• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, May 3, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

ZIYARA GA BUKAR USMAN: Ganawa Da Mutum Mai Karimci Da Tawali’u

Abdulhakim Dayyabu by Abdulhakim Dayyabu
October 19, 2023
in Gizago
0
Humility and Gentility: My Encounter with Dr. Bukar Usman

Daga hagu: Dr. Bukar Usman da Abdulhakim Dayyabu

43
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

ZIYARA GA BUKAR USMAN: Ganawa

Dokta Bukar Usman, OON

Da Mutum Mai Karimci Da Tawali’u

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026

Daga Abdulhakim Dayyabu

~~~~~~~
A ranar Asabar, 10 ga Oktoba, 2020, na samu kiran waya daga wani mutum mai kawo saƙo. Ya bugo mani waya, ya sanar da ni cewa an aiko mani da saƙo daga Abuja. Na yi musun cewa ba ni da wani saƙo saboda ban yi magana da kowa ba a ranar game da hakan. Saboda haka, na yanke shawarar ba zan je ba.

Jim kaɗan bayan kiran, sai na fara tunanin wane irin saƙo ne wannan kuma wane ne zai iya aiko da shi? Daga ƙarshe, na kira mutumin na tambaye shi abin da ke cikin saƙon. Sai ya sanar da ni cewa an rufe shi a cikin kwali amma yana zaton cewa ya ƙunshi littattafai ko takardu.

Da jin haka, sai na yanke shawarar tafiya ga ɗan saƙon. Da na je sai na iske manyan kwalaye guda biyu cike da littattafai tare da ambulan da ke ɗauke da wasiƙa da aka rubuto gare ni, a matsayin Shugaban Kamfanin AHD Clothing Emporium.

Maudu’in wasiƙar shi ne: “Gudunmawa.” Eh! Gidauniyar Dokta Bukar Usman ce ta ba da gudunmawar litattafai guda 71 tare da CD da jaridu ga kamfanina. Wasiƙar mai ɗauke da sa hannun shugaban gidauniyar, Dokta Bukar Usman, ta ƙunshi sunayen jerin littattafan da aka bayar da kuma adadin kwafin kowane.

Daga wurin karɓar wannan saƙon, sai na wuce kai tsaye zuwa ofishina, inda na buɗe waɗannan kwalaye cikin murna. Bayan wannan lokacin na murna da annashuwa, sai na aika da saƙon godiya ga Dokta Usman ta manhajar imel. Kuma tun daga wannan lokacin sai muka ci gaba da musayar wasiƙu ta imel, kiran waya da saƙonnin rubutu tare da shi (Dokta Usman ɗin).

Daga cikin littattafan da aka ba AHD Clothing, akwai littafin Dokta Usman mai taken: ‘Restructuring Nigeria: An Overview.’ Bayan karanta littafin, na samu marubucin a matsayin wanda na yi na’am da zurfin tunaninsa da fahimtarsa dangane da haɗin kai da zaman lafiya a Najeriya. Marubucin ya sadaukar da littafin ne ga … haɗin kan Tarayyar Najeriya, shugabanci na gari, tsaro da walwalar ‘yan Najeriya.

Bayan shekara biyu da wannan al’amari, na kammala aikin littafina mai taken ‘State of the Nation and Other Poems.’ Kuma ban yi tunanin wani ba face Dokta Usman domin ya rubuta ta’liƙin littafin nawa.

Na aika masa da wasiƙa ina neman cewa ya rubuta mani ta’aliƙin littafin a ranar 10 ga Agusta, 2022. A ranar 15 ga Agusta, 2022, na samu saƙon imel daga gare shi – wanda ke ɗauke da ta’aliƙin littafin.

A ranar 19 ga Agusta, na sake samun wani kira daga wani mai kawo saƙon, wanda ya sanar da ni cewa ina da wani saƙon da zan ɗauka. Da na je sai na samu kwafin littafin nawa da Dokta Usman ya sa aka buga, kuma ya yi gyaregyare masu matuƙar muhimmanci a ciki.

Samun mutum mai ƙima kamar Dokta Usman, a ce ya rubuta ta’liƙin littafina a cikin wannan ƙanƙanin lokaci, ya sa na samu karsashi da ƙwarin gwiwar ci gaba da al’amarin rubuce-rubuce ta fuskar adabi da nake a kai.

Bayan an yi nasarar wallafa littafin nawa da ƙaddamar da shi, sai na aika wa Dokta Usman kwafi ɗaya. Daga bisani ya kira ni ya taya ni murna sosai. Ya yi matuƙar farin ciki da jin cewa Farfesa Sani Abubakar Lugga, wanda shi ma ƙwararren marubuci ne a Najeriya, ya samu lokaci ya jagoranci ƙaddamar da littafin. Ya kuma buƙaci in miƙa gaisuwarsa gare shi idan muka haɗu a gaba – wanda na yi hakan.

Bayan saƙon taya murna, kuma Dokta Usman ya sayi ɗaruruwan kwafin littafin nawa da niyyar rabawa ga jama’a a sassa daban-daban na Najeriya.

Duk tsawon lokacin nan, ba mu taɓa tozali da juna ba kamar yadda Dokta Usman ya faɗa a ta’aliƙin littafin nawa: “Wataƙila ya zama dole in bayyana cewa Dayyabu yana zaune a Katsina, ni kuma [Usman] ina zaune a Abuja. Har yanzu ba mu yi ido huɗu da junanmu ba. Sanayyar mu a cikin shekaru biyun da suka gabata ta faru ne ta hanyar musayar saƙonni ta hanyar cibiyoyin sadarwa. Musayar saƙonni da shi [Dayyabu] ta kasance mai ban sha’awa sosai.”

Ban samu damar ganawa da Dokta Usman ba har sai da aka zaɓe ni don halartar taron ƙara wa juna sani game da Rubutun Littattafai, Gyarawa da Wallafawa, wanda Gidauniyar Daily Trust ta shirya tare da gudunmawar Gidauniyar MacArthur.

Lokacin da aka aiko da saƙon taron, an haɗa da kwafin jadawalin yadda zai gudana, gami da taƙaitaccen tarihin waɗanda za su gabatar da ƙasidu da maƙalu.

Da na ga muhimmancin abubuwan da ke ciki da kuma gogewar masu gabatarwar, sai na yanke shawarar yin tafiya daga Katsina zuwa Abuja, domin halartar wannan taro.

An gayyaci Dokta Usman don ya shugabanci tattaunawar da aka yi mai taken: “Harkar Wallafa Littattafai A Najeriya, Tsakanin Wallafa A Intanet Da Wallafa A Takarda: Wanne Ya Fi Tasiri Ta Fuskar Kasuwanci?”

Dokta Bukar ya ba da gudunmawa sosai yayin tattaunawar. Mahalarta taron sun yi mamaki matuƙa lokacin da suka fahimci cewa Dokta yana da shekara tamanin a duniya amma har yanzu yana da lafiya da kuzari.

Bayan an gama tattaunawar, sai na je na gaida Dokta Usman bayan sun sauko daga dandamalin tattaunawar. Sai na nemi in kai masa ziyara kafin in koma Katsina, inda ya yi na’am da hakan.

Don haka, ranar farko da na gana da Dokta Usman ita ce Litinin, 25 ga Satumba, 2023 a Merit House, Maitama, Abuja.

Yadda ganawar ta kasance kuwa ita ce, a ranar Alhamis, 28 ga Satumba, 2023, na kira Dokta Usman domin tsara ziyara ta gare shi, kamar yadda ya umarta a lokacin da muka fara haɗuwa. Na nemi haɗuwa da shi a ranar Asabar da yamma kuma ya amince da hakan.

A safiyar Asabar, 30 ga Satumba, 2023, ya aiko mani da adireshinsa ta saƙon wayar salula, tun ma kafin ni in kai ga tuna masa. Dubi yadda yake da kaifin ƙwaƙwalwa, duk da tsufansa – shekara 80 fa! A wannan lokacin, na lura da ɗabi’arsa ta farko: KAIFIN ƘWAƘWALWA!

Na hau motar haya, ta manhajar Bolt zuwa adireshin da ya turo mani kuma na isa cikin mintuna goma kafin lokacin haɗuwar mu.

Da isa ta, sai ga mai gadi ya fito, a inda na sanar da shi cewa ina da ganawa da Dokta Usman. Ya tambayi sunana, sannan ya shiga cikin gidan don ya sanar da mai karɓar baƙunci na.

Da misalin karfe 4:59 na yamma sai ga mai gadin ya dawo, ya yi mani nuni da cewa in shigo. Da shiga ta sai na hangi Dokta Usman a tsaye, yana jiran ya tarbe ni. Ya tarbe ni hannu bibbiyu, sannan ya shiga da ni cikin falonsa.

Wannan ya sa na ji ya girmama ni sosai. Bayan shiga falon nasa, sai ya yi mani ishara ga wata kujera kusa da kujerarsa, a inda na zauna. Nan-da-nan ya kashe akwatin talabijin da ke falon, domin mu gana.

Na biyu daga cikin kyawawan ɗabi’unsa, shi ne: GIRMAMA BAƘI!

Ya mayar da hankalinsa gaba ɗaya a gare ni, yayin da ni kuma na ɗauko littafin rubutuna, domin bin jadawalin da na tsara domin tattaunawa da shi.

Na fara da gode masa kan ɗimbin littattafan da ya ba kamfanina da kuma ta’aliƙin da ya rubuta wa littafina. Na kuma miƙa saƙon gaisuwa da godiya daga Cibiyar Karatu da ke Jihar Katsina mai suna “The Readers’ Hub” a gare shi. Daga nan sai na yi masa wasu tambayoyi musamman kan yadda ya koyi Hausa da yadda yake iya rubutawa da wallafa littattafai a cikin harshen, duk da cewa shi ɗan asalin ƙabilar Babur/Bura ne daga Jihar Borno.

Tattaunawarmu da shi ta kasance mai jan hankali da ƙayatarwa.

A karshen tattaunawar, Dokta Usman ya karɓi baƙuncin wasu dattawa guda biyu, waɗanda ‘yan garinsu ne suna daga ƙabilar Babur/Bura ne. Ya gabatar da ni gare su, ya kuma gabatar da su gare ni. Har ma ya zolaye ni da cewa za su iya sayar da ni da harshensu (Babur/Bura). Ni kuma na amsa da cewa ni (Bahaushe) duk na mamaye su, a inda duk muka yi dariya.

Mutanen biyu, ɗaya tsohon Kwamishina ne a Jihar Borno, Alhaji Mohammed Ibrahim Ɗanmasani da shugaban wata kungiyar kasuwanci ta ƙasa-da-ƙasa, Injiniya Ibrahim Usman. Sun je Abuja ne domin halarta bikin taya murna ga ɗaya daga cikin ‘yar uwarsu ‘yar asalin Jihar Borno, Dokta Salamatu Anas, wadda Shugaban Ƙasar Najeriyar ya naɗa ta a matsayin mai ba shi shawara ta musamman kan harkokin kiwon lafiya.

Duk da cewa yana zaune nesa da Jihar Borno, har yanzu Dokta Usman yana da kishin jiharsa ta haihuwa a zuciyarsa. Domin ya ƙarfafi gwiwar baƙinsa na Borno, waɗanda a yanzu su ne dattawan siyasar jihar da su bai wa wadda aka naɗa shawarar ta fara shirin kai wani gagarumin aiki a jihar tasu ta Borno, wanda zai sa a tuna da ita ko bayan barin ta wannan ofishi. Da haka, sai na lura da ɗabi’arsa ta uku: KISHIN ƘASA!

Ganin cewa Dokta Usman yana da wasu baƙi, kuma mun ƙare tattaunawarmu a kan abubuwan da ke cikin littafin rubutuna, sai na yi yunƙurin yin bankwana da shi, domin in tafi.

Da ya lura da haka, sai ya tambaye ni ko ina da direban da ke jira na a waje da zai ɗauke ni? Ni kuma na amsa masa da cewa direban motar haya na Bolt ne ya kawo ni kuma zan kira wani direban ya ɗauke ni, ta manhajar Bolt ɗin dai har-wa-yau.

Da jin haka sai ya ce in jira. Me zai faru bayan haka? Za ku sani ba da jimawa ba.

Ya yi bankwana da baƙinsa, yayin da ni kuma na jira shi a falon. Da ya dawo, sai ya zagaya da ni ɗakin nazarinsa kuma ya yi mini bayani game da yadda yake gudanar da lamuransa a ranakun aiki.

Ya sanar da ni cewa a halin yanzu ba ya rubutu a takarda da alƙalami. Ya ce yakan furta abin da yake so ya rubuta sai sakatarensa ya buga abin da ya furta a Kwamfuta. Bayan an gama rubutawa, sai a buga a takarda, sannan a gabatar masa, domin ya yi gyaregyare.

Bayan ɗakin nazarin, sai ya kai ni ɗakin ajiyarsa, a inda aka killace littattafansa, waɗanda adadinsu zai iya kai ɗaruruwa, ko ma dubbai.

A gefe ɗaya, na hango ‘yan tsirarun kwafin littafina, wanda hakan ya nuna mani cewa ya riga ya ba da wasu kwafin littafin da yawa. A falonsa da ɗakin nazarinsa da kuma ɗakin ajiyarsa, ya tambaye ni littattafansa da ba ni da su, a inda da ya ba ni su kyauta. Har ma ya ba ni wasu waɗanda ina da su tun tuni.

Duk yawan kwalayen da na gani, Dokta Usman ba zai taɓa sayar da ko da kwafi ɗaya na littattafansa ba – yana bayar da su ne kyauta. A wannan lokacin, na lura da ɗabi’arsa ta huɗu: KARIMCI DA KYAUTA.

Bayan ya gama zagayawa da ni, Dokta Usman ya bar ni cike da mamaki lokacin da ya yi mani nuni zuwa ga kujerar fasinja, yayin da shi kuma ya zauna a kujerar direba, cikin motarsa.

Shin wannan marubuci mai shekara 80 zai tuƙa mota ne? Tabbas – ba shakka! Ya tada motar, ya yi baya-baya, sannan ya fita daga cikin gidan da aka tsaftace a tsanake, yana mai ɗaga hannu ga masu gadin da suka buɗe masa ƙofa.

Duk da cewa gari ya fara yin duhu kuma ruwan sama ya fara safkowa, Dokta Usman ya tuƙa motar cikin gwaninta daga gidansa da ke Maitama zuwa Asokoro, a inda na sauka. Na lura da ɗabi’arsa ta biyar: ƘWAREWA A TUƘI.

Duk da cewa wasu direbobin suna ta danna ham cikin ɓacin rai da rashin haƙuri ga sauran direbobi, Dokta Usman ba ya cikin irinsu. Tun da na shiga motarsa, har na fita daga, bai danna ham ko sau ɗaya ba. Yana bin ƙa’idojin tuƙi sau-da-ƙafa. A kowace madakatar da ke da na’urar ba da hannu ga matuƙa, Dokta Usman yana tsayawa har sai ta haska koriyar kala kafin ya wuce, idan ba a wuri ɗaya ba na yankin A.Y.A; a inda na’urar ta yi kama da ta lalace. Daga wannan, sai na lura da ɗabi’arsa ta shida: BIYAYYA DA GIRMAMA DOKA.

Tafiyar mu zuwa Asokoro abar tunawa ce sosai. Dokta Usman ya nuna mani ma’aikatu da sauran wurare kamar Farmers’ Market (Kasuwar Manoma), Ofishin Jakadancin Libya, Ofishin Shugaban Ma’aikatan Tarayya, Titin Filin Jirgin Sama da Ginin ECOWAS. Ya kuma kai ni wani wurin da ke gundumar Wuse, inda ya taɓa sasanta wani rikici da ya ɓarke tsakanin wasu matasa guda biyu, wanda na karanta a muƙalarsa ta kwanakin baya, wadda ya yi nazari da tsokaci game da Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja. Ya kuma nuna mani tsohon ofishinsa da hanyar zuwa tsohon gidansa da ke Unguwar Asokoro, lokacin da ya yi aiki a Fadar Shugaban Ƙasa, a Ofishin Ayyuka na Musamman, a matsayinsa na Babban Sakatare.

Dokta Usman, kasancewarsa ɗaya daga cikin manyan ma’aikatan gwamnati da suka tashi daga Legas zuwa Abuja, da alama duk taswirar birnin tana a kansa. Ya san kusan ko’ina a cikin Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Ba wai kawai ya san wuraren ba, har ma ya san abin da aka tsara za a yi da wuraren a daftarin farko na birnin. Misali, ya nuna mani wasu wuraren da ake shagulgula, inda ya ce da farko an tsara cewa za su zama lambuna ne ba wuraren kasuwanci ba.

Tafiyar mu mai ban sha’awa ta ƙare lokacin da muka isa rukunin gidajen da na kwatanta masa a Asokoro. Da isar mu sai ya tsaya a bakin ƙofar shiga rukunin, yayin da ni kuma na yi masa godiya ƙwarai da gaske, da ya sanya zuwa na Abuja ya zama abin tunawa.

Gaskiyar magana, wannan tafiya ta sa na ji cewa Dokta Usman ya girmama ni sosai. Hakan kuma ya ƙara mani karsashi da ƙwarin gwiwa.

Kafin in fito daga motar, sai ya zura hannayensa a aljihu ya fiddo takardun Nairori masu yawa. Sai ya zolaye ni da cewa, “bari mu raba kuɗin,” a inda ya ɗebi kusan rabin su ya hannanta mani, ba tare da ya ƙirga ba. A nan ne ɗabi’arsa ta huɗu ta sake bayyana: KARIMCI DA KYAUTA.

A ƙarshe, na ƙara yi masa godiya sosai, a inda shi kuma ya yi mani fatan dawowa gida Katsina cikin ƙoshin lafiya.

~~~~~~~
Wannan muƙala da Abdulhakim Dayyabu ya rubuta, Dokta Bukar Usman ya same ta ta manhajar imel ne a ranar 4 ga Oktoba, 2023. Dayyabu, wanda ke zaune a Katsina, Jihar Katsina, ɗan kasuwa ne, marubuci, jakadan adabi kuma ɗalibin ilimi. Shi ne kuma wanda ya kafa kamfanin AHD Clothing da AHD Consulting. Za a iya samun sa ta adireshinsa na imel, ahdclothingemporium@gmail.com, ahdconsulting360@gmail.com da abdulhakeemdt@gmail.com
~~~~~~~

Previous Post

The Bloomsbury Handbook of Muslims and Popular Culture: An Endorsement

Next Post

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sababbin Shugabannin Hukumomin Yaɗa Labarai

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
Za Mu Inganta Rayuwa Da Ayyukan ‘Yan Jarida – Minista Idris

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Sababbin Shugabannin Hukumomin Yaɗa Labarai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

The Bloomsbury Handbook of Muslims and Popular Culture: An Endorsement

The Bloomsbury Handbook of Muslims and Popular Culture: An Endorsement

October 19, 2023
Minista Hannatu Musawa Ta Ƙudiri Aniyar Kafa Gidan Tarihi Da Na Wasanni Na Ƙasa A Abuja

Minista Hannatu Musawa Ta Ƙudiri Aniyar Kafa Gidan Tarihi Da Na Wasanni Na Ƙasa A Abuja

December 16, 2023
Janar Faruk Yahaya Ya Zama Zaruman Sakkwato

Janar Faruk Yahaya Ya Zama Zaruman Sakkwato

August 15, 2023
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (6)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (6)

January 6, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)
  • General Buratai (A Poem)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

Dokta Bukar Usman Ya Wallafa Sabbin Littattafai 6 A Bana

April 28, 2026
Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (11)

April 27, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.