• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, April 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Sarauta

Janar Faruk Yahaya Ya Zama Zaruman Sakkwato

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 15, 2023
in Sarauta
2
Janar Faruk Yahaya Ya Zama Zaruman Sakkwato

Zaruman Sakkwato Janar Faruk Yahaya, CFR, jim kaɗan da naɗinsa

103
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Janar Faruk Yahaya Ya Zama Zaruman Sakkwato

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, yana miƙa kyautar dokin alfarma ga Zaruman Sakkwato
A dama, Janar Tukur Yusufu Buratai ne, a zauren taron karrama Zaruman Sakkwato

A ranar Asabar da ta gabata (12-08-2023), Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Sa’adu Abubakar ya naɗa Laftanar-Janar Faruk Yahaya (mai ritaya), CFR, Sarautar Zaruman Sakkwato.

Related posts

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

October 26, 2025
Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

October 22, 2025

Bayan naɗin nasa, al’ummar Jihar Sakkwato sun shirya masa gagarumar daba, domin taya shi murnar kammala aikin soja lami lafiya, cikin gagarumar nasara. Janar Faruk ya kammala aikinsa na soja a ranar 23-06-2023, bayan ya kwashe kimanin shekara 37 a fagen aiki. Ya kammala aiki ne da muƙamin Laftanar-Janar, sannan kuma a matsayin Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Nigeria.

Da yake bayyana kyawawan halayensa sabon Zaruman Sakkwato, Babban Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojojin Nigeria, Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ya ce: “Shi mutum ne mai ƙana’a, jajirtacce, mai ƙaunar ƙasarsa ta haihuwa. A kullum idan yana bakin aiki, yakan nuna sadaukarwa da nuna ƙwazo da himma. Waɗannan kyawawan halaye nasa ne suka taimaka masa har ya cin ma ɗarewa ƙololuwar muƙami a Gidan Sojojin Nigeria, inda kuma ya zama Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Nigeria na 22.”

A yayin gagarumar dabar da aka shirya masa kuwa, Aal’ummar Jihar Sakkwato sun fito ƙwansu da kwarkwata. Manya da matasa, wasu a kan dawakai da raƙuma, wasu a kan motoci da babaura, wasu ma a ƙasa suka yi wa Babban Filin Wasanni na Sakkwato tsinke, ɗaliban makarantu daban-daban da makaɗa da mawaƙa suka gudanar da wasannin gargajiya domin karrama shi da yi masa barka da arziki.

Shugaban Kwamitin da ya shirya wannan gagarumar Daba, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, ya yaba sosai da halayen Janar Yahaya. Ya ce shi shahararren mutum ne kuma abin alfahari, a matsayinsa na ɗan Sakkwato mai mutunci, wanda ya bayar da gagarumar gudunmowa ga ƙasarsa ta haihuwa da kuma Gidan Sojan Nigeria.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Sakkwato, Dokta Ahmad Aliyu Sakkwato, ya bayyana Janar Faruk a matsayin mutum mai riƙon amana, wanda za a yi ƙishirwar gudunmowarsa a Gidan Sojan Nigeria.

Shi kuwa magajinsa, Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Nigeria, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, yaba wa Zaruman na Sakkwato ya yi, wanda ya ce shugabansa ne abin koyi a Gidan Soja. Ya ce ya bar babban gurbi mai wuyar cikewa a aikin soja. Ya ce ya bar babban tarihi da za a daɗe ana tunawa da shi a Gidan Soja.

Shi kuwa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji (Dokta) Sa’ad Abubakar III CFR, ya ƙimanta shi da Shahararren Janar, wanda ya taka rawa abin yabawa a fagen yaƙi, mulki da kuma aiki ga al’ummarsa.

Zaruman Sakkwato, Janar Faruk Yahaya, an haife shi a garin Sifawa na Karamar Hukumar Boɗinga. Yana auren Hajiya Salamatu Faruk, wadda ta haifa masa kyawawan ‘ya’ya kuma ta riƙe shi da soyayya da zumunci a matsayinta na Uwargida.

Wasu daga cikin hamshaƙan mutane da suka halarci gagarumar Dabar karrama Zaruman Sakkwato sun haɗa da tsohon Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Nigeria, Laftanar-Janar Tukur Yusufu Buratai, CFR (mai ritaya), Betaren Biu, da Birgediya-Janar Sani Usman Kukasheƙa, mni (mai ritaya), Sarkin Yaƙin Kanwan Katsina da tsohon Ministan Harkokin ‘Yan Sanda, Alhaji Maigari Dingyaɗi da tsohon Shugaban Rundunar Tsaro, Janar Lucky Irabor (mai ritaya) da sauransu.

Previous Post

PDP Ta Naɗa Yusuf Dingyaɗi Sabon Muƙami

Next Post

HAWAYE DON AFIRKA

Related Posts

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa
Sarauta

Galadiman Katsina Ya Karrama Ni Matuƙa – Waziri Shehu Musa

October 26, 2025
Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina
Sarauta

Alhaji Shehu Musa Ɗankano: Maraba Da Sabon Wazirin Galadiman Katsina

October 22, 2025
Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’
Sarauta

Betaran Biu Janar Buratai Ya Samu Sarautar ‘Baakoren Akure’

October 17, 2023
Next Post
HAWAYE DON AFIRKA

HAWAYE DON AFIRKA

Comments 2

  1. Idris Ibrahim Kubau says:
    3 years ago

    Allah Ya yi musu jagora Ya ba su ikon sauke nauyin da ke kansu. Shugabanci abu ne mai wahala duk da ya kai ƙololuwa a aikinsa na gwamnati.

    Reply
  2. Bashir Yahuza Malumfashi says:
    3 years ago

    Amin Amin Ya Allah. Babu shakka shugabanci babban al’amari ne.

    Reply

Leave a Reply to Idris Ibrahim Kubau Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

YADDA NA ƊAUKI SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA

YADDA NA ƊAUKI SHEIKH YAKUBU YAHAYA KATSINA

July 19, 2025
Da Albarkar Littafi Na Je Saudiyya – Sa’adatu Kankia

Da Albarkar Littafi Na Je Saudiyya – Sa’adatu Kankia

July 22, 2023
BIU: A Visit to a City on a Plateau (3)

BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (3)

December 23, 2023
Saura Ƙiris Kwankwaso Da Ganduje Su Dambace A Gaban Tinubu

Saura Ƙiris Kwankwaso Da Ganduje Su Dambace A Gaban Tinubu

June 10, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
  • Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye
  • Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.