Batun Tsaro A Malam Madori: Jan Hankali Ga Hukumomi Da Al’umma
Daga Okashat Musa Ado
~~~~~~~
Ina mai amfani da wannan dama wajen jajanta wa ɗaukacin al’ummar wannan gari na Malam Madori, bisa wannan mummunan ibtila’in da ya same mu kwana uku da suka wuce. Ubangiji Allah Ya kiyaye afkuwar haka nan gaba. Shi kuma wanda Allah Ya ƙarbi rayuwarsa, muna masa addu’ar neman gafarar Allah gare shi, kana daga bisani muna masu miƙa ta’aziyya ga ‘yan uwansa. Allah ba su ikon cinye wannan jarabawa.
Mai karatu zai matsu ya ji abin da zan ce dangane da ambatar gyara kayanka cikin rubutuna. In za mu iya tunawa, cikin wannan gari namu, an yi garkuwa da mutane ya fi gaban a ƙirga, ‘yan fashi kuwa sun maida garin tamkar wani dandali na zuwan su koyaushe. Ko a kwanaki ‘yan fashi sun shigo wannan gari, inda suka gudanar da fashi, sannan suka halaka yara biyu, gami da jikkata mahaifiyarau, inda yanzu haka take kwance a asibiti.
Tabbas babu abin da za mu ce ga Allah sai godiya, gami da addu’o’i ga mahukunta wannan gari, ganin yadda suka tashi tsaye, ba dare ba rana wajen ganin an samu tsaro cikin wannan gari namu. Sannan muna ƙara yaba wa jami’an tsaro bisa irin jarircewa da suke nunawa wajen kare wannan gari namu. Kai tsaye za mu iya cewa an fara samun ci gaba ta ɓangaren tsaro a wannan gari, sannan muna musu addu’oi gami da ƙara ba su ƙwarin gwiwa wajen aiwatar da abubuwan alheri da suke wajen ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali cikin wannan gari namu mai tarin albarka.
Sai dai kamar ana tufƙa ne ta baya na warwarewa, idan muka yi duba da wannan gari namu, dangane da wasu abubuwa da ke faruwa, ta ɓangaren yadda ake gudanar tsarin kunna fitilun kan titunan wannan gari – yau ka ga can akwai gobe ka ga nan babu, alhali fitilun sukan taimaka sosai wajen samar da tsaro a wannan gari namu. Ga shi yau kusan kwanaki biyar, wasu layuka da wannan hasken ba ya kai wa, ciki kuwa har da layin da wannan mummunan abun ya faru.
Kai tsaye ban danganta faruwar wannan ibtila’in da rashin kunna fitilun kan titi na yankin ba, amman tabbas da Allah ya sa akwai cikakken haske a layin, daidai lokacin da wannan mummunan abun yake faruwa, haƙiƙa za a samu gudunmawa daga mutanen da ke kewaye da wannan yankin, ciki kuwa har da ni, domin daga inda abun ya faru zuwa inda nake, bai fi nisan mita 200 ba.
Hasalima, wajen da wannan abun ya faru, yara ne ke gudanar da ƙwallo daga ƙarfe 9 zuwa 10 na dare, kasantuwar yadda haske ya raba layin biyu, wani ya yi kudu zuwa arewa, wani ya yi gabas zuwa yamma. Tabbas da a wannan lokacin ma ya kasance a kunne kamar kowanne lokaci, ko shakka babu da za a iya samun tsaro na musamman; ta yadda hasken da ke wajen ba zai bai wa yaron dama har ya iya zaro wani abu mai kama da makami a jikinsa ba, wajen yin sanadiyyar mutuwar abokin karawar tasa wajen budurwar ba.
Domin kuwa koda shi marigayin ganin ya fidda wannan makamin, zai iya guduwa, ko kuma ya yi ƙoƙarin kare kansa ko kuma mutanen da ke kusa da wajen su kawo ɗauki cikin gaugawa. Amma hatta yaran da ke wasa kusa da wajen ba su ma san da wani abu mai kama da makami aka yi amfani ba, har sai da wanda Allah ya yi wa rasuwar ya je ƙasa, sannan daga bisani suka haska suka gan shi jina-jina cikin jini, sannan suka iya yin ihu. Daga bisani al’umma suka kawo ɗauki, aka ɗauke yaron zuwa asibiti, shi kuma wanda ya yi wannan mummunan aikin, aka bi shi har aka yi nasarar kama shi.
Daga ƙarshe muna musu kira ga hukumomin gami da manyan ƙungiyoyi da muke da su, wajen bibiyar wannan lamarin, domin ganin an gudanar da adalci cikin wannan lamari. Sai dai akwai abubuwan da ya kamata a ce an ƙara ƙaimi kansu, kamar haka:
√Tabbatar da adalci ga wanda aka zalunta, ta yadda nan gaba babu wani wanda zai ƙara koda sha’awar aiwatar da kwatankwacin irin wannan laifi.
√Ƙara samar da kayan aiki ga jami’an tsaro, kamar sabbin motoci da babura, gami da samar musu da isasshen man gudanarwa
√Ƙara sanya ido wajen shige da fice na wata baƙuwar fuskar da ba a saba gani ba cikin unguwa ba.
√Kula gami da sanya idanu wajen ganin ana kunna waɗannan fitilu na titi kan lokaci.
Allah Ya ƙara tabbatar mana da tsaro cikin wannan gari na Malam Madori.
~~~~~~~
Malam Okashat Musa Ado, ya rubuto taokacin nan daga Malam Madori, Jihar Jigawa
~~~~~~~













