ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (6)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Shin Ɗanfodiyo Taimakon Hausawa Ya Yi Ko Cutar Da Su?
A ci gaba da wannan muƙala, a yau za mu duba amsar wannan tambaya ta sama, cewa shin Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo (RTA), taimakon al’ummar Hausawa ya yi, ko kuwa cutar su ya yi?
Babban dalilin da ya sanya muka kawo wannan tambaya shi ne, saboda ganin yadda ‘ya’yan Ƙungiyar Hausawa Zalla ke ta faɗi tashin jirkita tarihi kuma suke ta haƙilon su a dole sai sun ɓata shi, sun lalata ɗimbin alheran da ya haifar wa al’ummomin da ke Afirka ta Yamma da ma duniya baki ɗaya.
Kodayake ba za mu yi mamaki ba, domin kuwa ƙudurinsu shi ne, su shuka fitina da gaba tsakanin al’ummar Arewa gaba ɗaya. Ba za su kuwa iya yin haka ba, sai sun lalata tarihi, sannan za su iya haifar da shakku a zukatan al’umma. Idan ba haka ba, yaushe a wannan ƙarni na 21, wani zai yi burin komawa gidan jahilci irin na kishin ƙabilanci?
Game da tambayarmu dangane da alheran Mujaddadi Ɗanfodiyo kuwa, kafin mu kai ga amsarmu, muna kira ga al’umma cewa, duk mai neman sahihin labari ko tarihinsa da ayyukansa na ƙwarai, to ya binciki tarihi sahihi daga littattafan tarihi na gaskiya.
Misali, akwai littafin Murry Last, mai taken “The Sokoto Caliphate,” wanda kamfanin wallafa na Humanities Press ya wallafa a shekarar 1967. Akwai kuma littafin da Paul E. Lovejoy ya rubuta, mai taken “Jihad in West Africa the Age of Revolutions,” wanda kamfanin Ohio University Press ya wallafa a shekarar 2016.
Haka kuma, ga duk mai neman gaskiya game da Mujaddadi, to ya nemi littafin “Usman Danfodio: The Great Mujaddid and Reformer,” wanda Ibrahim Sulaiman ya rubuta kuma kamfanin Hudahuda Publishing ya wallafa a shekarar 1987. Akwai kuma littafi mai taken “Shehu Usman Danfodio: His Life, Teachings and Influence,” wanda shi ma Ibrahim Sulaiman ya rubuta kuma kamfanin Islamic Publications Bureau ya wallafa.
Dukkan waɗannan littattafai suna ƙunshe da sahihan tarihin Mujaddadi Ɗanfodiyo da ayyukansa. Wani abin mamaki ma, wasu marubutan, kamar Paul E. Lovejoy, ba Musulmi ne ba; wanda haka ke nuna cewa abin da suka binciko na tarihi, gaskiya ne kuma sahihai.
A waɗannan littattafai da ma wasu irinsu masu tarin yawa da ba mu ambata ba a nan ba, sun nuna cewa babu shakka Sheikh Usman Ɗanfodiyo mutumin kirki ne, malamin addinin Musulunci ne na ƙwarai, wanda ya jaddada Musulunci kuma ya yaɗa koyarwarsa a Afrika ta Yamma. Mujaddadi ne da ya kafa daular Musulunci mai kyakkyawan tsari da adalci. Tsarin da hatta sai da Turawan Yamma suka kwaikwaya kuma suka amfana da shi.
Haka kuma shaida ta tabbatar da tsarkin zuciyar Ɗanfodiyo, dangane da jihadinsa, cewa don Allah ne da manzonsa ya gudanar da shi, ba don kwaɗayin mulki ko dukiya ba. Shehu ya ƙaddamar da jihadinsa a shekarar 1804, inda ya zuwa 1808, ya cinye manyan garuruwan Hausawa na Kano, Katsina, Zariya da sauransu, inda ya kafa hamshaƙiyar Daular Sakkwato bisa Shari’ar Musulunci.
Haka kuma, bayan wannan nasara, Shehu bai zama sarki a daular ba, domin kuwa ɗansa Muhammadu Bello da ɗan uwansa Abdullahin Gwandu ne ya naɗa, suka ci gaba da mulki a daular. Shi kuwa sai ya ci gaba da ayyukansa na karantarwa da ilimantarwa, har zuwa ƙarshen rayuwarsa, a shekarar 1817.
Jama’a masu bibiyar muƙalar nan da haƙuri, yau ma a nan za mu tsaya. Sai mun sake haɗuwa a kashi na 7, inda za mu zayyano wasu daga cikin muhimman taimako da gudunmowar da Mujaddadi Shehu Ɗanfodiyo ya ba al’ummar Hausawa, waɗanda har zuwa yau kuma har duniya ta ƙare, za su ci gaba da amfana da su.
Muna maraba da tsokaci ko ƙarin bayani ko tambaya a Comment Section.
_______________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago (online).












