• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

BABBAN LABARI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
January 4, 2026
in Babban Labari
0
Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

Zannan Galadiman Katsina, Dr. Tukur Hassan Tingilin

23
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
Zannan Galadiman Katsina, Dr. Tukur Hassan Tingilin


                        __________
Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Katsina kuma Shugaban Gidauniyar Zanna-Wali, Injiniya Tukur Hassan Tingilin ya bayyana cewa kishin ilimi da buƙatar ganin ilimi ya bunƙasa a yankunan Malumfashi da Ƙafur, shi ya sanya ya ɗauki nauyin bayar da tallafin karatu ga ɗaliban yankunan, su 110 da suka samu gurbin karatu a sabuwar babbar makarantar College of Agriculture and Technology ta Nabanje, Ƙaramar Hukumar Ƙafur, Jihar Katsina.

Dokta Tingilin, wanda shi ne Zannan Galadiman Katsina, Cigarin Danejin Katsina kuma Walin Ƙafur, ya bayyana cewa, kasancewar wannan makaranta ita ce ta farko mai girma a wannan yanki, ya zama wajibi ya nuna goyon baya ga mai girma Mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Masari bisa ƙoƙarinsa na kawo ci cigaba a wannan yanki ta fuskar ilimi.

“Na daɗe ina kwaɗayin ganin yankinmu ya samu babbar makaranta, domin ilmantar da ɗinbin matasanmu maza da mata. Sai ga shi a ƙarƙashin mulkin Jam’iyyarmu ta APC, Allah ya ba mu shugabannin da ke kishinmu, suka kawo mana wannan makaranta. Don haka wajibi ne mu haɗa hannu domin taimaka wa al’ummarmu,” inji Injiniya Tingilin.

Ya ƙara da cewa: “Muna godiya ga mai girma Shugaban Ƙasa, Alhaji Bola Ahmed Tinubu da Mai ba shi shawara ta fuskar Siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari da kuma Mai girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa bisa ƙoƙarinsu na yi wa al’ummamu hidima a kowane lokaci.”

Da yake ƙarin bayani game da yadda wannan tallafin karatu zai kasance, Sakataren Giidauniyar Zanna-Wali, Malam Hassan Mukhtar Malumfashi ya ce, a kowacce Mazaɓar Kansila da ke ƙananan hukumomin Malumfashi da Ƙafur, su 22 za a zaɓi ɗalibai biyar-biyar. Wannan zai samar da jimillar ɗalibai 110 ke nan, waɗanda za su ci gajiyar wannan tallafi.

“Kuma dole sai ɗalibi yana da sakamakon jarabawar JAMB ta 2025 mai kyau, wadda za ta ba shi damar samun wannan tallafi na karatu, ƙarƙashin wannan gidauniya mai albarka,” a cewar Sakatare Hassan.

Ya ƙarƙare da cewa: “Kuma wannan karatu na National Diploma ne (ND), tsawon shekara biyu. Domin samun form na wannan tallafi ana iya tuntuɓar wakilan wannan gidauniya a yankin Malumfashi da Kafur, domin ƙarin bayani”
_______________

Previous Post

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (5)

Next Post

Hausa/Fulani: Together Forever

Related Posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Babban Labari

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume
Babban Labari

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel
Babban Labari

Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel

April 2, 2026
Next Post
Hausa/Fulani: Together Forever

Hausa/Fulani: Together Forever

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Jan Hankali Ga Shugabanni

Jan Hankali Ga Shugabanni

December 9, 2025
Littafin TAYA NI MU GYARA A Da’irar Nazari Da Sharhi

Littafin TAYA NI MU GYARA A Da’irar Nazari Da Sharhi

January 17, 2024
Gargaɗin Amurka kan Nijeriya na tada hankulan jama’a, kuma ya na yin illa ga tattalin arzikin ƙasa – Minista

‘Yan Nijeriya za su fara bin diddigin ayyukan da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa – Minista

November 8, 2023
TSOKACINMU NA YAU (05)

TSOKACINMU NA YAU (05)

March 5, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.