Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna
Daga Abdullah Yunus Abdullah

_______________
Gwamnatin Jihar Kaduna ta ƙaryata labaran da ke yawo a kafafen sada zumunta kan hukuncin da aka yanke wa Victor Solomon, wanda aka fi sani da Zidane, tana mai cewa labaran ƙarya ne kuma suna yaudarar jama’a. Ta jaddada cewa shari’ar ta gudana bisa gaskiya, doka da hujjoji ingantattu.
Da yake jawabi kan ce-ce-ku-ce da aka yi bayan hukuncin da aka yanke a ranar 6 ga Janairu, 2026, Babban Lauyan Jihar Kaduna kuma Kwamishinan Shari’a, Sir James A. Kanyip, KSM, PhD, ya bayyana cewa Victor Solomon ya fuskanci shari’o’i guda biyu daban-daban a gaban kotuna biyu, kan laifuka daban-daban da suka shafi mutane mabambanta.
“Babu wani saɓani a hukuncin kotunan da ake ta yaɗawa a yanar gizo. Victor Solomon an yi masa shari’a a shari’o’i biyu daban. An wanke shi a ɗaya a 2024, amma an same shi da laifi a wata shari’a a 2026 bisa hujjojin da aka gabatar a kotu,” in ji Kanyip.
Babban Lauyan ya bayyana cewa shari’ar farko — Lamba KDH/KAD/73C/2020 — wadda ta shafi haɗin baki wajen aikata laifi da yunƙurin kisan kai, ta ƙare da wanke Solomon a ranar 21 ga Mayu, 2024.
Sai dai shari’ar ta biyu — Lamba KDH/KAD/78C/2020 — ta shafi manyan laifuka ciki har da haɗin baki wajen aikata laifi, jikkata mutum ba tare da tsokana ba, da kisan kai wanda hukuncinsa kisa ne. An kammala wannan shari’a a Oktoba 2025, inda aka same shi da laifi kuma aka yanke masa hukuncin kisa ta rataya a ranar 6 ga Janairu, 2026.
“Kundin hukuncin ba na son zuciya ba ne ko siyasa. An bi dukkan ƙa’idojin shari’a, an saurari shari’a gaba ɗaya, kuma kotu ta yanke hukunci bisa hujjoji,” in ji Kanyip, yana mai ƙarawa da cewa, wanda aka yanke wa hukunci yana da damar ɗaukaka ƙara har zuwa Kotun Koli.
A nasa ɓangaren, Kwamishinan Yaɗa Labarai, Malam Ahmed Maiyaki, ya yi gargaɗi cewa yaɗa labaran ƙarya game da shari’o’i masu muhimmanci na iya barazana ga zaman lafiya.
“Yaɗa rabin gaskiya da labaran ƙarya kan hukuncin kotu abu ne mai haɗari. Yana iya tayar da hankula da haddasa tashin hankali ba tare da dalili ba. Mutanen Kaduna su riƙa tantance gaskiyar labari kafin yaɗawa,” in ji Maiyaki.
Gwamnatin Jihar Kaduna ta sake jaddada cewa a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani, CON, mulki zai ci gaba da tafiya bisa tafarkin doka, adalci da haɗin kai, tare da tabbatar wa al’umma cewa adalci a Kaduna zai kasance a bayyane kuma ba tare da son kai ba.













