KTSTA: HARKAR SUFURI A HANNUN GWANI (3)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

•••••••
A wannan rahoto kashi na uku, za mu kammala bayani ne game da taƙaitaccen tarihin Shugaban Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina (KTSTA), Malam Haruna Musa Rugoji, kamar yadda muka faro a rahoto kashi na biyu.
Tarihinsa ba zai cika ba, sai mun waiwayi baya, yadda ya samu ƙwarewa a harkar sufuri, tun ma kafin ya samu kansa a wannan muƙami a KTSTA.
A can baya, ya yi gwagwarmayar tuƙin babbar mota (DAF), mallakin mahaifinsa. Malam Haruna ya shahara kuma ya yi tashen da duk sai da kowace kasuwar shanu da ke Arewa aka san shi. A lokacin, ana yi masa lakabi da Haruna D.K. A wancan lokaci, saboda jajircewa da ƙoƙarinsa a fagen tuƙi, cikin kwana biyu yake zuwa da juyowa ga Legas daga Arewa; alhali wasu direbobin sai sun yi mako guda a kan hanya.

Baya ga harkar sufuri, Malam Haruna kuma ɗan siyasa ne – amma mai ingantaccen ra’ayi – bai yarda da siyasar ko-a-mutu-ko-a-yi-rai ba. Ba ya fitowa takara kai tsaye, sai dai idan al’umma sun tsayar da shi don ƙashin kansu. Dukkan yunƙure-yunkuren da ya yi a baya na takarar Ciyaman ko Ɗan Majisar Jiha, wasu ƙungiyoyin mutane ne suka buƙaci ya tsaya, domin sun aminta da cewa zai kawo gyara a hidimar al’umma.
Hannu ɗaya, masu iya magana sun ce ba ya ɗaukar jinka. A matsayinsa na ƙwararre a fannin kasuwanci da sufuri, Malam Rugoji yana cikin cibiyoyi da ƙungiyoyin ƙwararru daban-daban. Shi mamba ne a waɗannan ƙungiyoyi, makarantu da cibiyoyin ƙwararru: Institute of Corporate Executive of Nigeria da Institute of Transport Administration of Nigeria da Chartered Transport – The Council for the Registration Transportants in Nigeria da Institute of Industrialists and Corporate Administrators of Nigeria da Charted institute of Transport and logistics London, UK da Fleet Management in Road Transport Operations by the Nigerian Institute of Transport Technology (NITT).
Wani al’amari da ke taimakon Rugoji a rayuwa shi ne, yadda Allah ya ba shi ilimin addinin Musulunci, ga shi kuma da hikimar magana. Yana da zurfi da kaifin tunani, a yayin ɗaukar wani mataki ko zartar da al’amari. Ya iya magana, karatu da rubutu da yaruka uku manya – Hausa, Ingilishi da Larabci. Duk inda zai shiga a duniya, ba ya bukatar tafinta, domin duk runtsi za a iya samun mai magana da ɗaya ko dukkan waɗannan yaruka uku.

Haka kuma ya iya lissafi da ƙididdiga. Yana da ɗabi’ar bin diddigin matsala da gano hanyoyin warware ta cikin sauri. Yana da daraja lokaci a dukkan lamurransa. Yana da biyayya ga shugabanni, yana daraja doka da oda da ƙa’idojin hukuma ko waɗanda aka gindaya domin maslahar al’umma. Yana daraja mutane manya da na ƙasa da shi kuma ya iya aiki a ƙungiyance tare da ba kowa haƙkinsa.
Wani babban tambari da ya bayyana a cikin halayensa, wanda duk mutumin da ya yi mu’amala da shi zai shaida shi ne, shi mutum ne mai tsananin kwatanta gaskiya da adalci. Mutum ne mai ƙoƙarin cika alƙawari – kaifi ɗaya. Ba ya da nuƙu-nuƙu, idan zai yi abu to zai yi, idan kuwa bai natsu da abu ba, to ba zai yi ba.
Yaba kyauta, an ce tukwici! Malam Rugoji ya samu kyaututtuka da lambobin yabawa da yawa. Misali, ya samu Takardar Yabo ta Ƙasa daga Fadar Shugaban Ƙasa (National Productivity Order of Merit Award), wacce Shugaban Ƙasa Janar Muhammadu Buhari (Allah ji ƙan shi ) ya miƙa masa a ranar 10 ga Mayu, 2022. Ya taɓa samun Takardar Yabo ta Musamman (sau biyu) daga Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina, a ranar 30 ga Maris, 2022 da kuma wacce aka ba shi a ranar 9 ga Janairu, 2023 saboda yabawa da ƙwazonsa a aiki. Haka kuma ya samu wata karramawar a matsayin Gwarzon Hadimin Al’umma a Fannin Sufuri a Jihar Katsina da Ƙasa Baki Ɗaya (2018 – 2019). Sauran karramawa da yabo daga ƙungiyoyin al’umma, makarantu da cibiyoyi kuwa, ba za su lissafu ba cikin sauri.

Malam Haruna Musa Rugoji, shi mai sarauta ne a Fadar Galadiman Katsina Hakimin Malumfashi, Justice Saddik Abdullahi Mahuta, OFR. Shi ne Ubandawakin Galadiman Katsina. Yana da kyakkyawar shaida da aminci daga Mai Girma tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, CFR da Farfesa Y. Haruna na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa University of Technology Bauchi, CSP. Saleh M. Abdulhameed.
A rahoto na gaba, kashi na 4, in sha Allahu za mu duba irin wainar da Malam Rugoji yake toyawa a wannan hukuma mai albarka ta KTSTA, a matsayinsa na shugaba. Shin yaya ya samu ma’aikatar a 2018 kuma zuwa yanzu yaya take?
_______________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago (online)












