• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, January 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Adabi

Sanadiyyar Rubutu, Zane Da Waƙa: Na Samu Arzikin Sanin Jama’a – Kamal

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 15, 2023
in Adabi
2
Sanadiyyar Rubutu, Zane Da Waƙa: Na Samu Arzikin Sanin Jama’a – Kamal

Kamal Iyantama

82
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Sanadiyyar Rubutu, Zane Da Waƙa: Na Samu Arzikin Sanin Jama’a – Kamal

Related posts

Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

January 17, 2026
SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Littafin Kamal

Idan ya ɗauki fensir da takarda ya zana mutum, sai ka ce hoton kyamara ne. Marubucin ƙirƙirarrun labarai ne kuma ga shi gwanin rera waƙa. Muna maganar matashi mai fiƙira – Kamal Iyantama. Taskar Gizago ta tattauna da shi kuma ya yi faffaɗan bayani game da baiwar da Allah Ya ba shi.

TG: Kana ɗaya daga cikin marubutan Hausa kuma mai zane-zane da waƙa a wannan zamani. Ko za ka gaya mana tarihinka a taƙaice?

KAMAL: To, Ma sha Allah. Kamar yadda aka ce a taƙaice, cikakken sunana shi ne Kamal Yunus Bin Abdallah, wanda aka fi sani da Kamal Y. Iyantama. An haife ni a Ƙaramar Hukumar Ƙanƙara ta kudancin Jihar Katsina, shekaru kusan ashirin da bakwai da suka wuce, kasancewar mahaifina ma’aikacin gwamnati ne lokacin. Daga baya aka yi wa babana canjin wurin aiki zuwa Ƙaramar Hukumar Malumfashi, duk dai a Katsina ɗin. A nan na yi makarantun Islamyya, Firamare da kuma Sakandare. Bayan na kammala na tafi Kwalejin Ƙimiyya da Fasaha Abdu Gusau da ke Talata Mafara, Jihar Zamfara, inda na samu cikakkiyar shaidar Diploma mai kuma cikakkiyar daraja ta ɗaya, a ɓangaren L.I. SCIENCE. Haka kuma na samu satifiket a ɓangaren Computer Science daga wata makaranta mai zaman kanta mai suna AL-INAM RESOURCES, COMPUTER INSTITUTE, tare da wasu ƙarin satifiket masu muhimmancin gaske, da lokaci ba zai bari in kawo su ba. Wannan shi ne dai a taƙaice tarihina.

TG: Tun yaushe ka fara rubutu da zane da waƙa kuma mene ne ya ja ra’ayinka ga harkar rubuce-rubuce?

KAMAL: To a haƙiƙanin gaskiya shi zane dai baiwa ce daga Allah, wato abin a jinina yake. Da zane Allah Ya ƙaddara aka haife ni. Ban taɓa zuwa wata makaranta wai da sunan koyon zane ba, ban taɓa zuwa wurin wani shi ma da sunan hakan ba. Na tsinci kaina ina yin zane tun lokacin da aka kai ni aji ɗaya a makarantar firamare kuma har zuwa yanzu da nike muke wannan hirar da kai, ina yin zane-zane.

Waƙa kuma a batu na gaskiya, na fara ta ne daga lokacin da hankali ya fara zuwar min, ta hanyar ji ko sauraren waƙoƙin mawaƙa mabambanta. Sai na ce bari in jaraba ko zan iya, kuma ikon Allah sai na ga nasara ta samu. Kamar yadda na shiga harka ta rubutu ko rubuce-rubuce, ita ma gani na yi hanya ce ta isar da saƙo zuwa ga al’umar duniya cikin hikima kuma cikin sauƙi. Sai na ga kuma ai ina da ɗimbin saƙonnin da suka dace in yaɗa wa duniya. Wannan shi ne dalilina na shiga harkar rubutu.

TG: Ya zuwa yanzu, littattafai nawa ka rubuta? Guda nawa aka buga a littafin takarda kuma nawa ka buga a intanet?

KAMAL: To alalhaƙiƙa ban iya ce ma ga iya adadin littattafan da na rubuta, saboda yawan da suke da shi. Sannan waɗanda aka buga a littafin takarda ba su wuce guda biyar ba saboda rashin gamsuwar da na yi kan taɓarɓarewar harkar buga littafin ya sa na ɗan dakata. Su kansu wanɗanda na buga ɗin ma ban fitar da su ba, saboda rashin tabbas kan kasuwa da kasuwancin littafi, wadda nike fatar daidituwar lamuran da izinin Allah.

Batun bugawa a intanet shi ma dai babu ko ɗaya da ke kan kasuwar littafi ta samaniya, sai dai lokaci zuwa lokaci nakan ɗan tsakuro in yaɗa.

TG: Waɗanne irin matsaloli kake fuskanta a matsayinka na marubuci?

KAMAL: Matsaloli kam Malam ga su nan barkatai, sai dai babba a cikin manyan ita ce rashin jari, wanda shi ne babban turke ko jigo a harkar buga littafi ko rubutu. Sannan kuma satar fasaha ita ma babba ce cikin matsalolin rubutu. Haka kuma akwai rashin haɗin kan marubuta.

TG: Tun daga fara rubutu da zane, waɗanne irin nasarori ka samu ko kuma akasin su?

KAMAL: Gaskiya Alhamdu lillah! A kullum cikin godiyar Allah nike da irin nasarorin da yake ba ni a harkar rubutu da zane-zane. Don a dalilin rubutu har lambar girmamawa na samu kan zaman lafiya a shekarar 2012. Haka ma na samu nasarar haɗuwa tare da ƙulla kyakkyawan zumunci tare da manyan marubuta maza da mata, wanda a da sai dai a labarai nike jin su, ko hotunansu ba na gani. Uhm! Ko kai Malam Bashir, duk da muna gari ɗaya, ba mu san juna ba sai a dalilin rubutu. Ka ga wannan ma nasara ce a gare ni. Haka a dalilin zane, na samu nasarar haɗuwa da manyan mutane a ƙasar nan, kamar gwamnoni, matan gwamnoni, ministoci, manyan ‘yan siyasa da sauran manyan mutane masu yawan gaske. Kuma dai wallahi sai ƙarin godiya ga Allah.

TG: A harkar rubuce-rubuce da zane, waɗanne marubuta da masu zane ne gwanayenka, da kake koyi da rubutunsu?

KAMAL: Turƙashi! A zahirin magana dai gwanayena a rubutu suna da yawa, sai dai in ɗan tsakuro maka wasu daga ciki. A cikin maza akwai Madakin Gini (BAJAKADE), Abubakar Imam (MAGANA JARI CE), Nazir A. Salihi (KIBIYAR AJALI) da Bashir Y. Malumfashi (KUƊIN JINI).

A cikin mata kuwa akwai Rahma A. Majid (MACE MUTUM), Jamila U. Tanko (ƘABILATA) da kuma Maimuma Beli (NA SHIGA ALJANNA).

TG: Ya zuwa yanzu wane sabon littafi kake kan rubutawa kuma zuwa yaushe zai fita ga al’umma?

KAMAL: A yanzu dai kam ina tsaka da rubuta wani littafi mai suna KAMAR RAHILA, sai dai ba zan iya cewa ga lokacin da zan kammala shi ba, saboda ka san shi rubutu ɗan nazari da tunani ne, wanda yake buƙatar lokaci ba batun gaugawa. Idan lokaci ya yi in sha ha Allah zai bayyana.

TG: Wasu marubuta sun koma rubutun fim, ko kai ma kana da shirin rubuta wani littafi na faɗakarwa da za a maida zuwa fim?

KAMAL: Ƙwarai ma kuwa Malam, ai yanzu haka na juya da yawan litt

Kamal Mawaƙi

afaina zuwa fim, tare da wasu da daman gaske. Wasu ma yanzu haka ana aikin gudanar da fim a kansu. A cikin su akwai, WANNAN DUNIYAR, DINDINDIN, GAWAR RAHILA, RAI DA RAYUWA, NI DA KE MUN YI KAMA, GARNAƘAƘI, JUMANA da kuma BINTU – ADNAN.

TG: Mene ne babban burinka dangane da rubutu da zane?

KAMAL: Babban burina a dangane da rubutu ko zane ba ya wuce tsarkake harshe da alƙalami, wurin rubuta abin da zai amfani al’umma ko bayan babu rayuwata ban bar baya da ƙura ba. Haka a ɓangaren zane, shi ma ba ya wuce in ga ya zama silar in samu mace tagari in yi aure, in samu zuri’a tagari, in taimaki iyayena, mu rabu da su lafiya in cika da imani.

TG: Ko kana da wani kira ga gwamnati da marubuta ‘yan uwanka da kuma al’umma masu karanta littattafanka?

KAMAL: To, kira na dai ga gwamnati shi ne ta daure ta riƙa ɗaukar mu, mu marubuta da muhimmancin gaske, ta hanyar yi mana duk wani taimako ta kowane fanni, domin muna da baiwa da hikimomin isar da kowane irin saƙo a salo daban-daban.

Haka ‘yan uwana marubuta, ina ƙara kira gare mu da mu sani Allah Ya zaɓe mu tare da ba mu wata irin baiwa wadda za ma yi amfani da ita wurin sauya duniya daga ba daidai ba zuwa daidai. Don haka komai za mu yi, mu yi don Allah saboda mu ɗin abin tambaya ne. Haka ku ma masoyana ko masu karanta littattafaina, ku ci gaba da kasancewa tare da ni, domin ni ma ina tare da ku, sannan ina marhabin da duk wurin da kuka ga kuskurena ku ankarar da ni Wannan ita ce soyayya ta gaskiya.

 

Previous Post

Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

Next Post

Tarihin Shekara Biyu: Waiwaye A Turbar Nasara

Related Posts

Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a
Adabi

Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

January 17, 2026
SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)
Adabi

SAKAMAKON ZAGAYE NA BIYU NA GASAR RUBUTU TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

December 23, 2025
Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine
Adabi

Dalilan Da Suka Sanya Na Rubuta Littafin Tarihin Maitatsine

December 6, 2025
Next Post
Tarihin Shekara Biyu: Waiwaye A Turbar Nasara

Tarihin Shekara Biyu: Waiwaye A Turbar Nasara

Comments 2

  1. Alh Sada Rumah, Danwairen Katsina. says:
    3 years ago

    Taskar Gizago ta bijiro da sabuwar alkiblar samun sahihan labarai bisa doron mahangar hikima, da mutuntaka, da ilimin aikin jarida a zamanance.
    Maraba da sassaukar madafa ta sanin halin da Duniya ke ciki, tare da fito da 6oyayyun fasahohin matasa maza da mata, ba kuma tarevda an yi watsi da dattawa ko tsohuwar Zuma ba.
    Na aminta, Kuma Ina tare da Taskar Gizago!

    Reply
    • Bashir Yahuza Malumfashi says:
      3 years ago

      Ma sha Allah. Taskar Gizago na godiya da wannan babbar shaida da sa albarka daga babba kuma ƙwararren ɗan jarida, Danwairen Katsina. Allah saka da alheri.

      Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (2)

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (2)

May 7, 2025
Tambayoyin Neman Sani A Kan Littafin: JAWAHIRUL MA’ANI

Tambayoyin Neman Sani A Kan Littafin: JAWAHIRUL MA’ANI

October 5, 2025
Gwamnan Katsina Ya Raba Ma’aikatar Ilimi Zuwa Gida Uku

Katsina Governor Inaugurates Committees to Distribute Palliative

September 27, 2023
Gwamnan Katsina Ya Taya Murna Ga Ganduje Da Sauran Shugabannin APC

Gwamnan Katsina Ya Taya Murna Ga Ganduje Da Sauran Shugabannin APC

August 6, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)
  • Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
  • Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.