SHARHIN LITTAFI:
Yadda Za A Farfaɗo Da Martabar Najeriya
Daga Dokta Bukar Usman, OON
~~~~~~~
Sunan Littafi: Rebooting Nigeria: Nigeria 2.0
Marubuta: Farfesa Andrew Haruna Da Emmanuel Dandaura.
Kamfanin Wallafa: Nigerian Institute of Public Relations.
Shekarar Wallafa: 2023
Yawan Shafukan: 164
Mai Sharhi Bukar Usman
~~~~~~~~

Wannan littafi mai ɗauke da shafuka 164, da muke wa sharhi a yau, mai taken “Rebooting Nigeria: Nigeria 2.0” (Hikimomin Yadda Za A Farfaɗo Da Najeriya), ya samu ne daga rahoton sakamakon taron ƙasa-da-ƙasa dangane da Ci Gaban Ƙasa, Zaman Lafiya Da Samar Da Tsaro, wanda aka gudanar a Zauren Taro Na Ƙasa-Da-Ƙasa da ke Abuja; a ranar 23 zuwa 24 ga Agusta, 2023. Littafin yana ƙunshe ne da sakamako da sharhin dukkan abubuwan da aka tattauna, tare da shawarwari kan muhimman jigoginsu, waɗanda suka haɗa da:
Batu kan Matasa, Martaba, Mulki, Gasa Tsakanin Ƙasashen Duniya, Ƙungiyoyin Tallafa Wa Al’umma, Haɗin Kan Ƙasa, Harkar Ilimi, Yanayin Sadarwa, Muhimman Darajojin Ƙasa, Al’adun Gargajiya, Ƙalubalen Tsaro, Tattalin Arziƙin Ƙasa, ‘Yan Najeriya Mazauna Ƙasashen Waje da kuma batun Gine-Ginen Inganta Rayuwa.
Babu shakka, abin yabawa ne yadda Cibiyar Koyar Da Hikimar Yaɗa Manufofi Ga Al’umma Ta Najeriya (NIPR) ta shirya wannan taro na masana, wanda ya tattara ra’ayoyi a matakin shiyyoyi, ya haɗa har ma da na ‘yan ƙasar waje, inda kuma a matakin ƙasa, ya tattara na ƙungiyoyi 93 da na ‘yan Najeriya; dangane da abubuwan da suke addabar al’ummar Najeriya, ƙasar da ke da mabambantan al’amura da al’adu da addinai da sauransu.
Babu shakka waɗannan bambance-bambance sun taimaka wajen ƙarfafa mana ta wani ɓangaren, kamar kuma yadda suka taimaka wajen haifar da rikici da gaba da neman laifukan juna a ɗaya ɓangaren. Lallai ya kamata mu natsu, mu gyara halayenmu, domin mu samu ci gaba.
Kamar yadda wani ɓangaren rahoton taron ya bayyana, duk da cewa Najeriya ba ta kai inda ya kamata ta kai ba, sai dai ‘yan Najeriya da dama har yanzu suna da yaƙini da zaman ƙasar na tarayya, don haka aikin sake gina ta da farfaɗo da ita, aiki ne na kowa da kowa a tare (shafi na 103).
Bari mu duba wasu muhimman bayanai da rahoton bayan taron yake ƙunshe da su:
…ƙara faɗaɗa gaba da rashin aminci da juna a tsakanin ‘yan ƙasa, amfani da shugabanci wajen rarraba kan al’umma, haifar da ruɗani da rikice-rikice tsakanin ƙabilu da jam’iyyun siyasa… (shafi na 01).
…ɗa’a, mutunci, mutunta aiki ko sana’a, adalci, mutunta addinan juna, dogaro da kai da kishin ƙasa, su ne muhimman tubalan gina ƙasa. Sai dai kuma da dama daga cikin ‘yan ƙasa ba su mallake su ba… (shafi na 08).
…a inganta hanyoyin sarrafa ma’adinai da hanyoyin sana’o’i, domin samar da kuɗin shiga… (shafi na 12).
…ƙalubalen rashin tsaro, almundahana da ha’inci, rashin kyakkyawan yanayin samar da kamfanoni da masana’antu da kuma tsare-tsaren gwamnati marasa tabbas da ɗorewa… (shafi na 24).
…rashin aiki ga ‘yan bokon matasa majiya ƙarfi, da gazawar su wajen koyon aikin hannu ko sana’a ko su dogara da kansu… (shafi na 24).
A wannan zamanin, mutane ba su cika sakin jiki suna tafiye-tafiye cikin ‘yanci da walwala, musamman ta hanyoyin mota, zuwa sassan ƙasar nan ba… (shafi na 29).
…rashin aminci daga al’umma ga jami’an tsaro da hukumomin yaƙi da almundahana da kallon gazawa da ake masu na rashin gurfanar da masu laifi gaban shari’a, domin su fuskanci hukunci… (shafi na 29).
… wasu daga cikin abubuwan da ke haifar da rashin aminci tsakanin gwamnatoci na kowane mataki da al’umma sun haɗa da:
Rashin cika alƙawura daga ‘yan siyasa, munanan sace-sacen dukiyar gwamnati, taɓargaza, karan tsaye da cin zarafin martabar mulki daga ‘yan siyasa da manyan jami’an gwamnati; rashin samar da kayan more rayuwa da romon dimokuraɗiyya bisa ga al’umma bai ɗaya bisa daidaito.
Sauran sun haɗa da ƙalubalen rashin tsaro da ya ƙi ci kuma ya ƙi cinyewa, taɓarɓarewar samar da ayyukan more rayuwa daga gwamnati da jami’anta, lalatattun gine-ginen gwamnati, kamar makarantu da hanyoyi da makamantansu. Rashin daraja bukatun al’umma daga shugabanni ‘yan siyasa… (shafi na 36).
…mafi yawa daga Ƙungiyoyin Tallafa wa Al’umma a Najeriya (CSOs – Civil Society Organizations), ƙasashen waje ne ke tallafa masu da kuɗin gudanarwa, domin haka suna yin biyayya ga umurnin iyayen gidansu da ke ɗaukar nauyin ɗawainiyarsu… (shafi na 47).
Yadda ake samar da bayanai ga al’umma yana shafar yadda al’umma ke amsar shi…(shafi na 68).
Al’adu da ɗabi’un al’umma da addininsu, su ne ke samar da martaba da ƙimar ƙasa a idanun duniya (shafi na 69).
Kyakkyawan ƙudiri ya zuwa samar da sabuwar Najeriya, ya rataya ne ga kyakkyawan shugabanci da kyawawan mabiya (shafi na 72).
….ya kamata a samar da shugabancin gargajiya ga sababbin wuraren da ke ƙamfar hukumomi a Najeriya (shafi na 74).
…yin amfani da adadin kuɗi mai yawa daga ƙalilan ɗin albarkatun ƙasa da ake samu, da nufin kare martabar ƙasa…yana shafar sauran sassan tattalin arzikin ƙasa mai karsashi (shafi na 78).
Tsare-tsaren gwamnati na tabbatar da haɗin kan ƙasa da ake tafiyarwa na tsawon sama da shekara 50 sun taimaka sosai wajen samar da wani adadi na haɗin kai da fahimtar juna a Najeriya (shafi 81).
…yadda ake jirkita tsare-tsaren mulki har yanzu ya kasa samar da abin da ‘yan ƙasa da masu ruwa da tsaki ke tsammani (shafi na 85).
…tsarin gwamnatin shugaban ƙasa mai cikakken iko da muka aro muka yafa, ya haifar mana da matsalolin cunkoso a muƙamai da muhimmancinsu ke da ƙaranci (shafi na 86).
…al’ummu da dama a garuruwa da jihohi, ba su da hanyoyin sufuri…ga shi kuma suna fama da ƙarancin wutar lantarki…(shafi na 89).
Akwai matsalar samar da wadataccen abinci, a sakamakon rashin tsaro a wuraren da ake noma, domin samar da kayan abincin… (shafi na 89).
Rashin hanya mai sauki ta gudanar da sana’o’i, rashin hanyoyin sufuri, rashin wadatattar wutar lantarki da kuma hauhawar farashin mai sun haddasa mutuwar kamfanoni, suna barin Najeriya (shafi na 90).
‘Yan Najeriya da yawa suna zaune a ƙasashen waje da dama (shafi na 92).
…yanayin da ke ciki a Najeriya, dangane da siyasa, tattalin arziƙi da zamantakewar al’umma, shi ke taoratar da ‘yan Najeriya da ke zaune a wasu ƙasashen duniya daga dawowa gida domin zaman dindindin…(shafi na 93).
An riga an san manyan matsalolin da ke addabar ƙasar nan tun tsawon lokaci. Hanyoyin magance su ne ake jan ƙafa wajen samar da su. Dalili ke nan ake ta samun tashin hankali da yunƙurin neman biyan buƙatu daga al’umma. Ga wasu kaɗan daga cikin irin waɗannan manyan matsaloli:
Makamashi Da Wutar Lantarki:
Rashin gyara matatun mai kuma duk da cewa gwamnatin da ta shuɗe, ta ƙaddamar da Matatsar Mai ta Ɗangote cikin biki da ɗoki, har yanzu ana dogara ne da shigo da tataccen mai daga ƙasashen waje, duk kuwa da irin ɗimbin matsalolin da hakan ke haifarwa.
Akwai matsaloli sosai a ɓangaren wutar lantarki. Misali, Kamfanonin Samar Da Wutar Lantarki (GENCOs), suna fuskantar ƙamfar iskar gas da za ta wadaci injinansu. Haka kuma babu wadatattun layukan da za su ɗauki wutar lantarkin da ake buƙata. Ta fuskar Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki (DISCOs) kuwa, su ma suna da nasu matsalolin. Misali, da dama daga cikinsu basussukan banki sun yi masu yawa, ta yadda wasu bankunan ma sun amshe kadarorinsu. Waɗannan matsaloli sun sanya kamfanonin na rarraba lantarki, ba su iya wadatar da al’umma da wadatattar wutar lantarki. Dalili ke nan wannan babbar matsala ta ƙarancin lantarki ta gagari Kundila.
Masana’antar Tama Da Ƙarafa:
Babban ƙashin bayan tattalin arziƙin ƙasa ya rataya ne ga bunƙasassun masana’antun tama da ƙarafa. Tun sama da shekara 40 da ta gabata da aka samar da kamfanonin sarrafa ƙarafa na Ajaokuta da takwarorinsa na Jos, Katsina, Oshogbo da Aladja amma har yanzu sun kasa taka rawar gaban hantsi saboda wasu dalilai marasa makama. Haka ma al’amarin yake, idan aka zo batun kamfanin sarrafa alminiyum da ke garin Ikot Abasi. Bare kuma a ambato batun Kamfanin Ƙera Makamai na Najeriya (DICON), wanda ya kasance kwan-gaba-kwan-baya.
Harkokin Sufuri:
Gyaran hanyoyin jirgin ƙasa ya tsaya cik, don haka babu batun faɗaɗa samar da wasu. Kamfanin Safarar Jiragen Sama (Air Nigeria) da aka ƙaddamar cikin shagulgulan biki a lokacin ganiyar mulkin gwamnatin da ta shuɗe, ya zuwa yanzu ya sargafe da gutsuri-tsoma. Ta ɓangaren sufurin ruwa kuwa, babu inda za ka samu ingantacce, abin dogara, da za ka yi alfahari da shi. Babu wani tsarin safarar motoci ingantacce, duk kuwa da yawan al’umma da ke akwai a ƙasar nan.
Al’amuran Kuɗaɗen Waje:
A yayin da aka cire tallafin man fetur, ana kyautata zaton gwamnati ta samu kuɗi mai yawa a Naira. Sai dai kuma babbar matsalar ita ce, ƙarancin kuɗin waje da za su sauƙaƙa cinikayya da ƙasashen duniya, musamman yadda darajar Naira za ta samu ƙimar da ta dace da kuɗin Najeriya da ke ajiye a Asusun Ko-ta-kwana na ƙasashen waje. Haka kuma ga matsalar bashin ƙasashen waje mai yawa, alhalin kuma adadin yawan ɗanyen man da ake haƙowa ya yi ƙasa, wanda da shi ake dogara wajen samun kuɗin shiga. Babu tabbacin adadin zai ƙaru a nan da ɗan lokaci gaba (saboda rikice-rikice da sauran matsalolin da ke faruwa a yankunan da ake haƙo shi), balle a ce za a samu ƙarin kuɗi daga gare shi.
Al’amuran Noma:
Nan ma an samu matsala a bana, domin kuwa ruwan sama ya yi jinkirin sauka a sassa daban-daban na ƙasar nan. Haka kuma akwai matsalar rashin tsaro da ke addabar sassa da yawa na yankunan da ake nomawa. Mutane da yawa suna kokawa, yadda suke gaza zuwa gonakinsu, a sakamakon rashin tsaro.
Matsalolin Rayuwa:
Gwamnati ta yi yekuwar samar da tsarin bayar da rancen kuɗi ga ɗaliban da ke da ƙaramin ƙarfi. Sai dai kuma tun daga lokacin zuwa yanzu, watanni da dama sun shuɗe, ba tare da an ga batun ya kankama ba. Ga shi yanzu wasu ɗaliban suna ta haƙilon barar kuɗi daga attajirai, domin su iya biyan kuɗin rijistar makarantun da suke karatu.
Ga shi farashin kayan masarufi na ta hauhawa, haka ma farashin wutar lantarki, balle kuma farashin man fetur da ya ninka sau uku. Matsalolin sun yi yawa, kuma babu taƙamaimai na tabbacin lokacin da farashin zai sauko.
Babu shakka, abin da mutane suka nuna dangane da tsare-tsaren gwamnati a yau, shi ne mizanin tantance gamsuwa ko akasin gamsuwa da gwamnatin. Sai dai kuma mafi yawan mutane suna kokawa da nuna rashin gamsuwa da waɗannan matakai na gwamnati.
Wannan mataki da shugabannin Cibiyar Koyar Da Hikimar Yaɗa Manufofi Ga Al’umma Ta Najeriya (NIPR) suka ɗauka, na gabatar da rahoton ga masu ruwa da tsaki (shafi na 100), al’amari ne da yake kan hanya kuma ya dace a ƙara ƙaimi domin ganin an cin ma nasarar tabbatar da shi. A kan haka, abu ne mai kyau ga shugabannin na cibiyar ta NIPR su tattauna kan muhimman al’amuran da rahoton sakamakon taron ya samar, domin mayar da hankali a kan su, a tuntuɓa, domin ganin an cin ma gamsasshiyar nasara.
Cibiyar NIPR dai ta ɗaura ɗanba da ta samar da wannan taro na farko. Don haka taro na gaba sai ya ɗora kan na farko, a maida hankali wajen bijiyar nasarar da aka samu na ɗabbaƙa muhimman shawarwarin rahoton baya. Sai dai kuma ya kamata cibiyar ta riƙa bin komai a hankali, ta guje wa yin shifcin gizo.
~~~~~~~
Dokta Bukar Usman, OON, marubuci, masanin tsaro, tsohon Babban-Sakatare a Fadar Shugaban Ƙasa, ya rubuto sharhin nan daga Abuja a ranar 20 ga Satumba, 2023.
~~~~~~~













