ZAKARAN ADABI
BANKWANA NGUGI

__________
Wannan waƙe mai taken ZAKARAN ADABI, fasihin sha’iri, Malam Usman Nagado II ne ya rubuta shi a matsayin ta’aziyya ga fitaccen marubucin Afirka, Ngugi wa Thiong’o, wanda ya rasu a Larabar da ta gabata. Daga bisani kuma Bashir Yahuza Malumfashi ya biyo da ta’aliƙi da ya yi wa taken BANKWANA NGUGI. Ga jerin baitocin:
__________
Af! da ƙiftawar agogo,
Ta saɓaɓo ta bi bango.
Salalaf salalaf ta sanɗo,
Babu tsiwa ba cacago.
Tai saɗafɗaf ta fa dirgo,
Ta fa hauro kai ya basgo.
Zakaran Adabi ta sure,
Ngugi wa Thiong’o.
A’aha mun samu giɓi,
Lahira yau ta yi ango.
Dauri ko shago a harshe,
Adabi daɗi ya cango.
Tsaf ya mai taza da tsifa,
Sai ka ce an sa asago.
Wuyar Adabi kamar yin,
Atuni ne ko anago.
Adabi ya samu gata,
Gunsa yai tsoka da ɓargo.
Ya taho da ya fa miƙo,
Yanzu ko ya yada zango.
A Afirka ƙwarai uba ne,
Kai a kishi shi na hango.
Shi ya ce mu riƙe fa namu,
Harsunan mu kawar buɗago.
Harshe na uwa da baba,
Har su Yakumbo da Gwaggo.
Yai rubutu can a Kenya,
Sai ka ji shi kamar Ungoggo.
Ya karaɗe Afirka malam,
Ko’ina kai har su Rogo.
Kai ina-ma yai wafati,
Kan tafarkin Ɗaha bargo.
Kai ina-ma dai ina-ma,
Yai ma kansa gyaɗa ta Dogo.
To Adibai hattararku,
Sai ku lalleƙa ku hango.
Kun ga gemun ɗan uwanku,
Ku tsare naku ku fargo.
In ta zo ba ta tsimayi,
Ko a ɗaki ko a argo.
Za ta zazzaga ta zago,
Za ta zo tamfal gizago.
Ko’ina ka fake ta bi ka,
Ta bice rai ta fa tsigo.
Ko cikin ruwa za ta kutso,
Ko fa ka yi lamo a kargo.
Sai ta ɗauki uwa da jego,
Ba ruwanta da wane gago.
Har da jariri da tsoho,
Majiyin ƙarfi samargo.
Ƴan uwa mu yawaita hairi,
Tun gabanin dai ta zago.
Usman Nagado ya shiryo,
Ga jawabi nawa ungo.
(m) USMAN NAGADO (II)
29 ga Mayu, 2025.
__________
BANKWANA NGUGI
•••••
Madalla da baitukanka,
Ni ma zan ɗaura ɗango.
Ko baitoci za ni jero?
Bari in zo in ƙago.
Shi Ngugi ya fa milla,
Ka ji ɗa shi wa Thiong’o
Shi adibi ne na gaske,
Tun daɗewa ni na hango.
Jarumi ne babu shakka,
Ya daddasa icce na kargo.
Ya yi yaƙi don Afirka,
Rigar Bature shi ya tsargo.
Baibai baibai katibinmu,
Muna nan tafe wa Thiong’o.
Ni ne nai yo ta’aliƙi,
Bashiru Yahuza mai Gizago.
_____________
© Bashir Yahuza Malumfashi
Juma’a 03-12-1446 (Hijiriyya)
30-05-2025 (Miladiyya)
_____________












