• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

SHARI’AR MUSULUNCI: Bayan Yaƙi Da Baɗala, A Yaƙi Ɓarayin Gwamnati, Hanci Da Rashawa

Abdullahi Dahiru by Abdullahi Dahiru
November 3, 2023
in Gizago
0
SHARI’AR MUSULUNCI: Bayan Yaƙi Da Baɗala, A Yaƙi Ɓarayin Gwamnati, Hanci Da Rashawa
46
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

SHARI’AR MUSULUNCI: Bayan Yaƙi Da Baɗala, A Yaƙi Ɓarayin Gwamnati, Hanci Da Rashawa

                    ~~~~~~~
Ra’ayi Daga Abdullahi Dahiru
                     ~~~~~~~

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026

A shekarar 1999, Gwamnan Zamfara na lokacin, Ahmad Sani Yeriman Bakura ya yi shelar ƙaddamar da Shari’ar Musulunci a jiharsa. Aka yi gagarumin taron ƙaddamarwa.

Ba a daɗe ba abin ya zama kamar wutar daji. Sauran jihohin Arewa masu rinjayen musulmi, su ma suka ƙaddamar.
Bayan ƙaddamarwar, aka ce duk waɗansu dokokin addinin Musulunci za a ɗabbaƙa su, ba wadda ba za a yi ba. Aka sha riciki da Gwamnatin Tarayya da al’ummar da ba musulmi ba saboda nuna adawar su da ƙaddamar da shariar.

Musulmi sun goyi bayan ƙaddamar da shari’ar ce da fatan cewa za a yi adalci sannan rayuwarsu za ta inganta. Amma sai su masu gudanar da ita shari’ar suka mai da hankali kan hukunce-hukuncen da suka shafi laifuffuka kamar shan giya da zina da sata. Suka nuna kamar su ne kaɗai shari’a; in an tsaida su za a yarda ana Shari’ar Musulunci.

Amma ba su maida hankali wajen riƙe amanar dukiyar mutane da yi musu ayyukan da za su kawo ci gaban al’umma ba, kamar bunƙasa ilmi, lafiya da sauransu.

Sai ya zama a waɗannan jihohi babu abin da ya canza wajen harkar tafiyar da gwamnati. Aka ci gaba da cin hanci da rashawa da satar kuɗin al’umma, babu wani hukunci.

A Zamfara aka kama wani mai suna Bello Jangeɓe da laifin sata, aka zartar masa da hukuncin yanke hannu kuma aka yanke hannun. Amma in an ƙalubalanci wadannan gwamnatocin cewa, me ya hana hukunta ɓarayin gwamnati? Sai su ce ai su cin amana suka yi ba sata ba, babu hukuncin haddi a kansu.

Aka kafa hukumomin hisba a waɗannan jihohin don su tabbatar da bin dokokin shari’a.

A dai Jihar Zamfara, an samu mata da aka samu sun haihu bayan aurensu ya mutu da daɗewa, aka yi musu zargin zina. Kotuna suka yanke musu hukuncin rajamu. Sai da suka ɗaukaka ƙara aka soke hukuncin. Hisba suna bi gidajen giya da mata suna kame suna farfasa giya.

Haka aka ci gaba har wannan lokacin. Amma bayan irin ayyukan yaƙi da sai da giya da kamen mata masu zaman kansu, akwai sauran hukuncin shari’ar da ake ɗabbaƙawa?

Su kansu hukunce-hukuncen, kamar an ware waɗansu al’umma ne ake hukunta su kuma a ƙyale masu galihu da manya, idan sun yi irin waɗannan laifuffukan.

Misali, a Jihar Kano an sami bidiyo na wani shugaba yana saka Daloli a aljihu. Ga maganganu ana yi na kwangilolin tituna har da kana sunayen titunan da unguwannin da suke. Inda ake shari’a ta Allah, lallai ya kamata a bincika wannan zargi, koda shugaban yana da kariya a Shari’ar Bature. Aƙalla a kira shi a tuhume shi, cewa kudin mene ne?

Wataƙila a saka shi ya rantse cewa kuɗin nan ba satar su ya yi ba, nasa ne na halal. Shin an yi haka?

Kuma wannan gaba ɗaya al’ummar ce ba da gaske take yi wajen neman adalci ba.

Hisba tana kamen giya ta farfasa. In ka duba a cikin Musulmi ɗari, nawa suke shan giya? Wataƙila ka sami mutum biyar. Masu shan ƙwaya da wiwi fa? Za ka same su da yawa. Me ya sa aka mai da hankali kan giya ita kaɗai, aka ƙyale sauran kayan maye? Ka ga dole waɗanda ake ƙwace wa giyar, waɗanda yawanci ba musulmi ba ne, su yi zargin su kaɗai aka ware ake aiwatar da hukunci a kansu. Bayan kuma an ce shari’a ba za ta shafe su ba.

Yaran da ake kamawa da zargin yawon banza, in ka duba yawanci wani hali ne na rayuwa da rashin galihu ya jefa su haka. Kuma ana kamen karuwai, fyaɗe da jarirai da ake haifa ba iyaye suna ƙaruwa a cikin lunguna. Maimakon a nemi hanyar fid da su daga wannan halin sai a kira ‘yan jarida ana holin su. Abin ya zama kamar cin zarafi maimakon neman gyaruwar waɗanda aka kama ɗin.

Su kuma jagorori, ‘ya’yansu suna makarantu ko a ƙasashen waje ko na gida, ba yadda za su shiga waɗannan matsalolin.

Akwai lokacin da za ka ga an kama samari an yi musu aski saboda sun tara gashi na rashin tarbiyya. Amma kuma ga ‘yan ƙwallo da ‘yan fim suna da irin wannan gashin ko wanda ya fi shi muni, ana kallon su amma ba a yi musu komai ba.

Mutane sun ga me ya faru a lokacin bikin ‘yar gwamna da ya wuce. An ɗauka Hisba za su kai ɗauki, ba su kai ba. Ko da ba su kai ba, lokacin za su iya gayyatar mutanen, su tuhume su yadda suke yi wa sauran mutane. Amma uzurin da suke bayarwa shi ne, abin ya fi ƙarfinsu kuma tun da suna ɗabbaƙa shari’a kan talakawa, ba dole su ɗabbaƙa kan shugabanni ba.

Ga jihohin da ake shari’ar, irin su Zamfara suna fama da matsalolin garkuwa da mutane da hare-haren ‘yan bindiga. Kuma an ga yadda gwamnatocinsu suke wabdaƙa da kuɗaɗen al’umma kuma sun kasa warware waɗannan matsaloli.

Waɗansu matsalolin maganinsu ma shi ne ba da ilmi da rage talauci da riƙe amanar dukiyar al’umma. Shin shugabannin suna yin haka?

Da yawa in mun yi irin waɗannan maganganu, ana yi mana zargin munafunci. Amma maganar gaskiya akwai gyara, yadda ake tafiyar da Shari’ar Musulunci a Arewacin Najeriya.

                     ~~~~~~~
Dokta Abdullahi Dahiru, ƙwararren likita ne kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum.
                    ~~~~~~~

Previous Post

Dr. Buratai in Ibadan to Deliver Paper on National Security Tomorrow

Next Post

Kasafin N18b: INEC za ta biya ma’aikata 16,000 alawus ɗin su, ba a zaɓen Bayelsa, Imo da Kogi za ta kashe kuɗaɗen ba – Yakubu

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
Zaɓen gwamna: Mutum 2,318,919 za su yi zaɓe a Imo, 1,833,160 a Kogi, 1,017,613 a Bayelsa, inji INEC

Kasafin N18b: INEC za ta biya ma'aikata 16,000 alawus ɗin su, ba a zaɓen Bayelsa, Imo da Kogi za ta kashe kuɗaɗen ba - Yakubu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

YAU MALUMFASHI MUN YI RASHI

YAU MALUMFASHI MUN YI RASHI

July 26, 2025
YADDA NA ƊAUKI SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA

YADDA NA ƊAUKI SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA

July 19, 2025
My Takeaways from IBB’s Autobiography

My Takeaways from IBB’s Autobiography

March 18, 2025
Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Masallacin Dr. Yunusa Zuba- Abuja

Huɗubar Jumu’a A Taƙaice Daga Masallacin Dr. Yunusa Zuba- Abuja

August 4, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.