• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, June 15, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

AIKIN RUWA A MALUMFASHI: AN BUƘACI AL’UMMA SU BA HUKUMA HAƊIN KAI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 16, 2025
in Babban Labari
0
AIKIN RUWA A MALUMFASHI: AN BUƘACI AL’UMMA SU BA HUKUMA HAƊIN KAI

Daga Hagu: Alhaji Jibrin Sama'ila Jibson, Injiniya Tukur Tingilin da Injiniya Muntari Sagir

28
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

AIKIN RUWA A MALUMFASHI: AN BUƘACI AL’UMMA SU BA HUKUMA HAƊIN KAI

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Sojan Gona: An Kama Sojan Bogi Mai Muƙamin Manjo-Janar

Sojan Gona: An Kama Sojan Bogi Mai Muƙamin Manjo-Janar

June 12, 2026
Kotu Ta Ayyana Hausawa Da Fulani Halastattun ‘Yan Ƙasa A Jihar Filato

Kotu Ta Ayyana Hausawa Da Fulani Halastattun ‘Yan Ƙasa A Jihar Filato

June 11, 2026
Daga Hagu: Alhaji Jibrin Sama’ila Jibson, Injiniya Tukur Tingilin da Injiniya Muntari Sagir

 

An buƙaci al’ummar Ƙaramar Hukumar Malumfashi da kewaye da su kai hankali nesa, su ba Hukumar Ruwa ta Jihar Katsina da Manajan Daraktanta, Injiniya Tukur Hassan Tingilin goyon baya da haɗin kai, domin ganin an kammala aikin sabunta bututun ruwa cikin nasara, domin amfanin al’umma gaba ɗaya.

Wannan kira ya fito ne daga bakunan jajirtattun masu kishin Malumfashi, Injiniya Muntari Sagir da kuma Alhaji Jibrin Sama’ila (Jibson). Kiran nasu yana zuwa ne a sakamakon wata rashin fahimta da ta faru a kwanakin baya, dangane da aikin ruwan da ake gudanarwa a garin na Malumfashi.

Rashin fahimtar ta faru ne, inda aikin binne sabbin bututun ya shafi bakin shagunan wasu ‘yan kasuwa da ke bakin titi; waɗanda suka yi ta ƙorafi da nuna rashin yarda da aikin.

A tattaunawarsa da wakilinmu, Alhaji Muntari Sagir, shugaban kamfanin gine-gine na Muntasarab, ya shawarci al’ummar Malumfashi da kewaye, da su riƙa yin haƙuri da hukuma da jami’anta, musamman dangane da aikin da zai amfani al’umma. A cewarsa, “wannan aikin ruwa zai amfani al’umma ne gaba ɗaya. Mutane ba za su gane tasiri da muhimmancinsa ba sai nan gaba.”

Injiniya Muntari ya ƙara da cewa ya kamata al’ummar Malumfashi da kewaye, su riƙa nuna goyon baya da ƙarfafa wa mutanensu da suka samu dama a gwamnati gwiwa, maimakon cin zarafi da nuna rashin godiya.

“Ya kamata mutane su fahimta da cewa, kishin Malumfashi ne ya sanya Tukur Tingilin ya kawo aikin inganta samar da ruwan sha a garin. Goyon baya da ƙarfafa gwiwa yake buƙata ba tozarci ba.” Inji Muntari Sagir.

Haka kuma ya yaba wa M. D. Tukur Tingilin bisa yadda yake taimakon al’umma ta ɓangaren inganta ilimin yara da sauransu. Sai dai ya shawarce shi da cewa ya daina biye wa masu sukarsa, ya riƙa kauda kai daga abin da za su faɗa, ya daina cewa zai maida masu da martani.

A nasa ɓangaren shi ma, Alhaji Jibrin Sama’ila (Jibson), shugaban kamfanin JIBSON NASAKA INVESTMENT, yabawa ya yi da aikin ruwan da ake gudanarwa a garin Malumfashi. Kamar kuma yadda ya nuna yabo ga Injiniya Tukur Tingilin, wanda ya yi tsayin daka wajen tabbatutuwar aikin.

“Ina kira ga wasu matasa masu hawa Soshalmidiya suna rashin kunya da tozarta manya, cewa hakan da suke yi, ba daidai ba ne. Ku riƙa daraja manya kuma idan kuna da ƙorafi ko wata shawara ga jami’in gwamnati, ku riƙa gabatar da su cikin hikima da ladabi, ba da tozarci ba.” In ji Alhaji Jibrin.

Previous Post

WATER PROJECT IN MALUMFASHI: COMMUNITY URGED TO SUPPORT GOVERNMENT

Next Post

THE PUNCH EDITORIAL ON BENUE: A FABRICATION IN SEARCH OF A SCAPEGOAT

Related Posts

Sojan Gona: An Kama Sojan Bogi Mai Muƙamin Manjo-Janar
Babban Labari

Sojan Gona: An Kama Sojan Bogi Mai Muƙamin Manjo-Janar

June 12, 2026
Kotu Ta Ayyana Hausawa Da Fulani Halastattun ‘Yan Ƙasa A Jihar Filato
Babban Labari

Kotu Ta Ayyana Hausawa Da Fulani Halastattun ‘Yan Ƙasa A Jihar Filato

June 11, 2026
Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano
Babban Labari

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

May 13, 2026
Next Post
THE PUNCH EDITORIAL ON BENUE: A FABRICATION IN SEARCH OF A SCAPEGOAT

THE PUNCH EDITORIAL ON BENUE: A FABRICATION IN SEARCH OF A SCAPEGOAT

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
GODIYA

GODIYA

March 3, 2024
Youth: Build Peace Not Rancour – Hon. Rabi Salisu

Youth: Build Peace Not Rancour – Hon. Rabi Salisu

September 14, 2023
Allah Ji Ƙan Auwal Ɗanborno

Allah Ji Ƙan Auwal Ɗanborno

June 25, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Deepening Security Crisis: Buratai Calls for Emergency Measures
  • A Yayin Da Aka Kashe Janar Saura Wa Kuma Ya Rage?
  • Inna Lillahi… We Lost Gen. Rabe

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Deepening Security Crisis: Buratai Calls for Emergency Measures

Deepening Security Crisis: Buratai Calls for Emergency Measures

June 14, 2026
A Yayin Da Aka Kashe Janar Saura Wa Kuma Ya Rage?

A Yayin Da Aka Kashe Janar Saura Wa Kuma Ya Rage?

June 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.