• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, May 25, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

KISAN MAWAƘI MOHBAD: Darasi Da Jan Hankali G Al’ummar Arewa

Yusuf Dingyaɗi by Yusuf Dingyaɗi
September 22, 2023
in Gizago
0
KISAN MAWAƘI MOHBAD: Darasi Da Jan Hankali G Al’ummar Arewa
63
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

KISAN MAWAƘI MOHBAD: Darasi Da Jan Hankali G Al’ummar Arewa

Daga Yusuf Dingyaɗi

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026

~~~~~~~
Yanzu ‘yan Arewa suna kallon yadda wani ɓangaren al’umma na Najeriya suka haɗu a cikin abin da bai fi kwanaki uku suna zanga-zanga tare da haɗin kai don neman tilasta wa mahukunta da sai sun yi bincike da hukunta masu hannu a kan kisan ɗan rawa kuma mawaƙi, Ilerioluwa Aloba, wanda aka fi sani da Mobad, wnda ake zargin ya rasa ransa a kwanan nan ta hanyar kisan gilla.

Mutum ɗaya ne waɗannan ɗaruruwan mutane daga Legas, Oyo, Ekiti, Osun da Ingila suka haɗu suna neman haƙƙinsa, a ƙasar da a kullum ake bayyana akwai alƙalluman da suke bayanin sai an kashe fiye da rayuka 40 zuwa 50 ko harin ta’addanci ko na kisan gilla ko ganganci na hatsarin mota ko shan ƙwayoyi da sauransu.

AREWA, mussaman Arewa Maso Yamma, a jihohin Sakkwato, Kebbi, Zamfara, Katsina da Neja da Kaduna, kusan kullum an yi zargin sai an yi kisan gilla na ganganci ko a wajen ‘yan ta’adda ko masu amfani da hanyoyin ramuwar gayya da sauran irinsu, fiye da ko’ina a cikin ƙasar nan.

Zubar da jini da kisan jama’a da sace dukiyoyinsu a yankin Arewa ta Yamma ya zama abin da ke faruwa a kullum.

Shin har yaushe za mu iya fitowa fili mu jagoranci juna don aika irin wannan saƙon ga mahukunta dangane da matsalar tsaro da kisan gillar da ake yi wa al’ummarmu a birane da karkara?

Yankunan karkara a jihohin Sakkwato, Zamfara, Katsina, Kaduna, Neja da Kebbi kusan kullum sai an kashe ko yin garkuwa ko satar dabbobi ko kisan gilla a cikinsu.

Har yaushe zamu aje siyasa, son kai da ƙin juna mu haɗu a Arewa a tare, mu yi wa kanmu da jama’armu mafita dangane da bayyana koke-kokenmu a fili, gaban duniya don fatan samun nasara, har mahukunta nan su juyo don bai wa lamarin matakin da ya dace?

Ba wani babba a Abuja ko a fadar gwamnati da zai iya ɗaukar wani matakin da zai kai na muryar jama’a mai ƙarfi.

A tashi tsaye a tare da yi wa juna uzuri da mayar da hankali ga yaƙar wannan lamarin, ba tare da tsoro ko shakka ko kwaɗayi a kan makomar da za ta zama a kan wannan lamarin ba.

Dole mu yi kishin ƙasa da son juna da yi wa juna uzuri tare da haɗin kai da adalci kan samar da makoma ne kawai mafita a nan gaba.

Addu’oi da neman da muke Allah Ya kawo mana sauƙi, zai zo muddin muka gyara da juna, muka aje siyasa da hassada da cin amana da rashin gaskiya don fuskantar wannan matsalar a cikin haɗin kai.

‘Yan AREWA, mu koyi darasi da haɗin kai don kuwa tafiya ta fara nisa; kusan duk waɗanda suka dace su yi mana magani, tasu fitinar ta ishe su!

ALLAH ga Arewa da ‘yan Arewa. Muna fatan mafita!

~~~~~~~
Yusuf Dingyaɗi, ɗan jarida, marubuci,ɗan siyasa, ya rubuto taokacin nan Sakkwato!
~~~~~~~

Previous Post

Gen. SK Usman Now a Distinguished Knight for World Peace

Next Post

ALMAJIRCI: An Yaba Da Halayyar Farfesa Pantami

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
ALMAJIRCI: An Yaba Da Halayyar Farfesa Pantami

ALMAJIRCI: An Yaba Da Halayyar Farfesa Pantami

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Ali Nuhu Ya Shiga Rukunin Fitattun Taurarin Fim 100 Na Afirka

Ali Nuhu Ya Shiga Rukunin Fitattun Taurarin Fim 100 Na Afirka

July 9, 2023
THE MAN B. Y. M.

THE MAN B. Y. M.

June 28, 2024
RAMADAN KARIM: 23-1447

RAMADAN KARIM: 23-1447

March 12, 2026
KANNYWOOD JIYA DA YAU: DARASIN RAYUWA DAGA WASU TAURARI (1)

KANNYWOOD JIYA DA YAU: DARASIN RAYUWA DAGA WASU TAURARI (1)

August 3, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • POSITIVE COMRADE
  • BUKAR USMAN: The Human Library
  • Sule Lamido’s Theme of Authenticity

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

POSITIVE COMRADE

POSITIVE COMRADE

May 20, 2026
BUKAR USMAN: The Human Library

BUKAR USMAN: The Human Library

May 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.