• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, August 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Sarauta

Ya Zama Wajibi A Tallafa Wa Matasa A Masarautar Galadiman Katsina

In Ji Hasken Fadar Galadiman Katsina

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 10, 2026
in Sarauta
0
Ya Zama Wajibi A Tallafa Wa Matasa A Masarautar Galadiman Katsina

Alhaji Kabir Alwala 3030, Hasken Fadar Galadiman Katsina

30
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Ya Zama Wajibi A Tallafa Wa Matasa A Masarautar Galadiman Katsina

– In Ji Hasken Fadar Galadiman Katsina

Related posts

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

October 26, 2025
Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

October 22, 2025

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Alhaji Kabir Alwala 3030, Hasken Fadar Galadiman Katsina


__________
Hasken Fadar Galadiman Katsina, Alhaji Kabir Lawal 3030 ya yi kira da babbar murya ga attajirai da manyan ma’aikatan gwamnati na Masarautar Galadiman Katsina a Ƙaramar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina da su riƙa tallafa wa matasa yadda ya kamata, musamman wajen sama masu ayyukan yi, koya sana’o’i da kuma tallafin karatu, domin magance zaman kashe wando da gararamba a titi.

Alhaji Kabir 3030, wanda kuma shi ne Sarkin Hausawan Owerri, Jihar Delta, ya bayyana cewa rashin aikin yi ko sana’a da matasa suke yi, shi yake haddasa suke faɗawa cikin harkokin shaye-shaye da kuma shiga muggan ƙungiyoyin aikata manyan laifuka da sauransu. Ya jadadda cewa, babbar hanyar da za a magance matsalolin tsaro a yankunan Masarautar Galadima da ma Jihar Katsina baki ɗaya, shi ne gwamnati da masu hannu da shuni da manyan ma’aikatan gwamnati su riƙa jan matasa a jika, suna tallafa masu da aikin yi ko sana’a da kuma ɗaukar nauyin karatunsu.

Da yake ƙarin haske kan lamarin a wata tattaunawa ta musamman da wakilinmu, Hasken Fadar Galadima ya ba da misali da shi kansa, ya ce: “An haife ni a Unguwar Dawo, Ƙaramar Hukumar Malumfashi, Jihar Katsina. Na yi makarantar firamare a Tunau Primary School da kuma Unguwar Dawo Primary School, Malumfashi. Kuma tun da na taso, ban yi zaman banza ba, na ci gaba da neman ilimi,” in ji shi.

Ya ce ya ci gada da karatun sakandare a Government Day Secondary School Ɗanrimi, Malumfashi, inda ya yi aji uku, daga nan kuma ya ci gaba a Government College Katsina, inda yana aji biyu na babbar sakandare, ya sake canja makaranta.

A cewarsa, “Na ci gaba da karatun aji uku a babbar sakandare, a Arabic Teachers’ College Katsina, inda bayan na kammala, na shiga aikin ‘yan sanda kai tsaye.”

Da yake bayani game da sarautarsa ta Hasken Fadar Galadiman Katsina, Alhaji Kabir 3030 ya ce an naɗa shi wannan sarauta a ranar 12 ga watan Oktoba, shekara ta 2024.

“Mai girma Galadiman Katsina na 11, Mai Shari’a Saddiƙ Abdullahi Mahuta ne ya naɗa ni wannan sarauta ta Hasken Fada, bisa cancanta. Kaɗan daga cikin ayyukana a wannan masarauta, sun haɗa da bayar da muhimman shawarwari ga masasauta, domin bunƙasa al’umma, bayar da tallafi ga al’umma, musamman matasa ta hanyoyin da Allah ya hore mani da kuma kare martabar masarautar a ko’ina a faɗin duniya,” in ji 3030.

“A halin yanzu haka, ina tare da matasa ƙimanin 340, ina sama masu aiki da hanyoyin sana’a. A duk lokacin da dama ta samu, nakan yi amfani da ita wajen tallafa wa matasan Masarautar Galadiman Katsina.”

Alhaji Kabir 3030 ya ci gaba da cewa: “A nan Owerri, ni ne Sarkin Hausawa kuma ina samun damarmamaki da guraben aiki a kamfanoni. Nakan ɗauko matasanmu daga gida, in yi masu jagora su samu abin dogaro da kai.”

Hasken Galadima ya shawarci matasa da su guji zaman banza, su guji shaye-shaye. “A matsayinka na matashi, ka kama sana’a komai ƙankantarta, idan ka riƙe za ta bunƙasa. Ba sai ka jira aikin gwamnati ba. Ni a ra’ayina, na fi ba matasa shawara su kama sana’a, ba aikin gwamnati ba,” in ji shi.

Game da matsalar tsaro da take addabar masarautar Galadima da ma Jihar Katsina baki ɗaya, Alhaji Kabir 3030 ya ce ya kamata masarauta ta ba matasa muhimmanci, a tattara su, a riƙa ba su horo da kayan aiki, domin aikin tsaro na sa-kai. “Ni a misali, na ɗauki matasa sama da 30 a unguwarmu suna aikin tsaron unguwa. Na haɗa kansu, ina ba su shawararwari da kayan aiki, kamar tocila da sauransu, daidai gwargwadon abin da Allah ya hore mani.”

Wakilinmu ya tambayi Hasken Fada, shin ko Alhaji Kabir 3030 yana sha’awar shiga harkokin siyasa? Ya amsa da cewa:

“Ba ni da ra’ayin siyasa a rayuwata. Ko da na kammala aiki, kasuwanci zan kama. Ina da jama’a amma ba zan shiga siyasa ba saboda na san illarta. Ba na son in kasa sauke nauyin da Allah ya ɗora mani.”

Da yake yaba wa Galadiman Katsina kuwa, Hasken Fada Kabir 3020 ya ce: “Galadima Jastis Saddiƙ dattijo ne. A ra’ayina, ba a taɓa samun Galadima kamarsa ba a matsayin Hakimin Malumfashi. Bai da baƙin ciki, bai da girman kai, yana amsar kowa ba tare da wariya ba. Yana tafiyar da mulkinsa bisa daidai.”

Hasken Galadiman Katsina, Alhaji Kabir Lawal 3030 ya ƙarƙare da addu’a ga Galadima. “Tsakanina da Galadima sai fatan alheri. Allah ya sa ya gama mulkinsa lafiya kuma ya rabu da duniyar nan lafiya. Daga ƙarshe, ina fatan alheri ga ƙaramar hukumarmu ta Malumfashi da jiharmu ta Katsina da ƙasa baki ɗaya.”
__________

Previous Post

Inna Lillahi… Bandits Shoot Our Colleague

Next Post

Katsina A Makon Jiya (Kashi Na Ɗaya)

Related Posts

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa
Sarauta

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

October 26, 2025
Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina
Sarauta

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

October 22, 2025
Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’
Sarauta

Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’

October 17, 2023
Next Post
Katsina A Makon Jiya (Kashi Na Ɗaya)

Katsina A Makon Jiya (Kashi Na Ɗaya)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

MAGAJI GALADIMA: Yau Ne Maulidin Magayaƙin Kano

MAGAJI GALADIMA: Yau Ne Maulidin Magayaƙin Kano

September 29, 2023
ACF Endowment Fund Sets Agenda for Transparency, Education and Empowerment in Northern Nigeria

ACF Endowment Fund Sets Agenda for Transparency, Education and Empowerment in Northern Nigeria

June 24, 2026
IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne

IBB: Kai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne

August 17, 2026
…BUT WHERE IS IFEANYI?

…BUT WHERE IS IFEANYI?

February 26, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Professor Bello Sa’idu: The Demise of Literary Icon
  • Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu
  • Musulunci Ba Addinin Tsauri Ko Sakaci Ba Ne…

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

Professor Bello Sa’idu: The Demise of Literary Icon

August 23, 2026
Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

Bankwana Da Jigon Adabi: Ta’aziyyar Farfesa Bello Sa’idu

August 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.