• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, March 8, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Sinadarin Rayuwa

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 19, 2023
in Sinadarin Rayuwa
0

Barka da Sabuwar Shekarar Musulunci

13
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

1445 Hijiriyya: Muhimmanci Da Tasirin Sabuwar Shekara Ga Al’umma

A yayin da muka shiga sabuwar shekarar Musulunci 1445 Hijiriyya, bari mu yi nazari da tariya domin nusar da al’umma muhimmanci da tasirin shekarar ga rayuwar al’umma. Me ya kamata mutum ya yi domin cin gajiyar lokacinsa a wannan sabuwar shekara?

Related posts

Kada Ka Karaya Da Rayuwa

Kada Ka Karaya Da Rayuwa

November 30, 2025
Aiki Ya Fi Surutu: Muhimmin Darasi Ga Duk Mai Neman Nasara

Aiki Ya Fi Surutu: Muhimmin Darasi Ga Duk Mai Neman Nasara

November 24, 2025

A yau Laraba ce muka shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1445 (Bayan Hijira), don haka muke taya ɗimbin masu karatunmu barka da shiga wannan sabuwar shekara lafiya. Wannan ya nuna mana cewa, rayuwa na nufin shuɗewa daga wani zango zuwa waccan, domin kuwa watanni goma sha biyu da suka gabata sun yi mana ishara da haka.

Wannan dalili ne ma ya sanya muka ga ya dace mu yi tariya da tsokaci game da taken maudu’inmu na yau da ke sama, wato game da rayuwar al’umma, musamman ma shawarwarin da al’umma ke buƙata domin tunkarar ƙalubalen da wannan shekara ta bijiro mana da su a rayuwa.

Babu shakka, mutum bai yi kaɓɓa ba, bai yi katoɓara ba kuma bai kwafsa ba, idan ya ɗauki wannan maudu’in na yau da ke sama, sannan ya nazarce shi da idon basira. Wannan zai ba mutum damar ɗaura babbar ɗamarar tunkarar al’amuran rayuwa gadan-gadan. To, amma idan muka dubi kanun maudu’inmu na yau, mun ambaci al’umma gaba ɗaya, sai dai kuma za mu fi karkata akala ga matasa. Ko me ya sanya? Ga dalili:

Matasa ne aka yi ittifaƙin sun fi kowa yawa a yanayin rayuwarmu ta yau kuma su ne mafiya muhimmanci wajen fuskantar rayuwa, haka kuma su ne mafi akasari suke yin nadama da da-na-sanin ɗaukar wani mataki na rayuwa.

Matasa ne kan fuskanci babban ƙalubalen da ke sanyawa ko dai su samu nasara ko kuma su faɗi warwas. Dalili ke nan ya sanya za mu yi amfani da wannan lokacin, domin bijiro musu da wasu shawarwari domin jagora ga rayuwa, domin mu ƙara masu ƙaimi, domin mu tada su daga barci, idan barcin suke yi.

A lokacin da muka shiga wannan sabuwar shekara ta Hijiriyya, akwai buƙatar matasa su tsaya da ransu, su natsu, su gane muhimmancin lokaci, su daina ɓata lokaci wajen gudanar da wasu ayyuka ko al’amura marasa tasiri, wanda yin haka babu abin da zai amfane su da shi sai asarar lokacinsu. Ga masu hikimar magana kuwa, sun ce lokaci dukiya ne, duk wanda ya ɓata shi, ya ɓata rayuwa.

Idan mun lura da yadda matasanmu suka shantake kuma suke ɓata lokacinsu wajen gudanar da wasu abubuwa marasa tasiri ga rayuwa, lallai kuwa akwai buƙatar a yi musu tambihi, domin ankarar da su, su bi turbar da ta dace.

Ta wace hanya ce matasa za su ci gajiyar lokacinsu a cikin wannan shekara ta Hijiriyya da Allah cikin ikonSa muka shigo? Na farko dai, kamar yadda muka sha nanatawa a wannan fili, yana da kyau mutum ya raba lokacinsa zuwa gida-gida kuma daki-daki, sannan ya aiwatar da al’amuransa bisa jagorancin tsarin da ya yi wa lokacin nasa. Misali, a wannan zamanin, babu abin da ya kamaci matashi kamar neman ilimi. To, kuma ba neman ilimi ne kaɗai rayuwa ba, don haka sai matashi ya tsara lokacin karatu da lokacin neman wasu abebaɗai na rayuwa daban.

A nan ne ma ya kamata in jawo hankalin matasa, musamman ma masu ɓata lokacinsu wajen kallon ƙwallon Turawa, wanda illar haka har ta yi tasiri a rayuwarsu. Haka na haddasa rugujewar al’amuran matasa da dama. Misali, a wajen kallon ƙwallon nan, matasa kan shiga lokacinsu na hutu da ma lokacin da za su tsinana wa kawunansu wani aiki na amfani. A wajen kallon ƙwallon nan, za ka ji ana gardama, wacce ba ta da siɗi balle saɗaɗa.

Ƙwarai kuwa! Babu dalilin da zai sa matashi ya jajirce yana gardama game da wani mutum, wanda bai san ma shi matashin yana cikin duniya ba. Haka kuma, gardamar ba ta da amfani, domin ba wata ƙaruwa ta ilimi ko dukiya da mutum zai samu a sanadiyyar ta ba. To, me ya yi zafi da mutum zai ɓata lokacinsa haka?

Wani lokaci ma illar ba a gardamar kaɗai take tsayawa ba, abin na yin zurfi har ya kai ga faɗa. Faɗa ba ƙarami ba kuwa, domin takan kai ga yi wa juna rauni, wani lokaci ma har da rasa rayuka. To, idan aka yi rashin dacen haka ta faru, mene ne amfanin wannan kallon, kuma mene ne matashin ya samu a sanadiyyar haka?

A lokacin da muka shiga sabuwar shekara, matasa su maida hankali ga ayyukan ci gaba, su guji zaman kashe wando ko zaman maula. Babu abin da mutum zai amfana daga haka sai asara bisa asara. Kuma ina amfanin matashi ya wayi gari bai da abin yi sai dai zaman tsegumi da maula? Mu tuna da cewa, wanda ya miƙe ya nemi sana’a komai ƙanƙantarta, kuma idan dai za ta rufa masa asiri, ya fi ya zauna dashasha, wai sai wani ya nemo, sannan shi ya je yana maƙe murya don a ba shi. Babu shakka wannan ba ƙaramar illa ba ce ga rayuwa. Don haka, muddin matashi ya shiga sabuwar shekara da irin wannan ƙudurin, na cewa sai an ba shi na zaman kashe wando, to, lallai haka watannin nan goma sha biyu za su shuɗe, ba tare da ya tsinana wa kansa komai ba.

Lallai kam akwai buƙatar matasa su ɗauki babban darasi daga na gaba da su, musamman tsofaffi da ke raye da waɗanda suka shuɗe. Tasirin haka shi ne, domin masu iya magana sun ce, da na gaba akan gane zurfin ruwa. Duk wanda ya samu nasarar rayuwa ta fannin ilimi ko dukiya ko kuma rufin asirin rayuwa, akwai dalilin kasancewarsa haka. Domin kuwa a lokacin da yake ƙuruciya, babu shakka bai wulaƙanta kansa da lokacinsa ba. Ke nan ya yi amfani da lokacinsa yadda ya dace, wajen neman sana’arsa ko aiki; wanda haka ya sanya ya samu nasarar abin da ya sanya a gaba.

A taƙaice, darasinmu na yau na kira ne ga al’umma, musamman matasa, su fahimta da amfanin lokaci a rayuwa. Su binciki ayyukansu da rayuwarsu na shekarar da ta wuce, sannan su yi nazarin turbar da za su bi a cikin wannan sabuwar shekarar, da nufin samun nasara a rayuwa. Allah Ya taimaka mana, Ya yi mana jagora a cikin wannan sabuwar shekara, amin.

Previous Post

Lallai Hukuma Ta Tallafa Wa Marubuta Domin Yaƙar Jahilci – Sheikh Gamawa

Next Post

Sojoji Sun Cafke Manyan Dillalan Miyagun Ƙwayoyi

Related Posts

Kada Ka Karaya Da Rayuwa
Sinadarin Rayuwa

Kada Ka Karaya Da Rayuwa

November 30, 2025
Aiki Ya Fi Surutu: Muhimmin Darasi Ga Duk Mai Neman Nasara
Sinadarin Rayuwa

Aiki Ya Fi Surutu: Muhimmin Darasi Ga Duk Mai Neman Nasara

November 24, 2025
A Rayuwa: Alheri Danƙo Ne
Sinadarin Rayuwa

A Rayuwa: Alheri Danƙo Ne

November 11, 2025
Next Post
Sojoji Sun Cafke Manyan Dillalan Miyagun Ƙwayoyi

Sojoji Sun Cafke Manyan Dillalan Miyagun Ƙwayoyi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Go Back to the Roots, Write in African Tongues – PAWA

Go Back to the Roots, Write in African Tongues – PAWA

March 18, 2024
Jami’ar Bayero Ta Karrama Janar Buratai

Jami’ar Bayero Ta Karrama Janar Buratai

December 16, 2023
BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (4)

BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (4)

January 14, 2024
Hajj 2023: Uba Sani, Arrigassiyu bag awards

Hajj 2023: Uba Sani, Arrigassiyu bag awards

September 24, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • RAMADAN KARIM: 19-1447
  • FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
  • RAMADAN KARIM: 18-1447

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

RAMADAN KARIM: 19-1447

RAMADAN KARIM: 19-1447

March 8, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.