• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, August 14, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Jami’ar Bayero Ta Karrama Janar Buratai

Shi Kuma Ya Ba Jami'ar Kyautar Littafin Tarihinsa

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
December 16, 2023
in Babban Labari
0
Jami’ar Bayero Ta Karrama Janar Buratai
98
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Jami’ar Bayero Ta Karrama Janar Buratai

Shi Kuma Ya Ba Jami’ar Kyautar Littafin Tarihinsa

Related posts

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

August 12, 2026
Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

July 31, 2026

Jami’ar Bayero Kano ta karrama Laftanar-Janar Tukur Yusufu Buratai, CFR (mai ritaya) da Kambin Girmamawa, a matsayinsa na ɗaya daga cikin jakadun Najeriya da suka kare martabar ƙasarsu a ƙasashen waje.

Janar Buratai, wanda shi ne tsohon Hafsan-Hafsoshin Rundunar Sojojin Najeriya kuma tsohon Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Betaran Biu kuma Garkuwan Keffi, an karrama shi ne a yayin taron ƙara wa juna ilimi da Tsangayar Nazarin Jinsuna) (Center For Gender Studies) da ke Jami’ar Bayero Kano ta shirya.

Taron na kwana biyu, mai taken “Inganta Ilimin Matasa Domin Samun Kyakkyawar Rayuwa” ya gudana ne a jiya Juma’a (15-12-2023) a babban zauren taro na jami’ar da misalin ƙarfe goma na safe. Kuma an karrama shi ne bisa la’akari da irin gudunmowar da yake bai wa al’umma, musamman matasa maza da mata, domin inganta rayuwarsu.

A yayin gabatar da jawabinsa, Betaran Biu, ya miƙa godiyarsa ta musamman ga wannan tsangaya da ta shirya taron. Haka kuma ya yaba mata, bisa himmarta wajen horar da ƙwararrun mutane kuma ingattatu a fannoni daban-daban, domin samar da kyakkyawan ci gaba ga kansu da ƙasarsu baki ɗaya.

Haka kuma ya yi jinjina ga masanin Shari’a, Farfesa Auwalu Yadudu, wanda ya ce abokinsa ne mai ƙwazon yi wa al’umma hidima.

“Wajibi ne in miƙa godiya ta musamman ga abokina, wanda duk da cewa ya yi ritaya amma ba ya gajiya wajen yi wa al’umma hidima. Ga shi kuma ya halarci wannan taro. Muna ƙara yi maka barka da zuwa,” in ji Janar Buratai.

Haka kuma, bayan an karrama Garkuwan na Keffi da Kambin Girmamawa, shi kuma ya bai wa Sashin Nazarin Harsuna na Jami’ar ta Bayero kyautar littafin tarihin rayuwarsa da gwagwarmayarsa, mai taken HIKIYAR JARUMI BURATAI) na 1 da na 2, wanda Malam Bashir Yahuza Malumfashi ya wallafa kuma ake shirin ƙaddamarwa nan gaba.

Yayin da yake miƙa littattafan ga Shugaban Jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, Janar Buratai ya ce, “wannan na daga kaɗan daga gudunmowar da muke son bayarwa wajen bunƙasa harsunan gida, ta yadda cibiyar za ta ƙara haɓaka tare da gogar da matasa musamman a ɓangarori daban-daban, ta yadda za a kawo ci gaban ƙasa a harkokin tsaro da samar da ingantaccen ilimi, wanda kuma shi ne babban ƙalubale.”

Ya ƙara da cewa, “tun jiya ina cikin garin Kano. Na ga yadda suke da ɗimbin matasa da ke bisa hanyoyi. Na lura da cewa akwai ƙalubale a ɓangaren tattalin arziki saboda haka waɗannan matasa ku da kuka samu wannan horo, ku jajirce wajan tsamo ‘yan uwanku daga matsalolin rayuwa.

“Ina taya ku murna da kuka samu wannan ilimi. A ƙarshe, ina fatan idan kun fita daga wannan makaranta, za ku yi ƙoƙarin ɗabbaƙa abun da kuka koya a aikace. Ina gode muku baki ɗaya da dukkanin mahalarta.

Taron ya samu halartar manyan malamai da jami’an gwamnati masu ci da tsofaffi

Janar Buratai, a yayin jawabin godiya
Shugaban Jami’ar Bayero, yana amsar littattafai daga hannun Janar Buratai

bisa shugabancin Farfesa Sagir Adamu Abbas, Shugaban Jami’ar Bayero da Farfesa Ruƙayya Ahmad Rufa’i, tsohuwar Ministar Ilimi da Dokta Suwaiba Sa’id Daraktar Tsangayar Nazarin Jinsuna ta jami’ar (CGS). Akwai kuma Alhaji Ahmad Rabi’u Ahmad da Dokta Manzo Ahmad.

Sauran sun haɗa da Farfesa Auwalu Yadudu da Farfesa Muhammad Yahuza Bello da Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa, Shugaban Jami’ar Yusuf Maitama Sule da Alhaji Adamu Muhammad Buratai da sauransu da dama daga sassa daban-daban na ƙasar nan.

Previous Post

Minista Hannatu Musawa Ta Ƙudiri Aniyar Kafa Gidan Tarihi Da Na Wasanni Na Ƙasa A Abuja

Next Post

Gwamnatina Za Ta Mutunta ‘Yancin Kafafen Yaɗa Labarai

Related Posts

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara
Babban Labari

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

August 12, 2026
Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami
Babban Labari

Rarara Ya Ƙara Haska Farin Jinin Sheikh Pantami

July 31, 2026
Janar Buratai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne – Oba Adekunle Makama
Babban Labari

Janar Buratai Babban Ɗan Kishin Ƙasa Ne – Oba Adekunle Makama

July 30, 2026
Next Post
Gwamnatina Za Ta Mutunta ‘Yancin Kafafen Yaɗa Labarai

Gwamnatina Za Ta Mutunta 'Yancin Kafafen Yaɗa Labarai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

YUSUFARI EMIRATE COUNCIL CONFERS TRADITIONAL TITLES TO LIEUTENANT GENERAL TY BURATAI (RTD) CFR, ENGINEER HASSAN MUHAMMAD AND OTHERS

YUSUFARI EMIRATE COUNCIL CONFERS TRADITIONAL TITLES TO LIEUTENANT GENERAL TY BURATAI (RTD) CFR, ENGINEER HASSAN MUHAMMAD AND OTHERS

January 1, 2024
Janar Magashi Bai Mutu Ba

Janar Magashi Bai Mutu Ba

June 24, 2023
Musulmin Kudancin Najeriya Sun Jaddada Mubaya’a Ga Sarkin Musulmi

Musulmin Kudancin Najeriya Sun Jaddada Mubaya’a Ga Sarkin Musulmi

February 13, 2026
Lassa: A Different History

Lassa: A Different History

June 29, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Our Daily Message
  • Regulation, Standardisation of Qur’anic Schools Under Way in Katsina
  • Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Our Daily Message

Our Daily Message

August 14, 2026
Regulation, Standardisation of Qur’anic Schools Under Way in Katsina

Regulation, Standardisation of Qur’anic Schools Under Way in Katsina

August 13, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.