• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, January 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

HARKAR TSARO A JIHAR KATSINA: Ƙarin Haske Kan Ƙudurorin Gwamna Raɗɗa

Daga Maiwada Dammallam by Daga Maiwada Dammallam
February 12, 2024
in Babban Labari
0
HARKAR TSARO A JIHAR KATSINA: Ƙarin Haske Kan Ƙudurorin Gwamna Raɗɗa

Gwamnan Jihar, Malam Dikko Umar Raɗɗa

24
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

HARKAR TSARO A JIHAR KATSINA:
Ƙarin Haske Kan Ƙudurorin Gwamna Raɗɗa

Daga Maiwada Dammallam

Related posts

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

January 14, 2026
Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

January 4, 2026

A ranar Juma’a da ta gabata (9/2/24), Mai girma Gwamna, Dr. Dikko Umar Raɗɗa ya jagoranci wani taro na masu ruwa da tsaki a harkar tsaro a Jihar Katsina.
Taron wanda ya samu halarcin masu martaba Sarkin Katsina da Sarkin Daura da kuma Hakimai da ’yan kasuwa masu faɗa a ji, an gudanar da shi ne domin tuntuɓa kan matsaloli biyu masu dogaro da juna — matsalar saro da hauhawar tsadar rayuwa da a yau suka addabi kowa.

To, kamar yadda aka sani, matsalar tsaro ba matsala ba ce da ake bajewa a faifai a tattauna ba. Kan haka, Gwamna Raɗɗa ya yi jawabin buɗe taro daidai da yadda ya dace da wannan yanayin, sannan aka sallami ‘yan jarida; aka rufe ƙofa don tattaunawa ta sirri. Kan haka, ni ma zan taƙaita tambihina kan jawabin Gwamna na buɗe taro.

Da farko, zan fara yin gyara kan rahotannin wasu jaridu da na ga suna cewa “Gwamna ya ce al’umma su tsare kansu,” abin da wasu suka fahimta a karkace; suke ɗauka gwamnati ta fidda hannunta ne daga nauyin ba al’umma tsaro. Ko kusa ba abin da Gwamna Raɗɗa ke nufi ba ke nan.

Gwamna shawara dai ya ba da kan cewa mutane su kara himma wajen ganin sun yi tsare-tsare da za su taimaka masu wajen tsare kansu bisa kan abin da gwamnati ke iya yi.

Gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa bai tsaya a nan ba. Ya ƙara jaddada ƙudirin gwamnati na taimaka wa duk waɗanda suka fito da tsari na tsaron kai don samun nasarar abin. Ya kuma ƙara jaddada ƙudirin gwamnati na jajircewa kan kawo ƙarshen matsalar tsaro, duk da barazanar da gwamnati ke fuskanta daga gamayyar dabobin ‘yan ta’adda, waɗanda a bayyane yake cewa sun harzuƙa da nasarorin da Gwamnatin Jihar Katsina ke samu wajen kawo ƙarshen ta’addaci da rashin zaman lafiya.

Tabbas, wannan harzuƙar ita ta sa wannan gamayyar ‘yan ta’addan suka ɗauki ƙudirin shan-giyar-kusu, suke ƙulle-kullen yadda za su kai wa Mai girma Gwamna hari, yadda bayanan sirri na jami’an tsaro suka tabbatar kamar yadda Gwamna ya bayyana wa mahalarta taron.

Haƙiƙa, shawarar da Gwamna ya ba da, kan al’umma su jajirce wajen inganta tsare-tsare na sa-kai na tsaro, shawara ce mai inganci. Duk duniya babu gwamnati mai iya wanzar da tsaro ɗari-bisa-ɗari komai kuɗinta ko ƙarfin sojanta.

Harkar tsaro, harka ce mai tsada da sarƙaƙiya. Akan haka, gwamnatoci abin da suke yi shi ne, kawo tsare-tsare masu inganci na yadda za a iya samun tsaro mai inganci da kuma ba da tallafi inda ya dace. Ita kuma ke da hurumin ɗaukar mataki na karfin tuwo, inda abin ya wuce ƙima.

Al’ummar Jihar Katsina, a zauren taron neman mafita

Ke nan, yana da kyau al’umma su kalli shawarar Mai girma Gwamna Raɗɗa daga mahanga ta ƙarfi ba ta tsoro ba kuma ta hankali ba ta gazawa ba. Shawara ce ta a gudu tare, a tsira tare. Wannan shawara ta yi daidai da irin tallafin da gwamnati ta ba da akan tsaro na assasa jami’an sa-kai na (Community Watch Corps – CWC)” waɗanda suka taimaka sosai wajen rage matsalar tsaro a Jihar Katsina da fiye da kashi 80 bisa 100, cikin watanni 6 ko 7.

Haka zalika, duk yana daga cikin wannan ƙoƙarin na ba da tallafi, ware zunzurutun kuɗi fiye da Naira miliyan dubu bakwai (N7bn) da Gwamna ya yi don sayen kayan aiki ga jami’an tsaro don inganta ƙoƙarinsu.

Wannan abu ne da bai taɓa faruwa a Jihar Katsina koma ƙila a yankin Arewa baki ɗaya ba. Za a fi fahimtar wannan ƙoƙarin idan aka kalli cewa kundin tsarin mulki ya keɓance tsaro, ya ba da alhakin samarwa da tabbatar da shi ga Gwamnatin Tarayya.

Ke nan, yana da kyau mutane su fahimci cewa gwamnati na nan cikin harkar tsaro tsundum kuma ba za ta yi ƙasa a gwiwa wajen ƙoƙarin kawo ƙarshen matsalar tsaro ba.

A ɓangaren al’umma, sai a ci gaba da taya ta da addu’a da kuma ba ta goyon baya, har Allah Ya kawo mana ƙarshen fitinar.

A ɗayan hannun, Gwamna ya ja hankalin al’umma kan matsalar tsadar rayuwa, inda kamar kullum, ya tausaya tare da nuni da irin maƙarƙashiyar da wasu baragurbi daga cikin al’umma suke yi, wanda ke ƙara jefa al’umma cikin masifar tsadar rayuwa. Ya koka kan ‘yan kasuwa da suke kwashe abincin suna haurawa da shi ƙasashen ƙetare, inda ya fi tsada, don cin ƙazamar riba, ba tare da kallon halin ƙunci da tausayi da yin hakan ke iya jefa al’ummar gida Katsina da ma sauran al’ummar Najeriya baki ɗaya ba.

Wannan maƙarƙashiyar ba ta tsaya kan kayan abinci kawai ba. Ta haɗa da duk wani nau’in abin buƙatun al’umma, kamar su man fetur da sauransu. A ɗayan hannun kuma, duk yana daga cikin tsarin masu wannan halayyar, shigowa da muggan makamai da ake aikata ɓarna da su, inda a yau bindiga ƙirar AK-47 ta koma kamar sandar rake cikin ƙauyukanmu. Haka kuma, da yawa su ne masu shigo da miyagun ƙwayoyi da a wani ɓangare, ‘yan ta’adda ke amfani da don su gusar da hankali, su samu damar aikata abin da mai hankali bai iya yi.

Daɗin daɗawa kuma, su ne suka cika garuruwanmu da miyagun ƙwayoyi, waɗanda suke kan gaba wajen taɓarɓarewar rayuwar matasa tare da yin dabaibayi ga duk wani ƙoƙari na gwamnati na inganta rayuwarsu. Kai yau matsalar miyagun ƙwayoyi har cikin ‘yan mata, matan aure da dattawa.

Haƙiƙa, wannan abin Allah wadarai ne kuma manuniya ce ta cewa har yanzu ba mu gama fahimtar cewa da gwamnati da al’umma kamar hanta da jini ne ba, kowane na dogara da ɗayan don samu nasarar tafiyar.

Ke nan, idan gwamnati ba ta samun cikakken haɗin kan al’umma, samun nasarar tsare al’umma tare da sama masu rayuwa mai sauƙi zai zama abu mai wahalar gaske.

Ta wannan mahangar ce Mai girma Gwamna Raɗɗa ya zaburar da al’umma kan su kare kansu, ta hanyar haɗaka da gwamnati wajen musanyar bayanai da kuma kama-kama, inda buƙatar haka ta wajaba.

Dole fa al’umma su yarda cewa sai da haɗin kanmu gwamnati za ta iya aiwatar da ƙudurorinta, waɗanda za su taimaka kowa ya samu sauƙin rayuwa da walwala.

Yana da muhimmanci mu fahimci cewa babu gwamnatin da ke iya wadatar da kowa. Kamar yadda na faɗa a baya, amfanin gwamnati shi ne tabbatar da tsari na adalci, wanda ya yi daidai da kowa, wanda kuma zai samar da yanayi na walwala ga ‘yan ƙasa, yadda kowa zai iya ci da sha ba tare da ya jikkata ko mutuncinsa ya raunana ba.

Ingantataccen tunani zai tabbatar wa al’umma cewa ‘yan kuɗaɗen da suke shigo wa gwamnati, ba su taka kara sun karya ba, idan aka kalli nauyin ɗimbin al’ummar da ke rataye a wuyanta. Amma duk da haka za ka samu wasu marasa tausayi sun kwashe abincin da yakamata a ce an bar wa ’yan ƙasa suna saye cikin sauƙi, su fidda shi waje don ƙazamar riba kuma su dawo su saje da sauran al’umma suna kukan yunwa tare da ganin gazawar gwamnati wajen wadata al’umma da abinci.

Babu ƙasar da ta taɓa ci gaba da irin wannan halayyar kuma ina da tabbacin Najeriya ba za ta zama ta farko ba.

To nan ma aikin gayya ne. Ya wajaba mu sa ido don zaƙulo ɓata garin da a kodayaushe so suke su yi amfani da gazawar yanayi don su gallaza wa al’umma don mu miƙa wa gwamnati su, don ta ɗauki mataki. Da ma ɗaya daga cikin manyan dalilai na samar da gwamnati, shi ne ɗaukar mataki kan duk wani kangararre da bai yarda da tsarin raba-daidai da a-gudu-tare-a-tsira-tare ba.

Alhamdu lillah, zuwa yanzu kowa ya gamsu da kyawawan manufofin Mai girma Gwamna Dikko Umar Raɗɗa, kuma kowa zai iya yarda cewa sama wa talaka walwala da sauƙin rayuwa, su ne kan gaba a jerin manufofina.

To ba nan gizo ke saƙar ba. Samun shugaba mai tausayin al’umma da kuma zimmar sama masu mafita, rabi ne daga cikin aikin saita lamurran al’umma a ko’ina a faɗin duniya. Sauran rabin, haɗin kan jimallar al’umma ke samar da shi. Ban tababar cewa idan har muka na ce kan cewa nauyin saita lamurran al’umma gaba ɗaya ya dogara kan gwamnati ne, to kam kullum zamu zauna cikin wahala da baƙin ciki.

Jama’a, a sa ido. Duk inda aka ga abin da bai daidai da hankali ba, to a yi ƙoƙarin gyarawa. Idan abin ya ci tura, a sanar da gwamnati ta ɗauki matakin da ya dace.

Ina roƙon Allah (SWT) Ya kawo mana sauƙin rayuwa, walwala da yanayi mai albarka. Ina kuma roƙon Allah, duk tsageran da bai yarda da al’umma ta zauna lafiya cikin sauƙi da walwala ba, Allah Ya yi mana maganinsa.

~~~~~~~
Malam Maiwada, shi ne Babban Mataimaki Na Musamman Ga Gwamnan Jihar Katsina A Harkar Watsa Labarai.
~~~~~~~

Previous Post

ADADIN KUƊIN DA NAJERIYA ZA TA SAMU IDAN TA CI KOFI A YAU

Next Post

Tribute to Cultural Broadcaster: Muhammad Salissou Hamissou

Related Posts

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna
Babban Labari

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

January 14, 2026
Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin
Babban Labari

Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

January 4, 2026
Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci
Babban Labari

Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci

January 3, 2026
Next Post
Tribute to Cultural Broadcaster: Muhammad Salissou Hamissou

Tribute to Cultural Broadcaster: Muhammad Salissou Hamissou

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Taron editoci: Tinubu na so a riƙa yaɗa kyawawan labarai don jawo zuba jari a Nijeriya

Taron editoci: Tinubu na so a riƙa yaɗa kyawawan labarai don jawo zuba jari a Nijeriya

November 16, 2023
Shin Wai Akwai So? (1)

Shin Wai Akwai So? (1)

June 5, 2025
An Samar Da Maslaha A Takaddamar Sheikh Idris Da Gwamnatin Bauchi

An Samar Da Maslaha A Takaddamar Sheikh Idris Da Gwamnatin Bauchi

July 29, 2023
BATUN WATAN SALLAH A NAJERIYA

BATUN WATAN SALLAH A NAJERIYA

April 8, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)
  • Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
  • Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.