Yau Ne Maulidin Likitar Ma’aurata
A yau Juma’a 10-01-1445, 28-07-2023 ce ranar da Hajiya #KoloDauraZuwairaKolo Dauda ta ƙara shekara ɗaya a shekaraunta.
Tun da sanyin safiya ta wallafa bayanan shukura a shafinta na Facebook. Tana cewa:
~~~~~~~
Cikin hukunci da ƙudura ta Buwayi gagara misali, a yau ya sake ƙaddara ƙaruwar shekara da raguwar ɗaya daga cikin kwanakin da Allah ya ƙaddaro min a rayuwata.
Alhamdu lillah, a tsawon kwanakin da na yi na samu nasarori da baki ya yi kaɗan wajen gode wa Allah subhanahu wata’ala, sai dai Allah shi ne shahidi shi ya san cikin zuciyar KOLO.
A cikin nasarorin da na samu ban rasa fuskantar ƙalubale da tarin ƙaddarorin da ba don ina da dakakkiyar zuciya ba, da wata rana sai yadda hali ya yi. Alhamdu lillah.
Da yawa suna min wani kallo na wadda ni ban san meye matsalata ba. Wasu sun ce ina tozarta mata duk da na san ɗan Adam ajizi ne, sai dai ina mai ba ku haƙurin ku ci gaba da haƙuri da ni, wata rana sai labari. Wanda zai ba da labarin ma wata rana babu.
Musamman ƙalubalen da na fi fuskanta, wanda wallahi da yawa nakan ci karo da saƙon inbox na wai me bazawara mara aure take da shi da za ta iya zuwa tana wayar da kan matan da ke cikin gidansu riƙe da masajensu, wai yaya aka yi masu iya biyayyar haka mazan suka yi waje da su?
Shi zawarci ƙaddara ne, akwai ƙaddarar ƙarewar zama wanda ke sa ma’aurata rabuwa. Akwai kuma ƙaddarar ajalin da ke zuwa ta yi wa masoya yankan ƙauna, wadda ita ta faɗa kaina, na rasa mijina abin alfaharina.
Ku yi haƙuri da duk rubuce-rubucena, wanda ya yarda da ni in na yi ya ɗauka. Wanda kuma bai yarda ba ya yi watsi da shi. Don Allah ku yi haƙuri, kwanakinmu na rayuwa ƙarewa suke.
Allah ya sa wa rayuwarmu albarka, ya ba wa jiharmu da ƙasarmu zaman lafiya mai ɗorewa. Tare da fatan mu cika da imani. Amin.
~~~~~~~
Muna taya ta murna tare da addu’ar Allah Ya ƙara lafiya da imani!~
~~~~~~













