BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (1)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi
A rayuwata, na jima da jin sunan garin Biu, wanda gari ne mai daɗaɗɗen tarihi a Jihar Borno. Haka kuma na fara haɗuwar mu’amala da mutanen Biu a shekarar 2006. Tun daga lokacin na fara maida hankali da duk wani mutumin Biu da na haɗu da shi. Haka kuma tun daga lokacin na ci alwashin kai ziyara wannan babban birni na al’umma mai karimci, al’umma jajirtattu, al’umma jarumai, al’umma masu kishin ilimi, al’umma masu kishi da son juna – al’ummar Babur/Bura.
Na fara haɗuwa da mutanen Biu ne a Kaduna, a 2006, lokacin da nake aiki a kamfanin jaridar Public Agenda, a matsayin Editan Adabi. Zainab Musa, tana ɗaya daga cikin jami’an Sashin Gudanarwa a kamfanin kuma ita ‘yar asalin ƙabilar Babur ce daga Biu, Jihar Borno. Zaman aiki ne ya kai iyayenta Kaduna.
Zainab budurwa ce mai kunya, mai girmama mutane. Haka kuma wani kyakkyawan hali nata da na ankara da shi, shi ne yadda take da riƙon addini. Kullum za ka same ta cikin wadataccen hijabi. Ga ta kuma da kaifin basira. A zaman da muke yi na hidimar aiki a kamfani ɗaya da ita, sai na fahimci cewa babu shakka Zainab ta fito ne daga gidan tarbiyya. Kasancewar masu azancin magana na cewa, barewa ba ta gudu ɗanta ya yi rarrafe, haka ya tabbatar mani da cewa, iyayenta masu tarbiyya ne. Tun daga lokacin na rubuta kalmar daraja a zuciyata, game da mutanen Biu.
Mutum na gaba da na haɗu da shi, wanda ya ƙara bayyana mani halayen girma da daraja daga al’ummar Babur, shi ne Musa Salihu. Shi ma kamar Zainab, na haɗu da shi ne ta hanyar aiki a Abuja. Bayan na bar aiki a kamfanin jaridar Public Agenda a Kaduna, na fara aiki da kamfanin Media Trust Limited, Abuja. Na fara aiki a sabuwar jaridar kamfanin mai suna Aminiya, a ranar 15 ga watan Yuni, 2006.
Musa Salihu yana ɗaya daga cikin jami’an Sashin Tallace-Tallace na kamfanin jaridar Daily Trust da Aminiya a lokacin da muka haɗu a 2006. Matashi ne mai barkwanci, mai fara’a kuma mai zumunci. Wata tarbiyya ta Musa da ta ƙara burge ni da shi, ita ce, shi matashi ne mai son addini. Ga shi da gaskiya da amana. Ga shi mutum mai son mutane da ƙaruwa – ba ya da baƙin ciki ko ƙyashi. Waɗannan halaye nasa suka sanya, duk da cewa ya bar aiki a Daily Trust, muka ci gaba da mu’amala da shi da zumunci har zuwa yau ɗin nan.
Musa ya ƙara mani yarda da aminci da mutanen Biu. Daga halayensa na ƙara fahimtar cewa lallai ‘yan ƙabilar Babur mutane ne sahihai. Haka ne mana – idan dai har Zainab a matsayinta na budurwa ta zama sahihiya, sannan Musa a matsayinsa na matashi amma ya kasance mai Dattako, to ina ga manyansu?
Hajiya A’isha Umar Yusuf, duk da cewa Bakanuwa ce a tsarin zaman gari amma asalin tsatsonta daga Biu ne, kasancewar mahaifinta ɗan asalin ƙabilar Babur ne. Ita ma na haɗu da ita a shekarar 2006, sanadiyyar aiki a Abuja. Ita ce Editar farko ta jaridar Aminiya, wadda kamfanin Media Trust Limited ke wallafawa a Abuja.
Ita ma mutum ce mai karimci, mai fiƙira da sanin yakamata. Tana da kishin addinin Musulunci, kamar kuma yadda ta kasance mace mai son gaskiya da adalci. Tana da kishin ilimi da taimakon harkar ilimi. Ita ma ta kasance wadda ta ƙara sanya mani ƙaunar al’ummar Babur, a matsayinsu na sahihan mutane, jakadu nagari.
Nagartaccen mutum na gaba kuma ɗan asalin garin Biu kuma ɗan ƙabilar Babur da na haɗu da shi a rayuwata, haɗuwa ta alheri, haɗuwa mai albarka, shi ne Dokta Bukar Usman, OON. Ba zan mance ba, a shekarar 2007 na fara haɗuwa da shi, a sanadiyyar mashahuran littattafansa na Taskar Tatsuniyoyi da kuma Gidauniyar Bukar Usman. Na haɗu da shi ne ta hanyar marubuci, Ado Ahmad Gidan Dabino.
Ta hanyar mu’amala da Dokta Usman na gama sallamawa, na gama amincewa da cewa kaso mafi yawa na mutanen Biu ko kuma in ce ‘yan ƙabilar Babur nagartattu ne, masu kishi da ƙaunar al’umma. Ta hanyar littattafansa da maƙalolinsa, na fahimci cewa al’ummar Biu masu kishin ƙasa ne, masu girmama ilimi ne.
Wasu manyan misalai da suka sake cusa mani so da ƙaunar mutanen Biu, sun haɗa da littafin tarihin rayuwar Dokta Usman, Hatching Hopes (Cikar Buri), inda na fahimci muhimmancin gaskiya, riƙon amana, jajircewa a kan nema, muhimmancin ilimi, muhimmanci da tasirin ladabi da biyayya da makamantansu, waɗanda suka zama tubalan da shi Dokta Usman ya taka ya gina rayuwarsa mai kyau da ban sha’awa, har ya cin ma gagarumar nasara.
Haka kuma, ta hanyar mashahurin littafinsa na Taskar Tatsuniyoyi, na fahimci cewa lallai ƙabilar Babur ma babbar al’umma ce da ta yi tarayya da manyan ƙabilun nahiyar Afirka wajen girmama al’ada da koya tarbiyya a gargajiyance.
Ta hanyar littafinsa mai suna Girl-Child Education in Biu Emirate – Early Years (Tarihin Ilimin Mata A Masarautar Biu), na fahimci cewa babu shakka matan Biu ba ƙashin yadawa ba ne ta fuskar ilimi da yi wa al’umma hidima.
Babban goro, in ji masu azancin magana, sai magogin ƙarfe. A sanadiyyar mashahurin littafin Dokta Usman, A History of Biu (Tarihin Biu), na fahimta da irin girma da ɗaukakar da Allah Ya yi wa al’ummar Biu da ƙabilarsu ta Babur/Bura. Tarihin jarumi kuma muzakkarin mayaƙi Yamtarawala, na fahimci cewa mutanen Babur, ƙabila ce jarumai, marasa tsoro. Haka kuma na fahimci irin ni’imomi da albarkatun ƙasa da Allah Ya zuba a wannan yanki na Biu.
Wani mashahurin mutum na gaba da na haɗu da shi, wanda ya fito daga ƙasar Biu, shi ne Laftanar-Janar Tukur Yusufu Buratai, CFR, (mai ritaya), tsohon Hafsan-Hafsoshin Rundunar Sojojin Najeriya. Tun a farkon shekarar 2015 na naƙalce sunan Janar Buratai, musamman lokacin da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ambata shi a matsayin Shugaban Rundunar Sojojin Najeriya. Tun daga lokacin na yi ta bibiyar al’amuransa, har ta kai ga Allah Ya sanya na haɗu da shi.
Na haɗu da Janar Buratai ne ta hanyar Birgediya-Janar Sani Usman Kuka-Sheƙa (mai ritaya), inda ta kai ga har na yi aikin fassara littafin tarihinsa mai taken The Legend of Buratai zuwa harshen Hausa. Janar Buratai – halayensa na jarumtaka, jajircewarsa wajen nuna kishin ƙasa, kishinsa na ilimi da taimakon al’umma, su suka ƙara tabbatar mani da cewa lallai al’ummar Babur mutane ne zaɓaɓɓu kuma na musamman. Kuma hakan ya ƙara ta’azzara sha’awata ta son ziyartar wannan babban yanki na Biu – Babban Birni A Saman Tsauni.
A takaice, haɗuwa ta da Dokta Usman da Laftanar-Janar Tukur Yusufu Buratai (mai ritaya) da sauran mashahuran mutanen nan da na ambata, waɗanda suka fito daga Biu, ta sanya mani ƙishirwa da kwaɗayin ganin na ziyarci wannan babban gari na Biu mai ɗimbin tarihi, mai al’adun gargajiya na burgewa, mai tsaunuka da duwatsu masu ban al’ajabi.
Na sha alwashin lallai sai na je garin domin in gane wa idona wuraren tarihi, mazaunin Yamtarawala da maƙabartar sarakunan Biu mai abin al’ajabi da Tsaunin Tilla da Tafkin Tilla. Na sanya wa raina sha’awar zuwa garin Biu, domin ganin yadda tsarin sarautarsu ta gargajiya take, domin in ga yadda irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da raye-rayensu na gargajiya suke.
Allah maji roƙon bawanSa! Allah cikin ikonSa, Ya sahale mani, na ziyarci birnin Biu. Na isa birnin a ranar Laraba, 25-10-2023, inda na kwashe tsawon kwanaki bakwai cur. Na ziyarci muhimman wuraren tarihi da cibiyoyin ilimi da masarautar Biu. Na gana da mashahuran mutane maza da mata, ciki har da Mai Martaba Sarkin Biu, Alhaji (Dr). Mai Mustapha Umar Mustapha Aliyu II, CON. Na gana da sabon Betaran Biu da aka naɗa a makon, Laftanar-Janar Tukur Yusufu Buratai, CFR (mai ritaya).
Na samu jagoranci da kulawa na musamman daga jajirtaccen aboki, mai kishi da ƙaunar ilimi, Malam Umar Mohammed Midala, wanda bai yi ƙasa a gwiwa ba, bai yi kasala ko nuna ƙosawa da ni ba. Shi ya yi mani jagora zuwa dukkan muhimman wurare da sada ni da dukkan mashahuran mutanen da na tattauna da su.
Ku biyo ni a kashi na biyu na wannan rahoton ziyara, domin jin yadda na isa birnin Biu da abubuwan da na gani da kuma muhimman bayanan da zan ƙarar dangane da al’ummar Babur/Bura da babban birninsu mai ɗimbin tarihi – Biu.













