BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (4)
Bashir Yahuza Malumfashi
Ziyarar Fadar Sarkin Biu:
Sarautar gargajiya na daya daga cikin al’amura masu matuƙar muhimmanci a kusan kowace al’umma kuma tsari ne da ke samar da shugabanci bisa al’ada, addini da zamantakewar al’umma tun zamunna masu yawa da suka shige, har zuwa wannan zamani da ake gudanar da tsarin dimokuraɗiyya, wanda ya samo asali daga Turawan Mulkin Mallaka. Don haka Birnin Biu, a matsayinsa na daɗaɗɗen gari mai daɗaɗɗen tarihi, yana da babbar masarauta da babban sarki mai wuƙar yanka ta ajin farko. Tsarin sarauta ya samo asali a Biu tun daga shekarar 1535, wato zamanin sarkin Biu na farko Yamtarawala kamar yadda Dokta Bukar Usman ya tabbatar a littafinsa na Tarihin Biu. Tun farko ana kiran ‘Shugaba’ ko ‘Sarki’ a Masarautar Biu da laƙanin ‘Kuthli’ a gargajiyance. Aka zo ana kiran shi da ‘Mai’ (tsarin Kanuri ke nan), ko ‘Amir’ (kalmar Larabci da ke nufin Shugaba). Mai Ari Dogo, Sarkin Biu na 24, shi aka fara kira da laƙanin ‘Emir’ (Sarki) da kuma Lardin Biu da laƙanin ‘Emirate’ (Masarauta) a shekarar 1920. A shekarar 1935, sai Turawan Mulkin Mallaka suka zartar da cewa daga lokacin, a riƙa kiran shi da laƙanin ‘Mai.’ Wannan shi ne dalilin da ya sanya ake amfani da laƙanin ‘Kuthli’ ko ‘Sarki’ ko ‘Mai’ ko ‘Emir’ a Masarautar Biu.
A ranar Juma’a, 27-10-2023, daidai misalin ƙarfe 9:30 na safe, na ziyarci fadar Mai Martaba Sarkin Biu, Mai Mustapha Umar Mustapha II. Babban maƙasudin ziyarar shi ne, in shaida naɗin sarautu uku – Betaran Biu da Zannan Biu da kuma Shettiman Biu. Dukkan sarautun uku, manya ne, waɗanda kuma aka naɗa fitattu ne, jajirtattu, da suka shahara wajen yi wa al’ummar Masarautar Biu hidima.

Mutanen uku da aka naɗa sarautu daban-daban su ne, Betaran Biu, tsohon Hafsan-Hafsoshin Rundunar Sojojin Najeriya, Laftanar-Janar (mai ritaya) Tukur Yusufu Buratai, CFR, wanda kuma shi ne tsohon Jakadan Najeriya a Jamhuriyyar Benin. Sarautar Betara babba ce a Masarautar Biu, domin kuwa mai muƙamin yana ɗaya daga cikin masu zaɓen Sarki a lokacin da buƙatar haka ta taso. Haka kuma yana iya wakiltar sarkin a faɗin duniya, a duk lokacin da shi sarkin ya amince masa.
Sarauta ta biyu da aka naɗa, ita ce ta Shettiman Biu kuma Riya-Adimiral (mai ritaya), Dokta Abdul Adamu Biu, OFR aka naɗa. Sarauta ce mai girma da muhimmanci a Masarautar Biu kuma wasu daga cikin ayyukansa sun haɗa da kula da zaɓen Dagatai idan buƙatar haka ta taso. Haka kuma yana da ruwa da tsaki wajen tantance inda za a gina masallacin Juma’a da zaɓen Liman, kafin gabatar da rahotonsa ga sarki domin amincewa da sanya albarka da kuma naɗawa.
Sarauta ta uku da aka naɗa a wannan rana ta Jumu’a, ita ce ta Zannan Biu. Kuma wanda aka naɗa shi ma tsohon babban jami’in soja ne, wato Birgediya-Janar (mai ritaya) Abdullahi Dadan-Garba. Ita ma Sarautar Zannah tana da girma da muhimmanci a Masarautar Biu, domin kuwa aikin Zannah ne ya zama mai sasanta rikice-rikice da suka taso a masarauta tare da tabbatar da zaman lafiya ga al’umma. Haka kuma yana zama Jakadan Sarki a al’amuran da suka shafi masarautar da gwamnati.
Babu shakka fadar Sarkin Biu ƙayatatta ce, wacce aka yi wa kwalliya da zayyane-zayyanen gargajiya, duk da cewa tsarin ginin na zamani ne. Ainihin babbar fadar Sarkin, an gina ta ne tun a shekarar 1904, ana dai yi mata kwaskwarima ne daga lokaci zuwa lokaci. Wani abu da ya ɗauki hankalina a fadar, shi ne hoton kada da aka zayyana a ƙofar fadar, wanda kuma shi ne tambarin Masarautar Biu. A tattaunawar da na yi da Mai Martaba Sarki, na tambaye shi ma’anar wannan hoto na kada. Ya shaida mani cewa garin Biu ya shahara da kadoji, inda a can shekarun baya, duk inda ka duba za ka gan su kuma ba su cutar da kowa. Don haka sai suka zama tamkar abokan zaman mutane a garin. “Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da suka sanya kada ya zama Tambarin Masarautar Biu, musamman domin jaddada zaman lafiya da jarumtaka,” in ji Sarkin na Biu.

Masarautar Biu na yin zumunci da sauran masarautu na sassan Najeriya, musamman ma na Arewa. Bisa ga haka, a yayin wannan bikin naɗi, sarakuna daban-daban daga sassan ƙasar nan suka halarta, wasu kuma suka aiko da wakilai. Misali, Sarkin Machina, Alhaji (Dokta) Bashir Albishir Bukar Machinama, OON da Sarkin Keffi, Alhaji (Dokta) Shehu Chindo Yamusa III, CON da Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Umar Suleiman da kansu suka halarci bikin. Haka kuma akwai sarakuna daga Kudancin Najeriya da suka halarta. Waɗannan kuwa sun haɗa da Oba (Dokta) Hammed Adekunle, CON, Makama Oyelude (Teghosun III), Oluwo na Daular Kuta daga Jihar Osun. Akwai kuma Oba Khalid Olabisi, Okere na Daular Shaki, da sauransu.
Tsarin makaɗan Sarautar Biu na da burgewa da ban sha’awa. Suna da mabusa algaita da makaɗa gangunan rataye. Daddaɗan sautin da suke samarwa, shi ke ingiza masu rawa su malkwaɗa jikinsu da juyawa daidai da amon kiɗan da busar, a gargajiyance. Masu rawa na riƙe da doguwar takobi zararra, suna haska ta sama da ƙasa, a yayin da suke taka rawa. Makaɗa da mabusa da masu rawar, dukkansu suna sanye da sufuru na kamala, manyan riguna masu aiki da launuka mabambanta, ga su kawunansu naɗe da rawunna – shiga dai ta sarauta. A haka suke yin layi a jere suna rawa, gwanin burgewa.

Ziyarar Jami’ar Sojojin Najeriya Da Ke Biu (NAUB):
Al’ummar Biu maza da mata, mutane ne masu ƙauna da daraja ilimi kuma suna da himma wajen shiga kowane irin aiki ko sana’ar zamani. Dalili ke nan a duk ma’aikatar da ka duba a Gwamnatin Tarayya, za ka tarar da ‘ya’yan Biu a cikinsu, da yawa ma shahararru ne da suka kai ƙololuwa a wuraren aikinsu. Laftanar-Janar Buratai, shi ne sanadiyyar samar da Jami’ar Sojojin Najeriya Biu, a lokacin da yake shugabantar Rundunar Sojojin Najeriya. A ranar 30 ga Oktoba, 2018 ce Shugaban Ƙasa kuma Kwamandan Rundunonin Tsaro na Najeriya (a lokacin), Muhammadu Buhari ne ya yi bikin buɗe ta.
An gudanar da Bikin Ɗaukar Ɗalibai na farko a ranar 21 ga Fabrairu, 2019. Jami’ar na da tsangayoyi biyar, ana koyar da kwasa-kwasan digiri guda 31 a fannonin kimiyya, fasaha, ƙere-kere da sauransu. Shugaban Jami’ar na farko shi ne Farfesa Usman Ahmadu Mohammed, na biyu, Farfesa David Iliya Malgwi, ta uku ita ce Farfesa Fatima Tahir. Sai kuma na huɗu, wanda ke kan mulki, Farfesa Kyari Mohammed. Ubangoyon Jami’ar kuwa shi ne, Manjo-Janar (mai ritaya), Mai Sarauta Felix Mujakperou, CFR, Orhue I, Orodje na Daular Okpe.

Jami’ar ita ce makaranta mafi girma a Biu kuma tana da wadataccen fili, ga gine-gine masu yawa kuma da tsari. A bana ne, ranar 28 ga Oktoba ta yaye ɗalibanta na zangon farko a fagage daban-daban. A ranar aka yaye ɗalibai 417, inda guda 20 suka samu Babbar Shaida Mai Daraja Ta Ɗaya, ɗalibai 207 suka samu Shaida Mai Daraja Ta Biyu (tsaka-tsaki), ɗalibai 186 suka samu Shaida Mai Daraja Ta Biyu (ƙarama), sai kuma ɗalibai 4 suka samu Shaida Mai Daraja Ta Uku amma babu wanda ya faɗi. Bisa kan haka suka bayar da Digirin Girmamawa ga fitattun mutane biyu, Laftanar-Janar Buratai, wanda aka karrama da Digirin Girmamawa na Doctor of Letters da Janar Felix Mujakperou da Digirin Girmamawa na Doctor of Laws.
Ziyarar Tsauni Da Tafkin Tilla:
Ɗaya daga cikin wurare masu armashi da ƙayatarwa da na ziyarta a Masarautar Biu, shi ne Tsaunin Tilla wanda a ƙasansa kuma yake tare da Tafkin Tilla. Wannan tsauni yana ƙauyen Kwaya Bura da ke Ƙaramar Hukumar Hawul, a Jihar Borno, kodayake a tsarin sarauta, yana ƙarƙashin Masarautar Biu.
Tsaunin Tilla yana da tsawo da faɗi sosai, domin daga ko’ina mutum zai iya hango shi. Kamar yadda masana suka tabbatar a littafin Tarihin Biu na Dokta Usman, tsaunin yana tsaye ne a daidai tsakanin Layin Tsakiyar Duniya (Latitude) Digiri 10.5500 daga Arewa da kuma Digiri 12.1333, tsakanin Layin Tsakiyar Duniya (Longitude) ta Gabas. Haka kuma yana da tsawon ƙafa 2,900 ko mita 883.92 daga ƙasa.
Shi kuwa Tafkin Tilla, na same shi cike da ruwa. Yana da faɗi iya ganinka, kuma kamar yadda Malam Umar Maidala ya tabbatar mani, ya ce yana da zurfi sosai kuma masunta na kama kifi a cikin shi lokaci-lokaci. Kodayake lokacin da muka je bakin tafkin, ba mu samu kowa ba, sai dai mun ga kwale-kwalen masunta a gefen shi. Mai yiwuwa masuntan suna kasuwa, kasancewar ranar Litinin ce, ranar babbar kasuwar Biu.

Akwai labaru masu ban al’ajabi game da wannan tafki. Misali, an ce ruwan tafkin ya taɓa ƙafewa shekaru 20 da suka gabata, wanda kafin nan bai taɓa ƙafewa ba. Amma cikin ikon Allah daga baya kuma sai ruwan ya dawo cike, kamar yadda na same shi. A can baya akwai kadoji da ke yawo a bakin tafkin, su ma sun ɓace, amma da sannu an ce sun fara dawowa. Kodayake ni dai a lokacin da muka je wurin, idona bai gane mani ko ɗaya ba. Wataƙila suna cikin ruwa ko ramukan gefen tafkin. Haka kuma an bayyana cewa ruwan kogin ana amfani da shi wajen maganin ƙaikayin jiki da kuma magance ciwon hauka, ƙarami ko babba.
Koma dai yaya abin yake, wannan tsauni da tafki suna ɗauke da ikon Allah kuma wuri ne da ke tattare da ni’imar kallo da burgewa. Zai taimaka sosai ga masu yawon buɗe ido da shaƙatawa. Babu mamaki yadda na ga hukuma ta gina ɗakuna a gefen tafkin domin zaman baƙi ‘yan yawon buɗe ido, kodayake a yanzu na ga duk sun lalace, saboda rashin gyara da kulawa. Lallai ya kamata Hukumar Kula Da Yawon Buɗe Ido da Shaƙatawa ta Jihar Borno ta kawo wa wurin ɗauki, domin kuwa idan aka inganta shi, zai iya samar da aikin yi da sana’a ga matasa da yawa, kamar kuma yadda zai samar da ƙarin kuɗin shiga ga Jiha da ma Gwamnatin Tarayya.
Ziyarar Maƙabartar Viukuthla Mai Al’ajabi:
Kauyen Viukuthla na ɗaya daga cikin wurare masu tsawon tarihi a Daular Biu, domin kuwa tarihi ya tabbatar da cewa Yamtarawala ya taɓa zama wurin, kafin daga bisani ya matsa can gaba saboda neman wadataccen ruwa da abinci.
Viukuthla na da muhimmanci babba a Masarautar Biu, saboda a nan ne maƙabartar da ake rufe sarakuna. Na shiga maƙabartar, wacce ke tattare da abubuwan al’ajabi. A ganawa ta da mai kula da maƙabartar, Malam Bukar Musa Viukuthla, ya shaida mani al’amura masu yawa na al’ajabi game da wannan maƙabarta.
“A wannan maƙabarta, komai yanayin zafi da ake ciki a gari, idan ka shigo cikinta, za ka samu natsuwa domin kuwa akwai sanyi da iska mai kyau. Haka kuma akwai ƙudajen zuma da suke ɓoye a kogon itacen kuka. Suna zaune a maƙabartar nan tsawon lokaci mai nisa. A duk lokacin da wani ko wasu gungun mutane suka shigo maƙabartar nan da mugun nufi, ƙudajen zumar za su fito su fatattake su,” a cewar Malam Musa.

Ya ce mani wani abin al’ajabi da maƙabartar shi ne, idan wani ya aikata laifi kamar sata daga cikin garin Biu da kewaye, muddin ya biyo ta cikin maƙabartar, to cak zai tsaya, ya kasa motsi har sai an kama shi. Ya ba ni misali da labarin wasu da suka taɓa aikata laifi, aka biyo su don a kama su, ɗaya daga cikinsu ya shiga maƙabartar, nan ya kasa motsi har aka kama shi sai da ya fuskanci hukunci amma sauran da ba su shiga ba, suka tsere.
Haka kuma ya bayyana mani cewa akwai macizzai da suka daɗe a wannan maƙabarta kuma ya nuna mani wasu duwatsu da ke kafe a ƙasa, suna da gurbi kaɗan. Ya ce a ciki ake zuba masu madarar shanu suna fitowa daga ramukansu suna shanyewa.
“Akwai wata al’ada da macizzan kan yi a duk lokacin da wani Sarkin Biu ya mutu, musamman idan aka zo binne shi,” a cewar Malam Musa.
“Misali, idan aka zo binne sarki, macizzan kan fito su tsaya a kan reshen waccan itaciyar kuka (ya nuna itace). Duk wanda ya shigo maƙabartar sai ya sunkuya ƙasa, idan ba haka ba mutum ba zai wuce ba. Sun fito a zamanin rasuwar Sarki Mai Umar. Amma a lokacin jana’izar Sarki Mai Mustapha, ba su fito ba, sai dai wani abin al’ajabin da ya bayyana. A daren da ya rasu akwai duhu amma ikon Allah ko’ina sai wani haske ya bayyana. Ko cikin ɗaki mutum yake sai da ya ga wannan haske har zuwa asubahi,” in ji shi.
Ya ce lokaci-lokaci Sarkin Biu da ayarinsa suna ziyartar maƙabartar domin yin addu’a ga iyayensu da kakanni da ke binne. Ya ce a can baya idan Sarki ya zo maƙabartar, yakan zauna kan dutse a gindin babbar itaciyar kuka da ke kusa da ƙofar shiga. Akan dama fura da nono a babbar ƙwarya. Sarki da hannunsa zai ɗauki ludayi, yara za su yi layi, ya riƙa ɗebowa yana ba su suna shanyewa, a matsayin sadaka.
“Amma saboda canjin zamani, shi Sarki na yanzu, Mai Mustapha II, idan ya zo ziyara, yakan sanya a yanka sa, a raba wa kowa naman, sannan yana raba kuɗi a matsayin sadaka,” a cewar Malam Musa.
Na ga ƙaburburan wasu daga cikin sarakunan Biu, waɗanda suka haɗa da marigayi Sarkin Biu Mai Ali Dogo (1908-1935) da na marigayi Mai Ali Gurgur (1935-1951) da na Mai Mustapha Aliyu (1959-1989) da kuma Sarki Mai Umar Mustapha Aliyu (1989-2020). Allah Ya ji ƙan su da rahama, Amin.
Babu shakka na ji yanayin sanyi da iska mai daɗi a maƙabartar, kodayake rufe take ruf da itatuwa daban-daban masu yalwar ganye, musamman itatuwan kuka da ɗorawa da bedi da sauransu. A lokacin da muka fito daga harabar maƙabartar zafin rana ya kaurara, sai na riƙa jin zafi, ba kamar yanayin sanyi na cikin maƙabartar ba.
Bayan mun fito daga maƙabartar, Malam Musa ya kai mu wajen wata itaciyar kuka, ita ma mai al’ajabi. Ga ta dai gangar jikinta a kwance, amma tana da rai, ba ta mutu ba. Ga rassa da ganyaye a jikinta. Ya ce a tarihi, itaciyar ta girmi duk wani mutum da ke Masarautar Biu a yau, domin kuwa kamar yadda ya ce, “shi kansa Yamtarawala ya iske ta a wurin.”
Ya bayyana mani cewa, kamar yadda kakanninsa suka shaida masa, lokacin da Yamtarawala ya zo Viukuthla shi da mutanensa, a reshen wannan itaciyar kuka ya sargafe kwarinsa da baka. “A lokacin da ya sargafe, sai kukar nan ta ranƙwafa ta kwanta haka. Tun daga lokacin har yanzu haka take a kwance, amma ba ta mutu ba,” in ji Malam Musa.
Na hau kan wannan kuka har Umar Maidala ya ɗauke ni hoto. A lissafin tarihi, wannan itaciyar kuka ta wuce shekara 400, domin tarihi ya tabbatar da cewa tun wajajen shekarar 1530 Yamtarawala ya je yankin Biu.
Ziyarar Ɗakin Karatu Na Farko A Biu:
Al’ummar Biu mutane ne masu son ilimi da martaba, don haka tun zuwan Turawan Mulkin Mallaka, ba su yi wasa da ilimin zamani ba, maza da mata. Na ziyarci ɗakin karatu na farko da aka fara ginawa a garin Biu tun zamanin Turawa. An yi masa kwaskwarima zuwa ginin zamani a shekarar 1978.

Shugaban ɗakin karatun, Malam Hussaini Yusuf ne ya kewaya da ni sassa daban-daban na ɗakin karatun. Na ga littattafai da yawa, duk da cewa mafi yawansu tsofaffi ne. Idan ka ɗeɓe littattafan Dokta Bukar Usman daban-daban da suka mamaye ɗakin karatun, sauran duk ba wallafar zamani ba ne.
Haka kuma na lura da cewa babu jaridu da mujallu a ɗakin karatun, kamar kuma yadda babu wadatattun kujeru da tebura domin masu karatu. Wasu sassa na rufin ɗakin ma yoyo suke, daga yadda na ga alamar ruwan sama da ya bushe. Wannan ke nuna cewa lallai akwai buƙatar hukumomi da ɗaiɗaikun mutane masu abin hannu, su taimaka domin inganta da gyara wannan ɗakin karatu, musamman saboda muhimmancin ilimi.
Malam Yusuf ya shaida mani cewa, “Idan Allah Ya kai mu Juma’a, 3 ga Nuwamba, 2023, zan yi ritaya daga aiki, domin kuwa shekarata 33 a aiki.”
Ke nan a yanzu da nake rubuta wannan rahoto, tuni ya ajiye aikin da ya daɗe yana yi a rayuwarsa. Ya kuma shaida mani cewa a zaman da ya yi a wannan ɗakin karatu, ya yaba da halin girma da bunƙasa ilimi na Dokta Bukar Usman. “Wannan mutum ya taimaka sosai da gudunmowar littattafansa ga wannan ɗakin karatu. Idan ka duba nan, za ka ga duk littattafansa ne. A duk lokacin da ya wallafa sabon littafi, katon-katon yake aiko mana. Allah Ya saka masa da alheri, Ya ƙara masa himma da niyyar alheri,” in ji Malam Yusuf.
Ziyarar Makarantar Koya Sana’o’i Ta Biu:
Mutanen Biu, maza da mata, matasa da yara jajirtattu ne masu haƙilon neman na kansu. A yadda na ga suna kai-kawo a wuraren aiki, gonaki, kasuwanni da makamantansu, da wuya ka ga mutum yana zaman banza a Biu. Baya ga kasancewarsu manoma na gaske, sun kuma yi fice a aikin gwamnati da kasuwanci.
Na ƙara tabbatar da himmar al’ummar Babur/Bura, lokacin da na ziyarci Makarantar Koyon Sana’o’i ta garin Biu, a ranar Litinin, 30 ga Oktoba, 2023. Wannan makaranta, Gwamnatin Jihar Borno a ƙarƙashin Gwamna Farfesa Umara Zulum ta gina ta da kuma samar da kayayyakin koyon sana’a. A nan na gana da Mataimakin Shugaban wannan katafariyar makaranta, Mista Steven Yaro Mshelia, wanda bayan shi da wasu malaman makarantar sun tarbe mu cikin martaba da karimci, sai kuma suka zagaya da mu sassa da azuzuwa daban-daban.

Mista Steven ya shaida mani cewa Gwamna Zulum ne ya assasa gina ta a shekarar 2022, aka kammala a watan Agusta na 2023; sannan aka kama aikin koyarwa gadan-gadan a farkon watan Satumba. Ya ce ganin ba su da isassun ma’aikata, Gwamnan ya ba su ikon nema tare da ɗaukar ƙwararrun malamai 36, ƙari kan waɗanda suke da su.
“Babban dalilin samar da wannan makaranta shi ne, a rage zaman banza ga matasa maza da mata, ta hanyar koya masu ayyuka da sana’o’in da za su dogara da kansu. Ka san masu iya magana sun ce, mai zaman banza, Shaiɗan ne abokin tunaninsa.
“Jihar Borno na da ƙishirwar ci gaba ta fuskar ƙere-ƙere, don haka kafa wannan makaranta ta zo a kan lokaci, musamman ma yadda Gwamna Zulum ya wadata ta da kayan aiki ingantattu kuma na zamani. Don haka ina kira ga matasa da su tashi tsaye, su maida hankali wajen koyon sana’o’in dogaro da kai. Shi kuma Gwamna, Allah Ya saka masa da alheri, Ya yi masa jagora;” in ji Steven.
Da yake zagayawa da mu sassan makarantar, shugaban ya ce suna da sassa 16, inda suke koyar da sana’o’in noma, gyaran mota da injina, sarrafa ƙarafa, aikin kafinta, ilimin kwamfuta, jima, saƙa, gyaran gashi, gini, ɗinki da sauransu.
A ɓangaren koyon gyaran gashi, na gana da Zainab Musa Ibrahim, wacce ta ce tana alfahari da jin daɗin abin da take koyo. Ta ce kwas ɗin wata shida za ta yi, amma tun a yanzu cikin wata biyu ta iya abubuwa da yawa da suka danganci sana’ar.
“Ina fahimta sosai kuma malamanmu suna ƙoƙari sosai. Burina idan na gama, in buɗe shago domin gyaran gashi, in taimaki kaina da sauran al’umma. Ina godiya ga Allah da kuma gudunmowar da Gwamnatin Gwamna Zulum ta bada wajan gina wannan makaranta. Na gama NCE, babu aiki, babu sana’a, don haka na zo nan domin in koyi sana’ar dogaro da kaina,” a cewar ɗaliba Zainab.
A sashen gyaran mota da injina kuwa, nan ma na ga ɗalibai cikin himma, suna koyon abin da ake koya masu. Ɗaya daga ɗaliban da na tattauna da shi, Musa Suleiman Alƙali ya ce suna fahimtar darussan sosai. Ya ce daga abin da suka koya a wata biyu, zai iya buɗe injin kowace mota, ya gyara kuma ya maida shi daidai. “Burina idan na gama kwas ɗin nan, in buɗe gareji domin gyara motocin al’umma a matsayin sana’ar dogaro da kaina. Ina ba matasa ‘yan uwana da su daina zaman banza, su koyi sana’a domin taimakon kansu. Kada matashi ya tsaya, ya ce dole sai aikin gwamnati, domin ba kowa ne zai samu aikin ba,” in ji matashin.
A sashen kwamfuta kuwa, na samu matasa maza da mata suna ta himmar nazari. Cikinsu na gana da Esther Ayuba, wacce ta yaba da abin da take koyo, inda take cewa: “Idan na kammala kwas ɗina, zan buɗe shagona, inda zan riƙa gudanar da sana’ar da ta shafi kwamfuta, domin taimakon al’umma ta wannan ɓangaren. Ina ba mata ‘yan uwana shawara su gane cewa, aikin kwamfuta ba na maza ne kaɗai ba, su shigo su ma a dama da su. Matasa su yi ƙoƙarin zuwa makarantar nan domin koyon sana’ar dogaro da kansu, maimakon zaman banza. A madadin ‘yan uwana ɗalibai, muna godiya ga Gwamna Zulum wajan taimaka wa wannan makaranta. Allah Ya saka masa da alheri.”
Babu shakka, daga yadda na ga makarantar nan cikin armashi da ingantattun kayan aiki da yadda na ga malamai da ɗaliban cikin himma, na tabbatar da cewa lallai al’umma za su amfana sosai daga gare ta.
________
Wannan shi ne rahoto kashi na 4. A kashi na 5 kuma na ƙarshe, zan maida hankali ne kan wasu daga cikin muhimman mutane da na sani ko na gana da su a Biu. Waɗannan kuwa sun haɗa da Mai Martaba Sarkin Biu, Mai Mustapha Umar Mustapha II da Dokta Bukar Usman, OON, tsohon Babban Darakta a Fadar Shugaban Ƙasa da Laftanan-Janar (mai ritaya) Tukur Yusufu Buratai, CFR, tsohon Hafsan-Hafsoshin Rundunar Sojojin Najeriya da Sarauniyar Biu da Birman Biu, Barista Ibrahim Shehu Biu da Shugabar Asibiti Na Farko da ke Biu da fitaccen ɗan kishin ƙasa, Dokta Wandali Arhyel Dibal da Umar Mohammed Maidala da sauransu.













