri: Muhimman ayyukan da suka hau kaina, a matsayina na Wazirin Galadiman Katsina sun haɗa da bayar da shawarwari ga shi mai girma Galadima, domin kyautata masarautar gaba ɗaya. Na biyu, tabbatar da cewa dukkan al’amuran da suka shafi masarautar Galadima suna tafiya daidai yadda suka kamata, ko Galadima na nan, ko ba ya nan. Wannan amana ce babba a kaina in kula da al’amuran masarautar. Haka kuma aikina ne in saurari al’ummar masarautar, in ji kokensu, Sannan in sanar da Galadima, a tattauna yadda za a magance su. Haƙƙin Galadima ne a sanar da shi abin da ke faruwa a masarautarsa – wannan aikina ne.

Wazirin Galadiman Katsina, ana taya shi murna

TG: Bisa la’akari da cewa an san ka da jajircewa wajen hidimar al’umma, a yanzu ga sabon nauyi ya ƙara hawa kanka. Shin me al’umma za su tsumaya daga gare ka?

Waziri: Alhamdu lillahi. A duk lokacin da mutum yake tafiyar da ayyukansa domin Allah, to haka lamarin ke kasancewa a gare shi. Ni dai ban yi tsammanin samun wannan babbar sarauta ba, sai ga shi Allah ya hukunta. Galadima ya yi la’akari da abubuwan da nake yi a baya da kuma abubuwan da zan iya yi a nan gaba in sha Allah, su ne suka sanya ya girmama ni da wannan sarauta. Sarauta ce mai ƙima kuma mai daraja sosai. Don haka da yardar Allah zan yi iya ƙoƙarina wajen ganin na ci gaba da yi wa al’umma hidima da kare martabar ita kanta sarautar da ma garinmu, jiharmu da ƙasarmu baki ɗaya.

TG: Malumfashi da kewaye na fuskantar matsalolin tsaro a wannan lokaci, a matsayinka na sabon Wazirin Galadima, wace shawara za ka ba jami’an tsaro da shugabanni, domin ganin an magance wannan ƙalubale na tsaro a wannan yanki?

Waziri: Babbar shawarar da zan ba da ita ce, a yi duk mai yiwuwa, a ƙokarta a kawo ƙarshen wannan matsala ta tsaro. Babu shakka mutane suka cikin matsala, domin ba su iya zuwa gona cikin aminci. Masu sana’o’i da kasuwanci suna fuskantar matsaloli. Shugabanni da jami’an tsaro suna ƙoƙari amma su ƙara himma, domin ganin Allah ya agaza mana, domin kawo ƙarshen matsalar.

Fulanin da ake zargi da wannan al’amari, ‘yan ƙasa ne ba bare ba, don haka a saurare su, a tsaya a yi gyara na kirki. Su ma ana jin suna kawo ƙorafe-ƙorafensu. A tara masana da masu ruwa da tsaki a zauna a tattauna lamarin nan, a yi wa kowa adalci, domin magance matsalar nan. Ta haka za a samu zaman lafiya da aminci.

Taya murna ga Wazirin Galadinan Katsina, Alhaji Shehu Musa Ɗankano

TG: Ma sha Allah. Muna taya ka murna kuma Allah ya taya ka riƙo.

Waziri: To, Malam Bashir, Fasihin Galadima, ina godiya. Allah saka da alheri.
__________

Previous Post

Aure Sunnar Ma’aiki: Taya Murna Ga Uba Nagari Shehu Musa Sarkin Ƙofa

Next Post

Marigayi Sarkin Labaran Daura: Tunawa Da Mutumin Kirki Mai Zumunci

Related Posts

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina
Sarauta

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

October 22, 2025
Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’
Sarauta

Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’

October 17, 2023
KWATAM HUBA HALIMA TAHIR: Tattaunawa Da Fitattar ‘Yar Jarida Basarakiya
Sarauta

KWATAM HUBA HALIMA TAHIR: Tattaunawa Da Fitattar ‘Yar Jarida Basarakiya

August 19, 2023
Next Post
Marigayi Sarkin Labaran Daura: Tunawa Da Mutumin Kirki Mai Zumunci

Marigayi Sarkin Labaran Daura: Tunawa Da Mutumin Kirki Mai Zumunci

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (6)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (6)

January 6, 2026
ZINATU MATAR GWAMNA (2)

ZINATU MATAR GWAMNA (2)

January 20, 2024
Burina Rubutuna Ya Zama Silar Shiriyar Al’umma – Antin Kaduna

Burina Rubutuna Ya Zama Silar Shiriyar Al’umma – Antin Kaduna

September 10, 2023
BAKIN JAƁA (4)

BAKIN JAƁA (4)

September 16, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation
  • Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco
  • Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.