• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, January 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Noma Da Kiwo

Buɗe Boda Ba Zai Durƙusar Da Mu Ba – Shugaban Ƙungiyar Makiyaya Kaji

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 24, 2023
in Noma Da Kiwo
0
Buɗe Boda Ba Zai Durƙusar Da Mu Ba – Shugaban Ƙungiyar Makiyaya Kaji

MK. Adam a bakin sana'arsa

56
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Buɗe Boda Ba Zai Durƙusar Da Mu Ba – Shugaban Ƙungiyar Makiyaya Kaji

MK. Adam Gombe, shi ne Shugaban Ƙungiyar Makiyaya Kaji A Jihar Gombe. A tattaunawarsa da Taskar Gizago, ya bayyana irin ci gaban da suke samu a ƙungiyance. Haka kuma ya bayyana cewa koda gwamnati ta buɗe boda, ba za su cutu ba a sana’arsu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Related posts

SHIRIN BUNƘASA NOMA NA ƘASA A JIHAR KATSINA (NATIONAL AGRICULTURAL COMMODITIES PROJECT KATSINA STATE) NA GAYYATA

SHIRIN BUNƘASA NOMA NA ƘASA A JIHAR KATSINA (NATIONAL AGRICULTURAL COMMODITIES PROJECT KATSINA STATE) NA GAYYATA

December 11, 2024
SANA’AR NOMA: Ya Dace Attajirai Su Tallafa Wa Matasan Arewa – Dokta Sharif Almuhajir

SANA’AR NOMA: Ya Dace Attajirai Su Tallafa Wa Matasan Arewa – Dokta Sharif Almuhajir

September 17, 2023

TG: A matsayinka na manomi, ko za ka gaya mana abubuwan da kake yi a noma da kiwo?

MK: Sunana, Muhammad Kabir Adamu Gombe.
Ni ne Shugaban Ƙungiyar Masu Kiwon Kaji ta Jihar Gombe (Gombe State Poultry Farmers Association). Muna kiwo da kasuwancin kajin nama (broilers) da kuma masu yin ƙwai (layers).

TG: Shekara nawa ke nan kake cikin harkar noma kuma waɗanne nasarori kake samu?

MK: Aƙalla na samu sama da shekara 18 ina kiwon kaji amma kasancewata a shugabanci bai wuce shekara uku ba. Alhamdu lillah, kiwon kaji yana da sirriku masu ɗimbin yawa,waɗanda sai ka shiga za ka san da su. Duk mai yin sana’ar nan ba zai rasa kuɗin kashewa ba Sai dai kamar yadda ka sani, kowace sana’a tana da nata irin ƙalubale. Mafi akasarin matsalar da ake samu ta fuskar sana’ar kiwon kaji, ita ce, ba a neman ilimin abin sai a shiga. Wasu gani suke ai kaza ba sai an nemi ilminta ba, kawai a ba ta abinci da ruwa shi ke nan. Sai kajin sun fara mutuwa a nan zai fahimci ashe ba haka lamarin yake ba.

TG: A matsayinka na manomi a Arewa, waɗanne matsaloli kake fuskanta kuma ta yaya kake ganin za a iya magance su?

MK: Babbar matsala ta farko ita ce kasuwa. Wato yadda mai kiwon kaji zai sayar a lokacin da ya tashi sayar da kajinsa saboda su kajin broilers suna da zango da ake fitar da su. Wato daga ranar da ka sayo su, a ranar za ka saka a ranka ga makwannin da za ka fitar da su. Wasu sati 4 wasu 5, 6, 7 har zuwa 8 kuma duk makwannin da ka ɗauka, in dai ya zo bak a da abincin mako na gaba, a nan hankalin makiyayi ke tashi. Sai ya yi tunanin hanyar da zai bi domin sayar da su. Da zaran ya nemi kasuwa ba a zo aka saya ba, to kajin nauyinsu zai fara komawa baya, domin ba ya da ƙarfin jarin da zai ci gaba da ciyar da su.

Hanyar da za a magance irin waɗannan matsalolin domin gudun aukuwar asara su ne, a yanka kajin a adana su a gidan sanyi, wato Cold Room. Wannan ita ce hanya a matakin farko ke nan. Da irin waɗannan ne Kudancin ƙasar nan suka tsere mana. Wato Malam Bashir akwai hanyoyi masu yawa da za a warware matsalolin kiwo da inganta su Arewa. Shi ya sa mu a Jihar Gombe muka yi ƙoƙarin haɗa kan manoma kiwon kaji a matakin ƙananan hukumomi da jiha baki ɗaya,domin taimaka wa juna. Akwai bayanai masu tarin yawa da lokaci ba zai ba ni damar faɗin su gaba ɗaya a wannan lokaci ba.

TG: Ana raɗe-raɗin Gwamnatin Tarayya za ta buɗe boda don shigowa da shinkafa da sauran kayan abinci. Shin yaya kake ganin haka, anya shirin ba zai shafi manoman Najeriya ba?

MK: Ni a nawa ra’ayin, za a samu sauƙi idan aka buɗe boda, saboda za mu samu sauƙi fiye da halin da muke ciki a yanzu, duba da yadda ‘yan jari-hujja ke tsauwala mana farashin kayayyaki a duk lokacin da suka ga dama.

Previous Post

Wasu Muhimman Darussa Daga Zantuttukan Bukar Usman

Next Post

₦16,000 Za Mu Sayar Da Taki A Jigawa – Gwamna Namadi

Related Posts

SHIRIN BUNƘASA NOMA NA ƘASA A JIHAR KATSINA (NATIONAL AGRICULTURAL COMMODITIES PROJECT KATSINA STATE) NA GAYYATA
Noma Da Kiwo

SHIRIN BUNƘASA NOMA NA ƘASA A JIHAR KATSINA (NATIONAL AGRICULTURAL COMMODITIES PROJECT KATSINA STATE) NA GAYYATA

December 11, 2024
SANA’AR NOMA: Ya Dace Attajirai Su Tallafa Wa Matasan Arewa – Dokta Sharif Almuhajir
Noma Da Kiwo

SANA’AR NOMA: Ya Dace Attajirai Su Tallafa Wa Matasan Arewa – Dokta Sharif Almuhajir

September 17, 2023
DAMINAR BANA: Mu Dai A Yankinmu Sai Godiya – Barden Kubau
Noma Da Kiwo

DAMINAR BANA: Mu Dai A Yankinmu Sai Godiya – Barden Kubau

September 2, 2023
Next Post
₦16,000 Za Mu Sayar Da Taki A Jigawa – Gwamna Namadi

₦16,000 Za Mu Sayar Da Taki A Jigawa - Gwamna Namadi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

KANA SON FAHIMTAR MATA?

KANA SON FAHIMTAR MATA?

November 9, 2023
An Ƙarfafa Ƙawance Tsakanin Jigawa Da Zinder

Ambaliya: Gwamnan Jigawa Ya Nemi Tallafin Bankin Duniya

July 8, 2023
SASSANYAN AMINCI (5)

SASSANYAN AMINCI (5)

September 12, 2025
Abubakar Dalhatu Zurmi: Zahirin Ɗan Kasa Nagari Mai Kishin Ƙasa

Abubakar Dalhatu Zurmi: Zahirin Ɗan Kasa Nagari Mai Kishin Ƙasa

October 10, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)
  • Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
  • Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.