• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, January 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Lallai Hukuma Ta Tallafa Wa Marubuta Domin Yaƙar Jahilci – Sheikh Gamawa

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 18, 2023
in Adabi
0
Lallai Hukuma Ta Tallafa Wa Marubuta Domin Yaƙar Jahilci – Sheikh Gamawa

Sheikh Said Gamawa

87
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Lallai Hukuma Ta Tallafa Wa Marubuta Domin Yaƙar Jahilci – Sheikh Gamawa

Related posts

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

December 6, 2025
Sheikh Said Gamawa, a yayin wani taro

~~~~~~~
Sheikh Aliyu Said Gamawa na ɗaya daga cikin malaman addini da ke faɗakar da al’umma kuma marubucin littattafan addinin Musulunci. Shi ne Sarkin Malaman Gamawa a Jihar Bauchi. Taskar Gizago ta tattauna da shi dangane da al’amuran rubuce-rubucensa kuma ga yadda ta gudana:
~~~~~~~

TG: Ya Sheikh, ya zuwa yanzu ka rubuta littattafai da yawa, tun yaushe ka fara rubutu kuma mene ne ya ja ra’ayinka ga harkar rubuce-rubuce?

Sheikh Gamawa: Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad (saw) da alayensa da sahabbansa da waɗanda suka biyo shi da kyautatawa har zuwa ranar alƙiyama. Bayan haka; ina farin cikin samun wannan dama da wannan kafar sadarwa mai albarka ta Jaridar Taskar Gizago. Ina fatan haɗuwa da ‘yan uwa masu sha’awar rubutu da karatu. Kuma zan ƙaru da masana a wannan fanni. Kuma na ƙaru da masu baiwa ta fasahar isar da saƙo ta hanyar rubutu. Ina neman taimakon Allah wajen dacewa da wannan saƙo.

Na fara rubuce-rubuce tun wajen 1990, kuma abin mamaki zuwa ga shirin Shafa Labari Shuni… a Radio Nigeria Kaduna. In mun tashi karatu ko hira da dare sai mu je mu ji wannan shiri. Kawai sai hannu da zuciya suka ɗauke ni ni ma na yi nawa karambanin a matsayin farau. Abin mamaki na aika ta gidan waya, kawai sai na ji ana karantawa.

Na samu shaƙuwa da karatu da rubutu ne a gida don, a karkara ba sosai ake barin yara suna fita yawo ba dalili ba. Zaman gida ya sa kullum ina kan rubutu ko karatu na addini ko littattafan Hausa da Jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo. Wannan ne ya ja hankalina kan rubutu.

Daga nan sai aka ce yaya ba za ka rubuta littafin addini ba, za ka ɓige da wani ƙirƙirar labari a Shafa Labari Shuni?Wannan ya sa na fara da littafin “Hanyar Koyar Da Yara Addinin Musulunci.” Har yanzu yana nan a rubuce da biro. Sau ɗaya aka ta6a wallafa shi da bugun keken rubutu. Wannan littafi kai tsaye bibiyar littafin Durusud diniya na fiƙhu na yi. Littafi ne na ‘yan Sudan da ake koyarwa a makarantun firamare a da can. Shi na bi na fassara (littafin ya ƙunshi koyar da tsarki alwala da salla a karance da aikace, da yadda za ka koyar. Na rubuta shi a 1991.

Sai littafin farko da ya fita duniya ta gani, na yi shi ne a 1993. Wannan shi ne: “Bayani A Kan Jinya Da Jana’iza A Musulunci.” Malam Muhammad Babangida Muhammad na Jami’ar Bayero Kano (yanzu Farfesa ne a Sashin Nazarin Addinin Musulunci) ne ya duba mani shi da yi mani gyaregyare. Shi wannan littafi an yi ta gyarawa ana buga shi ya kai sau 7 kuma ya shiga hannun mutane da yawa a da da yanzu.

TG: Ya zuwa yanzu, littattafai nawa ka rubuta? Guda nawa aka buga a littafin takarda kuma nawa ka buga a intanet?

Sheikh Gamawa: Na rubuta littattafai 25, mafi yawa an buga su, wasu ma fiye da sau 10, wasu sau biyar, adadi dai daban-daban.

Ga jerin littattafan da na rubuta kuma aka buga su:
1-Rayuwar Iyali A Musulunci.
2-Bayani A Kan Tsarki Da Sallah.
3-Hanyar Da Ake Samun Ɗa Nagari.
4-Bayani A Kan Azumi (Bisa Koyarwar Alƙur’ani Da Sunnah).
5-Bayani A Kan Jinya da Jana’iza A Musulunci.
6-Gobarar Zamani (Littafi Na 1 Da Na 2).
7-Ilimin Alƙur’ani (Saukarsa, Mu’ujizarsa, Yadda Aka Tattara Shi Da Falalar Karatunsa).
8-Bayani A Kan Aikin Hajji Da Umra Da Tarihin Wuraren Ibada.
9-Falalar Addu’a Da Zikiri A Musulunci.
10-Bayani A Kan Shafar Aljanu, Sihiri Da Bokanci A Musulunci.
11-Tsarin Banki, Kasuwanci Da Asusun Hannun Jari A Musulunci.
12-Bayani A Kan Zakka Da Hukunce-Hukuncenta A Musulunci.
13-Tafarkin Tsira Bisa Fahimtar Rukunnan Musulunci.
14-Kira Zuwa Ga Tafarkin Magabata Naƙwarai (Mahajus Salafus Salih).
15-Tarihin Rayuwar Sa’adu Ɗan Abi Waƙƙas (RA).
16-Gargaɗi Da Hani A Kan Waƙa, Aske Gemu, Hoto Da Haramcin Shan Taba A Musulunci. 17-Al-Muntakab fi ahadithir Rasul (SAW).
18-Bayani A Kan Da’awah Da Muhimmancinta A Musulunci.
19-Kafofin Sada Zumunta Na Zamani (Social Media) A Mahangar Musulunci.
20-Matsayin Kiyaye Harshe A Musulunci.
21-Bayani A Kan Tauhidi Da Imani.
22-Tarihin Farin Jakada Annabi Muhammad (SAW). Littafi Na Ɗaya Da Na Biyu.
23-Siffofin Ɗan Agaji Naƙwarai.
24-Hanyar Da Ake Koyar Da Yara Addinin Musulunci. (Wannan ba a buga shi ba).
25-Falalar Biyayya Ga Iyaye Da Wajibcin Kyautata Masu. (Wannan ba a buga shi ba).

Yanzu haka ana kan aikin ɗora su a intanet. Idan an gama za mu sanar da al’ummarmu in sha Allahu.

TG: Waɗanne irin matsaloli kake fuskanta a matsayinka na marubuci?

Sheikh Gamawa: Rubutu akwai wahala da ƙalubale masu yawa. 1-Samun loakcin rubutu, don abubuwan rayuwa sun fara yi mani yawa. 2-Masu duba mani aikin suna takura da matsi don su ma da nasu aikin. Littafin addini dole ka je ga waninka ya taya ka dubawa da gyara daga malumanmu. 3-Tsadar bugawa, wannan ya sa a yanzu littafi biyu ne kawai a hannu, duk sauran sun ƙare kuma an kasa sake bugawa. Ga 4-Lalaci ya sa ana ta matsa mani wai in bi littafan gaba ɗaya in karanta su a minti 30-30 don a riƙa saurare, maimakon a samu lokacin karatu. Wai jama’a ba su da lokaci da juriyar karatu yanzu, har gidajen rediyo na matsa mani a kan haka. Akwai ƙalubalen ƙarancin masu sha’awar rubutu da karatu a fagen ilimi, wai yanzu an fi son kallo da saurare.

TG: Tun daga fara rubutu, waɗanne irin nasarori ka samu ko kuma akasin su?

Sheikh Gamawa: Alhamdu lillah na samu kusanci da shaƙuwa da ƙaruwa da malamai da yawa a jami’o’i da mutanen kirki maza da mata. Na sha shiga gasar rubutu a makarantu da gidajen rediyo kuma an sha ba ni kyauta mai faranta rai.Na yi abokai na alheri waɗanda ba zan manta da su ba a rayuwata. Ina shan saƙon addu’a gare ni da iyayena da malamaina, a ciki da wajen ƙasa.

Na ji daɗin abotar rubutu, musamman lokacin da jaridu ke saka rubutuna.
Jaridu irin su: Gaskiya Ta Fi Kwabo, Attatbiq, Aminiya, Jaridar JTI da sauransu.

Na samu gayyatar yin rubutu a kan babi daban-daban daga manyan mutane da manyan shugabanni, waɗanda sun ɗauki nauyin bugawa da raba su sadaka sau da yawa. An sha yi mani kyautar alfurma a kan rubutu.

TG: A harkar rubuce-rubuce, waɗanne marubuta ne gwanayenka, da kake koyi da rubutunsu?

Sheikh Gamawa: Akwai marubuta da yawa da suka yi littattafai, waɗanda suka yi mani tasiri, mafi yawa da su nake son koyi amma na kasa. Amma sun kasu kashi biyu ne.

Akwai waɗanda ban gan su ba, ban yi alaƙa da su ba, sai aikinsu. Irin su Sheikh Nasiruddenil albani, Sheikh Abdullahi bin abdul aziz Bin Baz, Shekh Abubakar Mahmud Gumi, Dokta Abubakar Imam, Malam Halliru Binji. Sai waɗanda suka rubuta littattafan: Rayyayen Nahawun Hausa, Tarihin Annabi Kammalalle, Mutum Da Sana’arsa, Fasaha Aƙiliyya, Waƙoƙin Mu’azu Haɗeja, Infiraji da sauransu.

Amma waɗanda na gani na yi alaƙa da su, su ne: Alƙali Na’ibi Suleiman Wali, Dokta Yahya Tanko Kano, Farfesa Muhammad Babangida Muhammad (BUK), Dokta Aminuddeen Abubakar Kano, Alƙali Abdulmalik Baffa Mahmud Azare da sauransu.

TG: Ya zuwa yanzu wane sabon littafi kake kan rubutawa kuma zuwa yaushe zai fita ga al’umma?

Sheikh Gamawa: Ina kan sake duba dukkan littattafaina da yi masu ragi da ƙari don saka su a intanet. Wannan ya sa ba ni da sabo da nake yi a yanzu. Sai wannan a kan biyayya ga iyaye, wanda na jingine shi sai bayan wannan aikin.

TG: Wasu marubuta sun koma rubutun fim, ko kai ma kana da shirin rubuta wani littafi na faɗakarwa da za a maida zuwa fim?

Sheikh Gamawa: A can baya na taɓa sha’awar littafina mai suna Gobarar Zamani, a yi shi cikin wasan kwaikwayo da burin ya zama faɗakarwa ga al’umma amma yanzu ba ni da wannan tunani. Zan bar shi a rubuce haka. An sha karanta shi a gidajen rediyo, irin su: FRCN Kaduna, BRC Bauchi da FM na jihohi da dama kuma an sha ɗaukar nauyin buga shi ana raba wa mutane kyauta a makarantu.

Taken sa shi ne: “In ana karanta shi ba a iya barci.” Na sabunta shi ya kai sau 5, har na gaji. Amma yanayin fim na yanzu ba zai dace da rubutuna ba.

TG: Mene ne babban burinka dangane da rubutu?

Sheikh Gamawa: In samu ci gaba da rubuta littattafai tun daga waɗanda na yi a baya da waɗanda zan yi a gaba, su isa zuwa ga al’umma, a ci gaba da karanta su yanzu da bayan na koma ga Allah. Ina burin rubutuna ya kai duk duniyar da ake jin Hausa da fatan ya zama sadaƙatul-jariya gare ni da mahaifana.

TG: Ko kana da wani kira ga gwamnati da marubuta ‘yan uwanka da kuma al’umma masu karanta littattafanka?

Sheikh Gamawa: Ina kira ga hukumominmu su tallafa wa marubuta da nemo hanyoyin cusa wa al’umma son karatu da rubutu. Lalaci zai ɓoye mana alheri mai yawa cikin littattafan da ke ɗakinmu. Da yawan karatu da rubutu ne za mu yaƙi jahilci da sanin fannonin ilimi masu yawa in muna juriyar karatu da rubutu. Ina fatan hukumomi su fito da dabarun ƙulla ƙauna tsakanin al’ummarmu ta yau da son karatu da rubutu ta hanyar faranta wa marubuta da taimaka masu.

Gwamnati ta sauƙaƙe hanyar wallafa littatttafai, ana ƙarfafa wa marubuta ta hanyar ɗaukar nauyin bugawa da rabawa da ba su lambar girmamawa. Marubuta su kakkafa ƙungiyoyin dawo da darajar karatu da rubutu zukatan ‘yan yau. A dawo da mutumcin jaridu da mujallu da harshen Hausa don amfanin matasanmu maza da mata da suka tare kafar social media.

Ina roƙon duk wanda ya karanta rubutuna ya ga kuskure, ya sanar da ni in gyara, matuƙar ina raye. Idan na koma ga Allah, ya gyara, ya yi mani addu’ar Allah Ya yafe mani. Na gode.

Previous Post

Kyautata Wa Marayu Da Mabuƙata Alheri Ne

Next Post

Related Posts

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)
Adabi

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine
Adabi

Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

December 6, 2025
Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu
Adabi

Yau Take Juma’a: Allah Ka Albarkace Mu

December 5, 2025
Next Post

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

A MESSAGE TO THE AREWA SOCIAL MEDIA INFLUENCERS

A MESSAGE TO THE AREWA SOCIAL MEDIA INFLUENCERS

August 2, 2025
Ƙauna ita ce tushen zamantakewa

Zamantakewa: Kowace Mace Na Buƙatar Namiji Kusa Da Ita

July 11, 2023
BIU: A Visit to a City on a Plateau (5)

BIU: A Visit to a City on a Plateau (5)

February 9, 2024
THE MAN B. Y. M.

THE MAN B. Y. M.

June 28, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation
  • Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco
  • Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

Tafawa Balewa, Sardauna And 15th January: A Day of Lamentation

January 15, 2026
Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

Gasar Kofin Afrika: Yau Take Tsakanin Nigeria Da Morocco

January 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.