• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, July 27, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

- Shugaban Ƙungiyar Likitocin Najeriya

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
May 9, 2026
in Babban Labari
0
Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

Farfesa Omoti, Shugaban Ƙungiyar Likitocin Najeriya

9
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

“Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi”

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

July 15, 2026
Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

July 11, 2026
Farfesa Omoti, Shugaban Ƙungiyar Likitocin Najeriya

__________
Shugaban Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya (NMA), Farfesa Afekhide Ernest Omoti, ya bayyana cewa mafi yawa daga cikin asibitocin da ke dukkan faɗin Najeriya, ba su da inganci, ta yadda ba su dace a kira su da wurin da ake jinyar ‘yan Adam ba. Ya ƙara da cewa, mafi yawan asibitocin ba su da bambanci da turakun dabbobi.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Farfesa Omoti ya ce: “A wasu asibitoci, likitoci suna aiki a ɗakunan da ba su ma dace da turakun da ake kiwon dabbobi ba. Duk da haka ake sa ran su yi aiki yadda ya kamata.”

Farfesa Omoti, wanda ƙwararren likita ne a fannin Ilimin Ido (Ophthalmology) kuma Babban Likita Mai Ba da Shawara (Honorary Consultant) a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin (UBTH), an zaɓe shi ne a matsayin sabon Shugaban Ƙungiyar Likitoci ta Najeriya a yayin Babban Taron Ƙungiyar na Shekara karo na 66, wanda aka gudanar a Kano. Ya samu ƙuri’u 253, inda ya kayar da Dokta Nosa Lancy Orhue, wanda ya samu ƙuri’u 143.

A yayin da yake ci gaba da zayyano matsalolin da ke fuskantar al’amuran lafiya a Najeriya, a taron manema labarai, Omoti ya yi gargaɗin cewa taɓarɓarewar yanayin aiki, haɗe da rashin kulawa da jin daɗi da walwala, suna ƙara ingiza ficewar ƙwararrun likitoci daga ƙasar nan.

“Ƙasarmu na cikin matsala. Babu isassun likitoci. Kaɗan daga cikin waɗanda suka rage, kowane likita ɗaya yana yin aikin da ya kamata likitoci kusan goma su yi,” in ji shi.

Sabon shugaban likitocin ya danganta wannan ƙaura ta ƙwararrun likitoci daga ƙasar nan saboda ƙarancin albashi da kuma rashin ingantattun kayan aiki, rashin ingancin yanayin aiki da sauransu. Yana mai cewa likitocin Najeriya na daga cikin mafi ƙarancin albashi a duniya.

“Babu wani likita da ya cancanci a biya shi ƙaramin albashin da ake ba shi a Najeriya, a ɗora masa haraji mai yawa, a jibga masa tarin aiki fiye da ƙima, sannan a saka shi cikin yanayin rashin tsaro da kuma rashin kayan aiki. Lokaci ya yi da za a sauya wannan yanayi,” in ji shi.

Haka kuma, babban likitan ya soki ƙarancin kuɗaɗen da ake ware wa ɓangaren lafiya. Yana mai jaddada cewa Najeriya ba ta cika muradun da Yarjejeniyar Abuja ta gindaya na ware kaso 15 cikin 100 ga harkar lafiya a ƙasa.

“A halin yanzu Najeriya na ware tsakanin kashi 4 zuwa 6 cikin 100 ne kawai ga lafiya. Idan muka matsa kusa da kaso 15, za mu fara ganin ci gaba a kayayyakin aiki da kuma ingantuwar aiki,” a cewarsa.

Ya kuma bayyana cewa likitoci da dama suna aiki na tsawon sa’o’i ba tare da isasshen hutu, tsari mai kyau na abinci ko tallafin hukumomi ba.

Game da yiwuwar shiga yajin aiki kuwa, Omoti ya ce ƙungiyar za ta fi mayar da hankali kan tattaunawa amma ba za ta kawar da yiwuwar yajin aiki ba idan gwamnati ta kasa ɗaukar matakan da suka dace. “Idan gwamnati ba ta yi abin da ya dace ba, za a shiga yajin aiki. Za mu fara da tattaunawa amma za mu ɗauki duk matakin da ya dace,” kamar yadda ya yi gargaɗi.

Ƙungiyar ta Likitocin Najeriya ta buƙaci a inganta wa ‘ya’yanta albashi, a samar masu da yanayin aiki mai kyau da kuma alawus-alawus marar haraji. Tana mai bayyana likitoci a matsayin masu bayar da muhimman gudunmawa ga al’umma. Haka kuma ta buƙaci a aiwatar da cikakken tsarin albashin likitoci a dukkan matakan gwamnati.

Taron na likitoci ya gudana ne a Kano daga ranar 26 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu, inda kuma suka zaɓi sababbin shugabannin da za su jagoranci ƙungiyar zuwa shekarar 2028. Cikinsu har da Dokta Abayomi Oluseye Olajide a matsayin Sakataren Kuɗi da Farfesa Olayinka Atilola, a matsayin Sakataren Yaɗa Labarai da Farfesa Anas Ismail a matsayin Babban Edita.
__________

Previous Post

Yan ta’addan Daji Kafirai Ne – Sarkin Musulmi

Next Post

Malumfashi An Yi Babban Rashi

Related Posts

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista
Babban Labari

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

July 15, 2026
Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo
Babban Labari

Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

July 11, 2026
ACF Endowment Fund Sets Agenda for Transparency, Education and Empowerment in Northern Nigeria
Babban Labari

Asusun Tallafi na ACF Ya Tsara Sabuwar Hanyar Bunƙasa Ilimi da Ƙarfafa Al’ummar Arewa

June 25, 2026
Next Post
Malumfashi An Yi Babban Rashi

Malumfashi An Yi Babban Rashi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (4)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (4)

January 2, 2026
Ɗalibi Ɗan Najeriya Ya Mutu A Yayin Faɗa A Amurka

Ɗalibi Ɗan Najeriya Ya Mutu A Yayin Faɗa A Amurka

June 29, 2023
Abdulkadir Nasir is the New CoS to Katsina State Governor

Abdulkadir Nasir is the New CoS to Katsina State Governor

December 12, 2024
A MESSAGE TO THE AREWA SOCIAL MEDIA INFLUENCERS

A MESSAGE TO THE AREWA SOCIAL MEDIA INFLUENCERS

August 2, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today
  • Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
  • Saƙon Godiya Da Bangajiya

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

July 25, 2026
Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.