SABON ZUMUNCI: KWANKWASO DA GANDUJE SUN YI SULHU
Wata majiya mai ƙarfi da ke da kusanci da tsofaffin gwamnonin Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Gabduje ta shaida wa SHANSHANI cewa, jigajigan siyasar na Jihar Kano sun yi sasanci da juna.
Al’amarin mai kama da almara ya faru ne a maraicen jiya Alhamis, inda majiyar ta ce giwayen biyu sun ɗaukar wa juna alƙawarin ɗinkewa wuri ɗaya, domin ci gaba da yi wa al’ummar Jihar Kano da ƙasa baki ɗaya hidima.
Da yake ƙarin haske dangane da wannan al’amari, wani na hannun daman Sanata Kwankwaso, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce sasanci tsakanin manyan ‘yan siyasar biyu ya tabbata ne, bayan da Ganduje ya ziyarci Kwankwaso a gidansa da ke Abuja, a jiya Alhamis.
Ya ce tsofaffin gwamnonin biyu sun killace kansu ne a ɗaki su biyu, inda suka kwashe kusan awa ɗaya suna ganawa, kafin daga bisani suka fito, inda Kwankwason ya yi wa Gabduje rakiya har ya shiga motarsa ya fita daga gidan.
“Bayan da suka fito daga ɗakin da suka gana, mun gan su suna ƙyakyata dariya, inda Kwankwaso ya raka Ganduje zuwa motarsa. A haka suka yi bankwana da juna.” A cewar na hannun damar Kwankwaso.
Alaƙa dai tsakanin Kwankwaso da Ganduje ta fara tsami ne tun daga shekarar 2015, bayan da shi Ganduje ya amshi ragamar mulkin Kano daga hannun Kwankwaso.
A haka aka yi ta tafiya cikin gaba da juna, inda ta kai ga Kwankwaso ya fita daga Jam’iyyar APC zuwa PDP, inda daga bisani kuma ya zarce zuwa Jam’iyyar NNPP.
Ko me zai biyo bayan wannan sulhu tsakanin giwayen biyu? Masu fashin baƙin alƙaluman siyasa suna ganin cewa al’amura za su inganta a siyasance a Jihar Kano, musamman zaman gaba da juna zai kawo ƙarshe, kamar kuma yadda siyasar zage-zage tsakanin magoya bayansu za ta mutu.
Haka kuma, wasu na ganin cewa wataƙila Kwankwaso da dukkan muƙarrabansa za su yi hijira daga NNPP zuwa APC.
Sai dai kuma wani al’amari da zai ɗauki hankali shi ne, yaya za ta kasance a batun shari’ar Gwamna Abba Kabir Yusuf da Yusuf Gawuna?
Ko me ke nan dai, yanzu kallo ya koma sama, inda za a saurari manyan ‘yan siyasar biyu, su bayyana wa al’umma inda suka dosa.
A cewar wani ɗan siyasa a Kano, “muddin dai Ganduje da Kwankwaso sun ɗinke wuri guda, to babu shakka su ne jagororin Jihar Kano a siyasance, yadda duk suka dama, dole haka kowa zai sha!
~~~~~~~
SANARWA:
Wannan labari, almara ce daga bakin SHANSHANI. Bai faru ba da gaske. To amma ku masu karatu, mene ne ra’ayinku? Yaya kuke gani, idan aka ce waɗannan manyan ‘yan siyasa sun sasanta da juna?
~~~~~~~













Congratulations,