• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, June 9, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

HARIN JIRGIN SAMA GA MUSULMI: Ya Wajaba A Zurfafa Bincike Kuma A Biya Diyya

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
December 7, 2023
in Babban Labari
0
HARIN JIRGIN SAMA GA MUSULMI: Ya Wajaba A Zurfafa Bincike Kuma A Biya Diyya
15
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

HARIN JIRGIN SAMA GA MUSULMI: Ya Wajaba A Zurfafa Bincike Kuma A Biya Diyya

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

May 13, 2026
Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

May 9, 2026

~~~~~~~
Abin da zai faru ƙaddararre ne daga Allah. Babu shakka ga wannan batu. Sai dai kuma abu ne mai kyau kuma mai tsari ga al’umma da su ɗauki darasi daga dukkan wani al’amari da ya faru da su, domin gyaran gaba.

Ina magana ne game da batun yadda wani jirgin Sojojin Najeriya ya jefa bamabamai ga wasu gungun mutane da suke bikin Mauludin Manzon Allah (saw), da maraicen Lahadi (3-12-2023) a ƙauyen Tudun Biri na Ƙaramar Hukumar Igabi, Jihar Kaduna, inda mutane sama da 80 suka rasa rayukansu, da dama kuma suka samu munanan raunuka.

A yau ba sai gobe ba, al’ummar Arewa, musamman Musulmi muna cikin jarabawa mai girma. An ƙulla mana ƙullalliya, an kitsa mana kitsatssa. An shirya mana yaƙin sunƙuru domin a wargaza mu. Lallai ne mu yi karatun-ta-natsu. Lallai ne mu hankalta, mu dawo cikin hayyacinmu, domin saita al’amuranmu zuwa hanya madaidaiciya.

A tsawon shekaru masu yawa da suka gabata, an ƙulla wa Arewa makirci da Boko Haram, wanda a sanadiyyar haka aka salwantar da rayuka marasa adadi. An tozarta iyalai da dama, an talauta wasu da dama, kamar yadda aka haddasa gaba da shakku da tsangwama tsakanin al’ummu.

An shigo mana da ‘yan bindiga daɗi, masu garkuwa mutane domin kuɗin fansa. A sanadiyyar haka, an ci zafafin mata, an tarwatsa iyalai, an maida wasu zawarawa, an maida yara marayu, an lalata tattalin arziƙin Arewa na noma da kiwo.

A makon jiya kuma sai ga wata bahallatsar da aka haddasa mana a Tudun Biri na Ƙaramar Hukumar Igabi, Jihar Kaduna.

Hukumomin Sojojin Najeriya sun ce wannan al’amari ya faru ne wai bisa “kuskure.” Kuskure kuwa? Lallai akwai tambayoyi da dama da ya kamata a yi, domin tantance wannan batu.

Shin waɗannan bayin Allah da aka jefa wa bam, ba bikin Mauludi suke gudanarwa ba? Shin hukumar ‘yan sanda da ta farin kaya ba su da masaniyar wannan biki?

Shin a yayin da jami’an da ke sarrafa jirgin nan suka ga dandazon mutane, ba su yi bincike mai zurfi ba? Shin sun tuntuɓi Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kaduna da Daraktan SSS domin neman ƙarin bayani ko kuwa kawai yanke hukunci suka yi?

Shin babu na’urar da za ta tantance abin da mutanen nan suke gudanarwa a cikin jirgin nan? Shin wane Kwamanda ne ya ba da umurnin saka waɗannan bamabamai a karo fiye da biyu? Kuma jefa bom shi ne mataki na ƙarshe da ya kamata a ce an ɗauka a daidai lokacin?

A daidai wannan lokaci da muke da Shugaban Ƙasa Musulmi, mataimakinsa Musulmi, Ministan Tsaro, babba da ƙarami duk Musulmi, lallai bai kamata a aikata wa al’ummar Arewa irin wannan ta’addanci da sunan kuskure ba.

Ya kamata shugabanninmu da mu kanmu mabiya mu gyara al’amuranmu. Mu daina yaudarar juna. Lallai ne hukumar ƙasa ta yi ƙwaƙƙwaran bincika domin hukunta duk mai hannu cikin wannan aika-aika. Kuma a yi hanzarin biyan diyya ga iyalan waɗanda suka rasu.

Lallai na yarda da Sha’iri mai fiƙira, Malam Sani Yusuf Ayagi, wanda ya tsara waɗannan baitoci:

Wata dai shari’ar sai Allah,
Ba dai mutum alƙali ba!

Shari’a ƙwarai ta lalace,
Ku biyo ni dangi kwai zance,
Zan bayyana ban ɓoye ba.

Ni na ji manya na cewa,
Shari’a ƙwarai gatan kowa,
Na yarda ba da musu nai ba.

Duk wanda an ka ci zalinshi,
Shari’a ka kai wa kukanshi,
Da a taimakar ba ƙarya ba.

Nan za a share hawayenshi,
Ta tsaya ta ƙwato haƙƙinshi,
Ba za ta yarda a danne ba.

A gurin shari’a kun gane,
Dukkan mutane kaf nata ne,
Ba ta nuna bambanci ɗaya ba.

Wani shugaba ko mai mulki,
Matsayinsa ko ya kai sarki,
Ba za ta duba muƙami ba.

Muna roƙon Allah (swt) Ya ji ƙan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan hari. Waɗanda suka samu raunuka da asarar dukiya kuwa, Allah Ya ba su lafiya, Ya kuma mayar masu da mafi alheri.

~~~~~~~
Bashir Yahuza Malumfashi, Babban Editan Mujallar Taskar Gizago, marubuci kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum.
Alhamis, 23-05-1445 (Hijriyya)
07-12-2023 (Miladiyya).
~~~~~~~

Previous Post

Ministan Yaɗa Labarai Ya Kafa Kwamitin Wayar Da Kan Al’umma, Cusa Ɗa’a, Kishin Ƙasa Da Kyawawan Ɗabi’u

Next Post

Minista Ya Buƙaci Masu Sana’ar Talla A Kafafen Yaɗa Labarai Su Faɗakar Da Jama’a Game Da Shirye-Shiryen Tattalin Arziki Na Gwamnatin Tinubu

Related Posts

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano
Babban Labari

Ta Banka Wa Mijinta, Kishiyarta Da Yara Wuta A Kano

May 13, 2026
Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi
Babban Labari

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

May 9, 2026
Yan ta’addan Daji Kafirai Ne  – Sarkin Musulmi
Babban Labari

Yan ta’addan Daji Kafirai Ne – Sarkin Musulmi

May 8, 2026
Next Post
Gargaɗin Amurka kan Nijeriya na tada hankulan jama’a, kuma ya na yin illa ga tattalin arzikin ƙasa – Minista

Minista Ya Buƙaci Masu Sana'ar Talla A Kafafen Yaɗa Labarai Su Faɗakar Da Jama'a Game Da Shirye-Shiryen Tattalin Arziki Na Gwamnatin Tinubu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

A Rayuwa: Alheri Danƙo Ne

A Rayuwa: Alheri Danƙo Ne

November 11, 2025
Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Ɗan Majalisa Aminu Acid

Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Ɗan Majalisa Aminu Acid

October 1, 2023
Rage Raɗaɗin Talauci: Attajirai Ku Yi Koyi Da Sabi’u Mahuta

Rage Raɗaɗin Talauci: Attajirai Ku Yi Koyi Da Sabi’u Mahuta

August 7, 2023
Aure Sunnar Manzo (saw): Isma’il Angon A’isha

Aure Sunnar Manzo (saw): Isma’il Angon A’isha

October 31, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido
  • Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji
  • Wasu Daga Manyan Ayyukan Sardauna Ga Al’ummar Arewa (1954-1966)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

Sharhin Littafin Tarihin Rayuwar Sule Lamido

June 8, 2026
Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji

Illolin Yaɗa Hotuna Da Bidiyon Aika-Aikar ‘Yan Ta’addar Daji

June 7, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.