Dharmendra: Ta’aziyyar Bankwana Da Mashahurin Afto
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

•••••••
A jiya Litinin, shahararren afton finafinan Indiya, Dharmendra, wanda aka fi sani da lakabin “He-Man” ya rasu bayan ya sha fama da jinya. Ya rasu yana da shekaru 89, abin da ya bar babban giɓi a masana’antar shirya finafinai ta Bollywood, wacce ya yi wa hidima ta sama da rabin ƙarni.
Rahotanni sun nuna cewa ya rasu ne a gidansa da ke Mumbai, bayan samun matsalar numfashi. Mutuwarsa ta girgiza masana’antar Bollywood, la’akari da gagarumar gudunmawar da ya bayar a fagen finafinan Indiya cikin shekaru 60 da suka gabata.
An haifi Dharmendra Kewal Krishan Deol a ranar 8 ga Disamba, 1935, a ƙauyen Nasrali na Jihar Punjab. Iyayensa ba wasu hashaƙai ba ne, amma za a iya kiran su da matsakaita. Mahaifinsa malamin makaranta ne, wanda daga bisani har ya kai ga zama shugaban makaranta.
A rayuwarsa, Dharmendra bai bi sahun iyayensa ba a fannin sana’a. Maimakon karantarwa, shi sai ya zaɓi shiga harkar fim. Ya fara fitowa a fim ɗinsa na farko a shekarar 1960, mai suna Dil Bhi Tera Hum Bhi Tere kuma cikin gajeren lokaci ya samu farin jini saboda kwarjininsa da kuma kamala a idon jama’a.
A tsawon shekaru, Dharmendra ya nuna bajintarsa a fannoni daban-daban, daga finafinai na soyayya zuwa na ban tsoro, barkwanci, har ma da na yaƙi. Ɗaya daga cikin finafinansa mafi tasiri shi ne Phool Aur Patthar (1966), wanda ya zame masa babban mataki a harkar sana’arsa. Haka kuma ya haskaka a fim ɗin Haqeeqat (1964), wani babban fim, wanda ya bayyana labarin yaƙi tsakanin ƙasar China da Indiya. Wannan fim ya yi fice sosai kuma ya ƙara wa Dharmendra kwarjini.
A rayuwarsa ta fim, an yi ittifakin cewa babu wani fim da ya fi kambama sunansa kamar Sholay (1975), bisa la’akari da rawar da ya taka a matsayin Veeru. Haka kuma, Dharmendra ya nuna hazaƙa a manyan finafinai irin su Chupke Chupke, ta fannin barkwanci. Kamar kuma yadda ya nuna hazaƙarsa ta fannin jaruntaka a fim ɗin Mera Gaon Mera Desh. A cikin wannan fim ne ya ƙara nuna jaruntaka da salon ban tsoro kuma hakan ya ƙara masa farin jini sosai ga ‘yan kallo.
Baya ga fitowarsa a fim, Dharmendra ya taka rawa a bayan fage, a matsayin mai shirya finafinai. Ɗaya daga cikin aikinsa mafi tasiri a wannan ɓangaren, shi ne Ghayal, fim ɗin da ɗansa Sunny Deol ya fito a ciki, wanda kuma ya samu yabo sosai. Ya kuma samu manyan kyaututtuka a harkar fim, ciki har da Filmfare Lifetime Achievement Award a 1997 da ta Padma Bhushan, wacce ya samu daga Gwamnatin Indiya a 2012 saboda gagarumar gudunmawarsa ga masana’antar Bollywood.
A bayan fage, Dharmendra ya shahara saboda halayensa na kirki, tawali’u da kusanci da masoyansa. Har zuwa shekarun ƙarshensa yana tattaunawa da jama’a a kafafen sada zumunta, ya rika tafiyar da rayuwarsa mai sauƙi. Dharmendra yana tuƙa babur, yana noman gonarsa, yana kuma bayar da shawarwari da nasihohin rayuwa ga mutane. Wannan hali nasa ya ƙara masa daraja da ƙauna a zukatan mutane da dama, tsofaffi da matasa, maza da mata.
Shin Dharmendra mabiyin wane addini ne? Tun da farko dai shi mabiyin addinin Sikh ne, wanda addinin gargajiya ne a ƙasar Indiya. Sai dai kuma a shekarar 1980, lokacin da zai auri matarsa ta biyu, Hema Malini, ya musulunta. A lokacin ne ma ya canja suna zuwa Dilawar Khan.
Marigayi Dharmendra ya bar duniya yana da shekara 89. Ya bar iyalansa, ciki har da matarsa ta farko, Prakash Kaur da matarsa ta biyu, Hema Malini. Ya bar ’ya’yansa Sunny Deol, Bobby Deol, Esha Deol da Ahana Deol.
Babu shakka mutuwarsa ta bar babban giɓi a masana’antar finafinan Indiya, musamman ganin cewa ya fito cikin finafinai sama da 300 a rayuwarsa. Wani abin da yake dahir shi ne, duk da cewa Dharmendra ya rasu amma aikin da ya bari zai ci gaba da wanzuwa a zukata da tarihin finafinan Indiya. Muna roƙon Allah ya ji ƙan shi da rahama.
_______________












