• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, April 18, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

HAƊIN KAI: SHAWARA TA MUSAMMAN GA ƊAUKACIN MARUBUTAN HAUSA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 29, 2025
in Adabi
0
HAƊIN KAI: SHAWARA TA MUSAMMAN GA ƊAUKACIN MARUBUTAN HAUSA

Ranar Marubutan Hausa ta Duniya (Jigawa-2025)

19
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

HAƊIN KAI: SHAWARA TA MUSAMMAN GA ƊAUKACIN MARUBUTAN HAUSA

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Ranar Marubutan Hausa ta Duniya (Jigawa-2025)


                             •••••••
A yau, kowa shaida ne yadda harshen Hausa da adabinsa suka shahara kuma suka karaɗe dukkan duniya. Haka kuma kowa shaida ne yadda harshen da masu harshen suke ba da gagarumar gudunmowa a dukkan sassan rayuwar al’umma, waɗanda suka haɗa da ayyuka da sana’o’i, ilimi, tsaro, noma, nishaɗantarwa, watsa labarai, wayar da kai, addini da sauransu.

Sai dai kuma duk da wannan ɗaukaka ta harshen, amma an bar MARUBUTAN HAUSA a baya. Marubutan Hausa sun zama gugar yasa, sun zama tattaki, duk kuwa da cewa a kullum da bazarsu ake rawa. A fannin ilimi, da littattafansu ake amfani a jami’o’i da kwalejijin ilimi. A finafinai, da ayyukansu ake bugun gaba. Za ka ga malamin jami’a ya zama gangaran, albarkacin marubutan Hausa. Za ka ga furodusa, darakta da aktoci sun samu shahara da tarin dukiya, duk albarkacin marubutan Hausa. Amma abin takaici, su marubutan suna durƙushe, an mayar da su tamkar mabarata. Wannan shi ake kira, kura da shan bugu, gardi da amshe kuɗi.

Kuma wannan lalacewar, tana faruwa ne ga MARUBUTAN HAUSA na wannan zamani kaɗai. Muna sane a tarihi, yadda marubutan dauri suka samu gata da tarairaya daga gwamnatocin zamaninsu, da ma sauran al’umma. Haka kuma a wannan zamanin, muna ganin yadda MARUBUTAN INGILISHI ke samun tagomashi da kula ta musamman daga gwamnati da ma al’ummar duniya. To ga tambaya: Shin me ya sa marubutan Hausa na wannan zamani ke fuskantar wannan ƙalubale?

Babbar amsa ita ce, RASHIN HAƊIN KAI. A yau, marubutan Hausa suna da ƙungiyoyi barkatai amma na banza. Ƙungiyoyi ne na je-ka-na-yi-ka, tarin tsintsiya babu shara. Ƙungiyoyi ne da suka yi kama da kumfar kogi, sai yawan afki amma babu wani alfanu.

Haka kuma, wani dalilin da ke haifar mana da koma baya shi ne, SON KAI da NINANCI da HASSADA da ƘYASHI. Ba sai na fassara ma’anar waɗannan matsaloli ba ga dukkan wani marubuci da marubuciyar Hausa. Domin kuwa ruwa ya daɗe yana kwarara, ƙasa tana shanyewa. To yanzu, ina mafita?

Babu shakka, madamar marubutan Hausa suna son gyara lamarinsu, to ya zama dole su yi karatun-ta-natsu, domin fitar da jaki daga duma. Ya zama dole a magance, waɗancan matsaloli da na zayyano a baya. Lamari ne mai sauƙi kuma mai wuya. Mai sauƙi ne idan muka ɗaura niyya da kyakkyawar manufa. Kuma lamari ne mai wuya, idan ba mu shirya kawo gyaran ba da gaske.

Domin samar da HAƊIN KAI, ya kamata mu yi amfani da wannan taro na bana, wajen kafa GAGGARUMAR ƘUNGIYAR MARUBUTAN HAUSA TA NAJERIYA. Wacce za ta zama babbar uwa ga dukkan marubutan Hausa kuma ta zama uwa ga dukkan sauran ƙungiyoyin marubuta da ke akwai a sassa daban-daban a faɗin ƙasa.

Dole marubuta su haɗa kai a ƙarƙashin wannan ƙungiya. Kuma a samar mata da JAJIRTATTUN SHUGABANNI, waɗanda ya kamata a zaƙulo su daga sassan jihohinmu gaba ɗaya.

Tun yanzu, a shirye-shiryen nan na ranar taron Jigawa, a fara tattauna samar da wannan ƙungiya, a samar da shugabannin riƙon ƙwarya, waɗanda za su jagorance ta zuwa ga nasara, kafin ta kafu. A nan, ina ba da shawara, a miƙa shugabancin riƙo ga jajirtacce, mai ƙaunar adabin Hausa da marubutan Hausa – FARFESA ABDALLA UBA ADAMU. Sannan a sama masa mataimaka daga marubuta maza da mata daga jihohinmu daban-daban.

Ina da tabbacin, muddin muka samu wannan ƙaƙƙarfar ƙungiya kuma muka cire son kai, muka cire ninanci, muka cire ƙyashi da hassada daga zukatanmu, wallahi MARUBUTAN HAUSA sai sun zama abin kwatance a duniya baki ɗaya.

Ina fata da roƙon Allah ya sa mu duba wannan shawara, mu yi wa kanmu ƙiyamullaili, domin kawo gyara ga lamarinmu, yadda mu ma za mu amfana daga baiwar da Allah ya ba mu.

Allah sa mu dace, ya yi mana jagora, Amin.

Wassalam.
Daga ɗan uwanku a Alƙalami da Takarda,
Bashir Yahuza Malumfashi
_______________

Previous Post

Abubuwan Da Za Su Iya Faruwa Idan Kwankwaso Ya Koma APC

Next Post

Gwamna Raɗɗa Ya Kusa Kammala Tashar Mota Mafi Girma A Najeriya

Related Posts

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza
Adabi

Littafin Rayuwar Fitacciyar ‘Yar Jarida Jamila Tangaza

April 11, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Let’s Speak Our Mother Tongue
Adabi

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

March 6, 2026
Next Post
Governor Radda Builds Nigeria’s Largest Motor Park

Gwamna Raɗɗa Ya Kusa Kammala Tashar Mota Mafi Girma A Najeriya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

INSECURITY IN MALUMFASHI: A CLARION CALL TO SERIOUS ACTION

INSECURITY IN MALUMFASHI: A CLARION CALL TO SERIOUS ACTION

March 6, 2025
An Karrama Ɗanmadamin Yusufari Da Kambin Yabo Da Girmamawa

An Karrama Ɗanmadamin Yusufari Da Kambin Yabo Da Girmamawa

November 13, 2023
Nasarar Shari’ar Zaɓe: Ya Kamata Mu Mara Wa Shugaba Tinubu Baya – Janar Buratai

Nasarar Shari’ar Zaɓe: Ya Kamata Mu Mara Wa Shugaba Tinubu Baya – Janar Buratai

September 11, 2023
Hararar Baba Ganduje

Hararar Baba Ganduje

June 29, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?
  • Mu Ji Tsoron Allah
  • Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

Ko Me Ya Sa Manyan Mata Ke Auren Yara?

April 18, 2026
Mu Ji Tsoron Allah

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.