• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Tuesday, September 15, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

FAƊA DA ‘YAN TA’ADDA: Malam Dikko Kada Ka Shiga Daji – Abdullahi Mahuta

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
October 16, 2023
in Babban Labari
0
FAƊA DA ‘YAN TA’ADDA: Malam Dikko Kada Ka Shiga Daji – Abdullahi Mahuta

Gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa

38
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

FAƊA DA ‘YAN TA’ADDA: Malam Dikko Kada Ka Shiga Daji – Abdullahi Mahuta

~~~~~~~
An yi kira da nusarwa ga Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa da cewa ya canja tunani, kada ya yarda ya shiga daji domin faɗa da ‘yan ta’adda, kamar yadda ya ayyana a hirarsa da BBC Hausa.

Related posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026

Fitaccen ɗan siyasa a Jihar Katsina, Malam Abdullahi Ibrahim Mahuta ne ya bayar da wannan shawara ga gwamnan, a shafinsa na Facebook.

Kamar yadda ya ce, “ina wannan rubutu ne a dalilin wata hire da mai girma gwamna ya yi kwanan nan da gidan rediyo dio na BBC.

“A wannan hira, gwamna ya ƙara jaddada aniyarsa ta bin jami’an tsaro cikin daji domin a yaƙi waɗannan ‘yan ta’adda tare da shi.”

Mahuta, ya ci gaba da cewa, “duk wanda ya yi la’akari da matakan da Dokta Dikko Raɗɗa ya fara ɗauka domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a Jihar Katsina zuwa yanzu, ba na tsammanin akwai mai sauran shakku na game da wannan niyya da sadaukarwa nasa.

“A bisa haka ne nake kira da kuma tunasar da gwamna cewa ɗaukar makami da shiga daji ba naka ba ne yallaɓai; ba na shugaba ba ne.

“Kamar yadda aka ruwaito sayyidina Abubakar ya taɓa faɗar cewa ‘abin da ke tafiyar da al’umma shi ne hikima ta dattawa da kuma ƙarfin jiki na matasa.’

“Abin da ke kanka a yanzu shi ne amfani da ilimi, hikima da basira da Allah Ya ba ka, domin samowa da kuma tsara hanyoyin da za a bi wajen magance wannan matsalar, kamar yadda ka fara yi a yanzu.”

Ɗan siyasar ya kuma ci gaba da kawo dalilan da ya sa yake nusar da Gwamnan, inda ya ce, “amma ainahin aiwatar da ko gudanar da yaƙin a daji, to wannan kuma na matasa ne da sauran jami’an tsaro, waɗanda ke da horo na musamman.

“Yallaɓai, idan da a ce cikin aikin soja kake, zuwa yanzu da kake da shekara 55, da yanzu kana kan muƙamin Janar. To su kuma Janarori ba su zuwa fagen daga, sukan yi tunga ne a tsakiya, suna shirya hikimomi da dabarun yadda za a fafata yaƙin a can filin daga.

“Ya mai girma Gwamna, mun fahimci irin himma da azamarka bisa ɗawainiya ga al’umma. Mu ma muna tare da kai a wannan himma amma don Allah kada a shiga dajin nan da kai.

“Mun san cewa alƙawari ne ka ɗauka lokacin kamfen, cewa za a shiga daji da kai. To ni dai na yafe wannan alƙawarin. Allah Ya kawo mana ƙarshen wannan matsalar a ƙasarmu.”
~~~~~~~

Previous Post

SATAR AZZAKARI: Gaskiya Ko Ruɗanin Tunani?

Next Post

Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’

Related Posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?
Babban Labari

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta
Babban Labari

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya
Babban Labari

KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya

August 29, 2026
Next Post
Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’

Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar 'Baakoren Akure'

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

Sharhin Littafin Faɗakarwa Dangane Da lllar Miyagun Ƙwayoyi

December 24, 2024
Musulmin Kudancin Najeriya Sun Jaddada Mubaya’a Ga Sarkin Musulmi

Musulmin Kudancin Najeriya Sun Jaddada Mubaya’a Ga Sarkin Musulmi

February 13, 2026
Abdullahi Garba Faskari Ne Sabon Sakataren Gwamnatin Katsina

Abdullahi Garba Faskari Ne Sabon Sakataren Gwamnatin Katsina

August 7, 2023
Kana Son Zaman Lafiya? Ka Bi Shawarar Sani Rogo

Kana Son Zaman Lafiya? Ka Bi Shawarar Sani Rogo

May 29, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78
  • ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya
  • SUNANTA UMMU-KHULSUM

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

MALAM SULE LAMIDO:  Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

September 15, 2026
ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya

ADO GWANJA – Ya Samu Lafiya

September 13, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.