• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, March 8, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Na Wallafa Littattafai 89 A Shekara 25 – Sadiya Yakasai

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 12, 2023
in Adabi
0
Na Wallafa Littattafai 89 A Shekara 25 – Sadiya Yakasai

Sadiya Garba Yakasai

131
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Na Wallafa Littattafai 89 A Shekara 25 – Sadiya Yakasai

Related posts

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Let’s Speak Our Mother Tongue

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

March 6, 2026
Sabon littafin Sadiya Garba Yakasai
Sadiya Garba

~~~~~~~I

dan ana maganar rubutun littattafan soyayya a wannan zamanin, sunan Sadiya Garba Yakasai ya zama tamkar hantsi, wanda ya leƙa gidan kowa. A tattaunawar ta da TSAKAR GIZAGO, marubuciyar, wacce ta fara rubutu tun tana makarantar sakandare, ta bayyana muhimman al’amura dangane da harkar rubuce-rubuce:

~~~~~~~

TG: Kina ɗaya daga cikin marubuta na dauri, ko za ki gaya mana tarihinki a taƙaice?

SADIYA: Sunana Sadiya Garba Yakasai.An haife ni a Unguwar Yakasai, cikin birnin Kano. Shekaruna 46. Na yi karatu tun daga firamare da sakandare kuma na yi Diploma a fannin girki da kayan ƙawa na gida, ma’ana kamar kwalliyar gida da suka haɗa da kamar zannuwan gado, kamfala, jera sarƙoƙi da ‘yan kunne na duwatsu da sauran su.

TG: Tun yaushe kika fara rubutu kuma mene ne ya ja ra’ayinki ga harkar rubuce-rubuce?

SADIYA: A gaskiya na fara rubutu tun ina makarantar sakandare. Hakan ya samo asali ne idan na zo hutu ina saye littattafan Hausa in karanta. Tun a lokacin ne sha’awar hakan ta ɗarsu a raina kuma ya zuwa yanzu sai dai mu ce alhamdu lillahi a fannin rubuce-rubuce. Na fara wallafa littafi ya shiga kasuwa tun a shekarar 1998 kuma har zuwa yau ina wallafawa.

TG: Ya zuwa yanzu, littattafai nawa kika rubuta? Guda nawa aka buga a littafin takarda kuma nawa kika buga a intanet?

SADIYA: Ya zuwa yanzu na wallafa littatafai guda 89 kuma duk an buga su, sun shiga kasuwa. A batun wallafa a intanet kuwa, ya zuwa yanzu ban taɓa saka wani littafina ba gaskiya.

TG: Waɗanne irin matsaloli kike fuskanta a matsayinki na marubuciya?

SADIYA: Alhamdu lillahi. Ni dai ba na fuskantar kowacce matsala, musaan ma a Soshalmidiya, inda aka fi hayaniya saboda ba na shiga sabgogin da zan fuskanci matsala. Ina zaune da kowa lafiya, da mutunci muke zaune da juna.

TG: Tun daga fara rubutu, waɗanne irin nasarori kika samu ko kuma akasin su?

SADIYA: Alhamdu lillahi, nasarori na samu ta kowace fuska saboda faɗar su ma kamar ragewa ce. Na samu nasara ta jama’a daga garuruwa, na samu ta fannoni da dama, duk ta dalilin rubutu. Babu abun da zan ce sai godiyar Allah. Duk da cewa duk ɗan Adam ba ya rasa wasu abubuwa, to ni dai kam sai godiya; alhamdu lillah.

TG: A harkar rubuce-rubuce, waɗanne marubuta ne gwanayenki, da kike koyi da rubutunsu?

SADIYA: Ina da gwanaye da yawa gaskiya, duk littafin da ya yi mani, ina yaba wa marubucin ko marubuciyar. Sai dai dole akwai waɗanda kake so su yi rubutu, har jira nake su ce ga littafi ya fita. Irin waɗannan sun haɗa da Bala Anas, Ibrahim Mandawari, Zaharadeen Yakasai, Balaraba Ramat, Hafsat Abdulwaheed da Bilkisu Funtuwa.

Haka kuma akwai Hafsat Sodangi, marigayiya Halima Ama, marigayiya Jamila Ɗanfajo da Fatima Ɗanbarno da Fauziyya D. Sulaiman, Maimuna Beli, Bilkisu Yusuf, Rahma Abdulmajid da Nazir Adam Salihi.

Sauran sun haɗa da Sumaiyyah Takori, Nasir Nid, Kabiru Anka, Umma Sulaiman, Zulaiha Kagara, Asma’u Lamiɗo, Halima K/Mashi da Sadiya KD da sauransu da dama, domin kuwa gwanayen nawa suna da yawa.

Game da koyi da salon rubutun wasu kuwa, gaskiya ba na koyi da na kowa. Ina amfani da salon rubutun kaina saboda kowa da irin tasa baiwar. Gaskiya nawa salon na daban ne.

TG: An daɗe ba a ji ɗuriyarki da sabon littafi ba, shin me ya faru, ko kin daina buga littafi ne?

SADIYA: Hakan ya faru ne a sakamakon faɗuwar kasuwa da muka samu sai rubutu ya koma intanet. Dole ta sa na ajiye alƙalami amma ba don na daina ba, sai dai yanzu na kuma ɗaukar alƙalami ina rubuta sabon littafina mai suna “Kuskure Ko Ganganci?” Wannan shi ne wanda zai fito nan gaba kaɗan in sha Allahu Rabbi.

TG: Wasu marubuta sun koma rubutun fim, ko ke ma kina da shirin haka?

SADIYA: E to, gaskiya dai a yanzu ban da ra’ayi, ban sani ba ko nan gaba ba, tun da komai kira ne na Allah, in da rabo zan yi.

TG: Mene ne babban burinki dangane da rubutu?

SADIYA: Babban burina a rubutu shi ne, Allah daɗa bunƙasa shi, domin ni ina da kishin sa, kullum fatana rubutu ya ci gaba da yaɗuwa a duniya. Sannan ina da burin Allah Ya ba ni ikon kammala rubuta littafin gajerun labarai a kan maudu’in ta’addanci guda ɗari da nake kan rubutawa. Ina roƙon Allah Ya ara mani wannan damar, domin in ga na gama da shi.

TG: Ko kina da wani kira ga gwamnati da marubuta ‘yan uwanki da kuma al’umma masu karanta littattafanki?

SADIYA: Gwamnati, ina kira da ta bai wa marubuta daraja domin ina ga daga Malami sai Marubuci a ƙulafucin zaƙulo abubuwan rayuwa masu amfani, yana da kyau a ce gwamnati na girmama marubuci domin shi ba abun yasarwa ba ne amma har gobe ba mu da wannan gatan.

Ina kira ga marubuta ‘yan uwana, su riƙa zaƙulo hanyoyin magance matsalolin da matasanmu yanzu suke ciki game da shaye-shaye; yadda za a daƙile wasu abubuwan da suke yi, ta hanyar rubutunsu. Sannan iyaye su sa ido a kan tarbiyyar yaransu mata da maza, don yanzu tarbiyya ta yi ƙaranci.

Ina yi wa duk masu karatun littattafaina da masu bin rubuce-rubucena na filin Tarbiiyya a Mujallar Manhaja fatan alheri da kuma nuna jin daɗin yadda suke yaba wa filin nawa. Ni ma ina jin daɗin yadda suke yabawa da yi mini fatan alheri bisa wasu da yawan abubuwan da nake rubutawa yana musu tasiri don suna fuskantar wasu abubuwa da ke faruwa na rayuwa. Ina musu fatan alheri.

Previous Post

Zamantakewa: Kowace Mace Na Buƙatar Namiji Kusa Da Ita

Next Post

Tsarin Mulki: Jan Hankali Ga Shugabannin Arewa

Related Posts

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
Let’s Speak Our Mother Tongue
Adabi

Mu Yi Kishi Da Alfahari Da Harshen Uwa

March 6, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)
Adabi

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (2)

March 1, 2026
Next Post
Tsarin Mulki: Jan Hankali Ga Shugabannin Arewa

Tsarin Mulki: Jan Hankali Ga Shugabannin Arewa

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Ƙungiyar CAN Ki Daina Yi Wa Musulmi Kutse – YUSUF Dingyaɗi

Ƙungiyar CAN Ki Daina Yi Wa Musulmi Kutse – YUSUF Dingyaɗi

March 4, 2025
KAMUN LUDAYIN JEMAGE

KAMUN LUDAYIN JEMAGE

July 23, 2023
RAMADAN KARIM: 10-1447

RAMADAN KARIM: 10-1447

February 27, 2026
AN DAKATAR DA MALAMIN MUSULUNCI DAGA YIN WA’AZI

AN DAKATAR DA MALAMIN MUSULUNCI DAGA YIN WA’AZI

November 19, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • RAMADAN KARIM: 19-1447
  • FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
  • RAMADAN KARIM: 18-1447

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

RAMADAN KARIM: 19-1447

RAMADAN KARIM: 19-1447

March 8, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.