• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, September 20, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Marigayi Sarkin Labaran Daura: Tunawa Da Mutumin Kirki Mai Zumunci

GIZAGO

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
October 27, 2025
in Gizago
0
Marigayi Sarkin Labaran Daura: Tunawa Da Mutumin Kirki Mai Zumunci

A dama, marigayi Sarkin Labaran Masarautar Daura, Alhaji Ibrahim Yaro da Bashir Yahuza Malumfashi (Gizago), a taron Goron Sallah na Ƙungiyar Gizago da ya gudana a 2011

69
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Marigayi Sarkin Labaran Daura: Tunawa Da Mutumin Kirki Mai Zumunci

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

SUNANTA UMMU-KHULSUM

SUNANTA UMMU-KHULSUM

September 13, 2026
HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1

HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1

September 12, 2026

                            •••••••
Ina zaune ina binciken tulin hotunan da suke kimshe a faldojin ma’adanata, kawai sai idona ya kai kan wannan hoton, ni da marigayi Sarkin Labaran Masarautar Daura, Alhaji Ibrahim Yaro.

Da ma a kwanakin baya da na kai ziyara Fadar Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, na gana da ɗan marigayin, Alhaji Usman Ibrahim Yaro, wanda kuma shi ne ya gaje shi a wannan sarauta. A yanzu haka shi ne Sarkin Labaran Masarautar Daura na yanzu.

A lokacin da muke tunawa da Marigayin, mun tattauna al’amura sosai dangane da shi. Ya tuno lokacin da marigayin yake raye, yadda ya ɗauki Ƙungiyar Gizago da muhimmanci, a matsayinsa na Uban Ƙungiya.

Babu shakka nakan tuna kyawawan halayensa na himma da son zumunci. A matsayinsa na jajirtaccen Uban Gizagawa, marigayi ya yi hidima mai tarin yawa na jaddada zumunci da ‘yan uwantaka. Nakan tuna yadda a duk lokacin da aka kira taro, marigayin kan cika motarsa da mai, ya ɗauki ayarinsa tun daga Daura, ya halarci taron.

Muhimman taruka biyu ne ba zan mance da su ba, inda marigayin ya halarta kuma ya yi hidima mai yawa. Na farko shi ne taron Kaduna, wanda aka gudanar a Arewa House a shekarar 2010 da kuma taron Goron Sallah, wanda aka gudanar a Funtuwa, a shekarar 2011. Ba zan mance ba, a Funtuwa ne ma muka ɗauki wannan hoton.

Duk wani Bagizage da ya kwana cikin Ƙungiyar Gizago, ya san irin ƙima, daraja da mutuncin marigayi Sarkin Labaran Masarautar Daura, Alhaji Ibrahim. Babu abin da muka sani a kansa, daga alheri sai alheri, sai zumunci da mutunci.

A yau da nake tuna wannan bawan Allah, ni Bashir Yahuza Malumfashi, Gizago, a madadin ɗaukacin Gizagawan Zumunci da ke faɗin duniyar nan, muna addu’a: Allah ya ji ƙan Sarkin Labaran Masarautar Daura, Alhaji Ibrahim Yaro. Allah ya sanyaya makwancinsa, ya jaddada masa rahama. Allah ya ba shi ladar zumuncinsa da muke tunowa a yau. Amin-Summa-Amin!
_______________

Previous Post

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

Next Post

Tarihin Rayuwar Sabon Shugaban Rundunar Sojojin Ruwa Na Najeriya Rear Admiral Idi Abbas

Related Posts

SUNANTA UMMU-KHULSUM
Gizago

SUNANTA UMMU-KHULSUM

September 13, 2026
HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1
Gizago

HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1

September 12, 2026
Ayyukan Alheri Daga Gidan Amana
Gizago

Ayyukan Alheri Daga Gidan Amana

September 5, 2026
Next Post
Tarihin Rayuwar Sabon Shugaban Rundunar Sojojin Ruwa Na Najeriya Rear Admiral Idi Abbas

Tarihin Rayuwar Sabon Shugaban Rundunar Sojojin Ruwa Na Najeriya Rear Admiral Idi Abbas

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

KO ME YA SA MABIYA PETER OBI SUKA RIƘA MURNAR MUTUWAR HON. EKENE ABUBAKAR ADAMS?

KO ME YA SA MABIYA PETER OBI SUKA RIƘA MURNAR MUTUWAR HON. EKENE ABUBAKAR ADAMS?

July 17, 2024
Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

August 13, 2026
Jami’ar Bayero Ta Karrama Janar Buratai

Jami’ar Bayero Ta Karrama Janar Buratai

December 16, 2023
Soyayya: Yadda Wata Budurwa Ta Samu Mijin Kirki

Soyayya: Yadda Wata Budurwa Ta Samu Mijin Kirki

May 29, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.