SHIN KO GAMAYYAR ‘YAN ADAWA NA JAM’IYYAR ADC ZA SU IYA KADA TINUBU A 2027?
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Yayin da kakar zaɓe ta 2027 ke ƙara matsowa, yanayin siyasar Najeriya yana ƙara ɗaukar zafi, inda wasu jigajigan ‘yan siyasa ɓangaren adawa suka yi gangami tare da haɗewa a inuwar Jam’iyyar ADC (African Democratic Congress). Wani abin lura shi ne, waɗannan jigajigai, sun fito ne daga sassa daban-daban na ƙasar nan, kamar kuma yadda suka kasance masu mabanbantan ƙabilu da addinai. Kuma rabon da a ga irin wannan gamayya, tun a 2013, lokacin da aka haifar da babbar jam’iyar adawa ta APC. Babban burin wannan gamayya shi ne, su ƙwace mulki daga Shugaban Ƙasa da ke kan kujera a yanzu, Bola Ahmed Tinubu; kamar dai yadda waccan gamayya ta tunɓuke Shugaban Ƙasar lokacin, Goodluck Jonathan.
Wannan gamayyar ta haɗa manya kuma fitattun ’yan siyasa na Najeriya. Ana maganar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, tsohon Gwamnan Jihar Anambra Peter Obi, tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa David Mark, da sauransu.
Wata babbar ayar tambaya ita ce, shin anya wannan gamayyar ‘yan siyasa masu mabambantan aƙidoji da halayya da tarihi, da mabambantan buƙatu da suka fito daga sassa daban-daban na ƙasar nan, za su iya shan inuwa ɗaya a siyasa kuma su yi nasara? Shin jam’iyyar ADC da aka daɗe ana kallon ta a matsayin ƙaeama, ko za ta iya zama dandalin siyasa ta ƙasa gaba ɗaya? Wannan muƙala za ta yi nazarin wannan gamayya, yanayin ƙarfinsu, ƙalubalen da ke gabansu da kuma duba yiwuwar ko za su iya yin nasara ko akasi.
Shin su wane ne jigogin ‘yan siyasar da ke cikin wannan gamayya? Tabbas idan ka duba fuskokin ‘yan siyasar da suka ƙulla wannan babban ƙawance, za a iya kiransu da kankat na shahararru a siyasar Najeriya. Ana maganar Atiku Abubakar – gogaggen ɗan siyasar da ya daɗe yana takara, wanda kuma yake da karɓuwa a Arewa maso Gabas da sassa da dama na ƙasar nan. Ga Peter Obi – ɗan siyasa mai goyon bayan matasa, kuma wanda ya ƙware wajen naƙaltar nazarin yadda ake samun ci gaba da kawo sauyi a wasu ƙasashen duniya a siyasance. Ya samu karɓuwa daga matasa da mata a zaɓen Shugaban Ƙasa da ya gabata, a 2023.

Akwai Malam Nasir El-Rufai – mutumin da ba ya shakkar magana kuma ba ya tsoron ta bakin mutane. Ga shi kumma ƙwararren masanin tattalin arziƙi, kuma ya kafa tarihi a dukkan wuraren da ya yi mulki, tun daga kan Babban Darakta, zuwa Ministan Abuja da kuma mulkinsa na shekara takwas a matsayin Gwamnan Jihar Kaduna. Akwai Aminu Waziri Tambuwal – wanda ya kasance tamkar gada tsakanin tsofaffi da matasa a siyasance, wanda kuma yake da idanu a tsakanin ‘yan siyasar Arewa da na Kudancin Najeriya.
Tsofaffin Gwamnoni, Rotimi Amaechi, Rauf Aregbesola da Sule Lamido jigogi ne na gaban sahu, masu tasiri a siyasance, a yankin Kudu maso Kudu, Kudu maso Yamma, da Arewa maso Yamma. Sauran jigajigan su ne manyan masana harkokin Shari’a da kamar Abubakar Malami (SAN) da kuma soja, Air Marshal Sadique Abubakar (mai ritaya). Don haka waɗannan ba kawai taron ’yan siyasa masu karsashi da tasiri ba ne, babbar gamayya ce da ta haɗa sassa daban-daban na ƙasa, waɗanda za su iya tunkarar kowane irin ƙalubale daga kowane ɗan siyasa a Najeriya.

Bari mu duba irin awon ƙarfinsu da irin damar da suke da ita. Ta fuskar wakilcin ƙasa gaba ɗaya, wannan ƙawance ya haɗo kan dukkan shiyyoyin siyasa guda shida na ƙasa, wanda wannan kaɗai wata alamar nasara ce a siyasar Najeriya, wacce ke cunkushe da rarrabuwar kai. Madamar haɗin kan ya ɗore kuma suka tafi a ɗinke yadda ya kamata, al’amarin zai iya samar da martabar haɗin kan ƙasa da karya tsarin fifita yanki ɗaya da aka saba da shi a harkar siyasar Najeriya.
Ta ɓangaren goyon bayan matasa kuwa, bisa la’akari da yawan matasa da ake watsi da su a siyasa, akwai yiwuwar wannan gamayya ta iya janyo hankalinsu, musamman ta hanyar Peter Obi, wanda ya zama ginshiƙin da matasa suka ba amanna a zaɓen da ya gabata a 2023. Zai iya haifar da yawan fitowar masu kaɗa ƙuri’a, musamman a yankin Kudu maso Gabas, Kudu maso Kudu da jihohin Arewa ta Tsakiya.
Idan aka zo batun hikimar murza zaren siyasa kuwa, akwai ƙwararru a wannan fannin, kamar Atiku, Tambuwal da Amaechi. Suna da ƙarfaffen tsarin siyasa daga tushe. Haka nan shi ma Ahmad Mu’azu, tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP; sananne ne wajen tafiyar da ƙungiyoyi a siyasance.
Haka kuma idan aka zo kan batun ƙwararru da masana harkokin sarrafa al’amura, mutane irinsu El-Rufai, Peter Obi da Sadique Abubakar, za su iya tallata wannan sabuwar tafiya, har su ga sun kafa gwamnati, ta hanyar jawo ra’ayin masana irinsu, musamman ma wajen mayar da hankali kan tsaro, gyare-gyaren gine-gine da harkokin raya al’umma da farfaɗo da tattalin arziki – waɗanda su ne muhimman batutuwa ga matsakaitan talakawa da ma’aikata.
Wane irin canji za su iya kawo wa al’umma, domin magance halin matsi da takura da al’ummar ƙasa suke ciki? Yadda al’umma suka nuna gajiya da APC da PDP, hakan na iya taimaka musu. Domin kuwa yawancin ’yan Najeriya suna neman wata hanyar tsira ta daban da za ta ceto su daga ƙuncin da suke kukan jam’iyyun biyu suka jefa su. Ana maganar yadda tattalin arziki da tsaro suka taɓarɓare da kuma yadda rayuwar yau da kullum ta zama mai wahala ga talaka.
Ko ina maganar kuɗin ɗawainiya da kayan aikin wannan hidima za su fito? Maganar gaskiya ba su da matsalar kuɗi, musamman idan muka yi la’akari da hamshaƙan attajirai, kamar Atiku da Amaechi da sauransu. Tabbas za su iya karo-karo su haɗa kuɗaɗe da samar da kayan aikin yaƙin neman zaɓe.

Kowace tafiya, musamman ta siyasa, ba za ta rasa ƙalubale ba. Kan haka, ita ma wannan tafiya ta ADC, akwai manyan ƙalubale da ka iya kawo masu cikas, idan ba su taka da lura ba. Wannan kuwa ya haɗa da rikicin ra’ayi da buri, domin kuwa wannan gamayya ta haɗa mutane masu ra’ayoyi da buri daban-daban. A cikinsu akwai masu ƙarajin neman canji kuma akwai masu ra’ayin ’yan mazan jiya da kuma masu goyon bayan jama’a. A yayin da mutane irin su Peter Obi ake masu kallon masu don kawo canji da tsabtace hanyoyin bunƙasa tattalin arziƙi, su kuwa irinsu Malami, ana kallon su a matsayin wakilan ‘yan mazan jiya a siyasa. Wannan bambanci, idan ba a samu daidaito ba, yana iya hana samun haɗin kai daga magoya baya, ya haifar da rigingimu a tsakani.
Wani ƙalubale kuma da ka iya zama matsala, shi ne batun fitar da ‘yan takara, musamman ma na Shugaban Ƙasa. A yayin da Atiku zai iya cewa shi ya fi cancantar takara bisa gogewarsa, Shi ma Obi yana iya dagewa, domin yana da goyon bayan matasa. Haka ma Tambuwal da Amaechi, suma suna iya yi wa kansu tayin wannan takara. Idan har ba su cin ma matsaya ba tun da wuri ba, ƙawancen na iya tarwatsewa nan gaba.
Matsalolin ƙabilanci da bambancin addini, su ma ƙalubale ne da ka iya kawo wa wannan tafiya cikas. Siyasar Najeriya har yanzu tana ƙunshe da yoyon kishin ƙabila da addini. Daidaita tsakanin Arewa da Kudu, da Musulmi da Kirista zai buƙaci kulawa. Duk wani fifiko da za a nuna wa wani ɓangare, yana iya tayar da hankali ko rage magoya baya.
Raunin Jam’iyyar ADC ma abin la’akari ne ta fuskar ƙalubale. Jam’iyyar ba ta kafu ba sosai a Jam’iyyar a jihohi da dama. Aikin sama mata amsuwa, ta karaɗe dukkan sassan ƙasa baki ɗaya, cikin ƙasa da shekara biyu, babban aiki ne. Amma da irin waɗannan fitattun ‘yan siyasa da ke cikinta, hakan zai iya yiwuwa.
Wani ƙalubalen kuma shi ne, tasirin Shugaba Tinubu, a matsayin wanda zai yi takara kuma yana kan mulki. A halin yanzu dai shi ke sarrafa harkokin gwamnati, shi ke da tasarrufin jam’iyya mai mulki (APC), kamar kuma yadda yake da cikakken iko kan hukumomi, ciki har da ta zaɓe (INEC). A irin wannan yanayi, kada Shugaban Kasa mai ci, ba abu ne mai sauƙi ba. Sai dai talakawan Najeriya na cikin wahala saboda tsauraran matakan tattalin arziki da gwamnatinsa ke aiwatarwa, hakan na iya zama sanadiyyar faɗuwarsa.
Gajiya da tsarin zaɓe, shi ma ƙalubale ne. Yawancin ’yan ƙasa sun gaji da yadda tsarin zaɓe ke gudana, don haka ana iya samun kaso mai yawa da zai ƙi fita zabe. Don haka, idan ba an yi da gaske ba, jam’iyyun adawa za su iya samun tasgaro, domin ana iya yin maguɗi, sakamakon ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a ko kuma a murɗa sakamakon. Ya kamata su yi taka-tsantsan kuma su ɗauki salon da Buhari ya yi amfani da shi a 2015 na “A Kasa – A Tsare – A Raka – A Ƙirga.”
Bari mu juyo kan babbar tambayarmu – shin ko wannan jigajigan ‘yan gangamin adawa za su iya doke Tinubu a 2027? Za su iya – idan suka cin ma matsaya cikin lumana, kan ɗan takarar Shugaban Ƙasa tun da wuri kuma suka tafi cikin haɗin kai.
Za su iya samun nasara, idan suka ja matasa sosai cikin tafiyarsu, sannan su samar da tsari da alƙawari na gaskiya game da gyara tattalin arziƙin ƙasa da dama wa al’umma sana’o’i da ayyukan yi.
A hannu ɗaya kuma, gamayyar ‘yan adawar ba za su iya kayar da Tinubu ba, idan har suka bari rikice-rikicen cikin gida suka samu galaba a tsakaninsu, musamman dangane da fitar da ɗan takara mai tasiri. Haka ma Idan suka gaza fito da sabuwar manufa ta kawo sauƙin rayuwa ga al’umma, suka maimaita abin da PDP/APC suka yi, ba za su samu nasara ba.
Haka ma idan har Tinubu ya daidaita tattalin arziki, ya gina ababen more rayuwa da amfani da albarkatun gwamnati wajen yaƙin neman zaɓe, to lallai ‘yan adawa da wuya su samu nasarar kawar da shi. Idan ADC ta kasa samun amincewar jama’a ko ta kasa fitar da ƙwararan ’yan takara da mutane ke so a matakai daban-daban, to tana iya rasa nasara.
Daga ƙarshe, wannan gamayya ta ‘yan adawar siyasa, ita ce gagarumar ƙawance mafi tagomashi da aka kafa a Najeriya gaba ɗaya cikin shekaru aru-aru. Amma tarihi ya nuna cewa buri kaɗai ba zai wadatar ba. Abin da suka fi buƙata yanzu shi ne jagoranci mai hangen nesa, tsari mai ma’ana, da kuma ɗa’a da ƙwazo wajen fifita gina ƙasa fiye da son kai. Idan har ADC ta gaza wajen samar da haɗin kai, amincewa da manufa, za ta zama ɗaya daga cikin jerin ƙawance da suka mutu a tarihin siyasar Najeriya. Amma idan ta yi nasarar fidda hanyar da ta dace da sauya salo, to wataƙila ita ce jam’iyyar da za ta rubuta sabon tarihin siyasa a 2027.
_______________
Bashir Malumfashi shine Editan Taskar Gizago Magazine (online)
📩 bashiryahuza47@gmail.com













An gaishe ka Fasihin Galadiman mu. Gaskiya ka ka fiddo da matsaloli da Kuma hanyoyin samun nasara ga kowanne bangare ba tare da daukar bangare guda ba
To mu dai a gaskiya Muna bangaren cin nasara ga Yan adawa saboda halin da muke ciki Kuma muddin gwamnati Mai ci bata canza salo ba to babu shakka duk matsalon da ka hango wadanda za su iya kawo ma Yan adawa cikas to ba za su yi tasiri ba!
Madalla da wannan tsokaci. Allah ya ba mu Sa’a. Amin