• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, October 11, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

INEC Za Ta Gudanar Da Zaɓuɓɓukan Da Kotu Ta Soke Da Na Cike Gurabu 34 A Fabrairu 2024 – Yakubu

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
December 20, 2023
in Labarai
0
Zaɓen gwamna: Mutum 2,318,919 za su yi zaɓe a Imo, 1,833,160 a Kogi, 1,017,613 a Bayelsa, inji INEC

Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Mahmud Yakubu

15
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

INEC za ta gudanar da zaɓuɓɓukan da kotu ta soke da na cike gurabu 34 cikin Fabrairu 2024 – Yakubu ko

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa mai yiwuwa a satin farko na Fabrairu, 2024 za ta gudanar da ragowar zaɓuɓɓukan da za a sake da kuma na cike gurabun a wasu mazaɓu, yankuna da shiyyoyin tarayya da jihohi.

Related posts

Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro

Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro

September 26, 2026
Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026

Shugaban hukumar, Farfasa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a taron da INEC ta yi da jam’iyyu ranar Litinin, a Abuja.

Yakubu ya ce INEC ta ɗaura aniyar gudanar da zaɓuɓɓukan biyu, wato zaɓukan da za a sake da kuma waɗanda ba a samu gudanarwa ba duk a rana ɗaya. Wato ya na nufin har da zaɓukan cike gurabu kenan.

Ya ƙara da cewa yayin da aka kafa Kotunan Sauraren Ƙararrakin Zaɓe bayan kammala zaɓen 2023, to yanzu dai za a ce sun kusa kammala zaman su.

“Abin da ya rage shi ne hukumar zaɓe ta gudanar da zaɓuɓɓukan da kotuna suka bada umarnin a sake a wuraren da za a sake zaɓuɓɓukan.

Yakubu ya ce INEC za ta kuma gudanar da zaɓuɓɓukan cike gurabun waɗanda suka mutu, ko waɗanda suka ajiye muƙaman da aka zaɓe su a kai a Majalisar Ƙasa ko Majalisar Jihohi.

“Kamar yadda ku ka sani, shi zaɓe na ‘re-run’, zaɓe ne da ya ƙunshi jam’iyyu da ‘yan takara waɗanda suka rigaya suka fafata a babban zaɓe. Sai fa idan jam’iyya na buƙatar musanya ɗan takara idan ya rasu kafin a sake wannan zaɓen da za a yi.

“Shi kuma ‘bye-election’, zaɓe ne sabo da za a yi. Don haka a wannan tsari, tilas ne jam’iyyu su sake gudanar da zaɓen fidda gwanaye cikin ƙa’idar kwanakin da dokar zaɓe ta gindaya.

“Zuwa yanzu dai Kotunan Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓe sun umarci INEC ta gudanar da zaɓuɓɓuka a mazaɓu 34 da suka ƙunshi shiyyar sanata ɗaya, sai mazaɓun ɗan majalisar tarayya guda 11 da majalisun jihohi 22.

“Sai dai kuma daga zaɓuɓɓuka 34 ɗin da za a sake, guda wurare uku ne kawai za a sake zaɓen baki ɗaya.”

A ƙarshe Yakubu ya ce sai bayan an kammala sauraren shari’un zaɓen gwamnoni a kotunan tarayya da Kotun Ƙoli, sannan hukumar sa za ta tattara yawan shari’un da aka gudanar, domin yin bayanin su dalla-dalla.

Previous Post

Gwamnatina Za Ta Mutunta ‘Yancin Kafafen Yaɗa Labarai

Next Post

Kafafen Yaɗa Labarai Su Ne Manyan Dirkokin Da Ke Ɗauke Da Nagartacciyar Dimokiraɗiyyarmu – Minista

Related Posts

Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro
Labarai

Janar S.K. Usman Ya Zama Dakta A Fannin Nazarin Tsaro

September 26, 2026
Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin
Labarai

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda
Labarai

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026
Next Post
Kafafen Yaɗa Labarai Su Ne Manyan Dirkokin Da Ke Ɗauke Da Nagartacciyar Dimokiraɗiyyarmu – Minista

Kafafen Yaɗa Labarai Su Ne Manyan Dirkokin Da Ke Ɗauke Da Nagartacciyar Dimokiraɗiyyarmu - Minista

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Gombe 2027: Kotu Ta Soke Takarar Pantami…

Gombe 2027: Kotu Ta Soke Takarar Pantami…

September 24, 2026
TSOKACINMU NA YAU (13)

TSOKACINMU NA YAU (13)

March 13, 2025
Taya Ni Mu Gyara: Kisan Baƙi Sai Gayya

Taya Ni Mu Gyara: Kisan Baƙi Sai Gayya

November 1, 2025
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Kwamishina Ɗahiru Ya Harzuƙa Maryam Jan Kunne
  • NASIHARMU TA YAU (18)
  • Rikici Ya Kacame Tsakanin Moofy Da Tage A Kan Pantami

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Kwamishina Ɗahiru Ya Harzuƙa Maryam Jan Kunne

Kwamishina Ɗahiru Ya Harzuƙa Maryam Jan Kunne

October 11, 2026
NASIHARMU TA YAU (18)

NASIHARMU TA YAU (18)

October 11, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.