• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, January 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Addini

Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 14, 2023
in Addini
0
4
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Unguwar Tumbu – Madallah

Related posts

Baffa Hotoro Ka Ci Amanar Ilimi

Baffa Hotoro Ka Ci Amanar Ilimi

November 29, 2025
Jama’a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban

Jama’a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban

November 28, 2025

A yau Juma’a, 26-12-1444 (Hijriyya), 14-07-2023 (Miladiyya), a Masallacin Unguwar Tumbu da ke Garin Madallah, Ƙaramar Hukumar Tafa, Jihar Neja; Liman ya buɗe huɗubarsa da godiya ga Allah da yabo da salati ga fiyayyen talikai, Manzon Allah (saw). Sannan ya fara gabatar da huɗubar mai taken: “Mu Guji Zalunci, Mu Ji Tsoron Allah.”

Malam ya bayyana cewa lallai zalunci abin ƙi ne, saɓon Allah ne kuma alfasha ne, wanda duhu ne a ranar ƙiyama. Ya gargaɗe mu da mu kauce wa zalunci kowane iri, domin sakamakonsa azaba mai raɗaɗi ga wanda ya tafi lahira da haƙƙin zaluntar wani.

Malam ya gabatar da wani hadisi, wanda ke nuna yanayin ranar tashin ƙiyama a matsayin ranar tashin hankali, ranar da komai zai zama zafi da uƙuba. Sai dai a ranar akwai rukunin mutane bakwai da za su tsira, waɗanda za su shiga “Inuwar Allah” ta musamman. Waɗannan kuwa su ne:

1-Adalin shugaba wanda ya guje wa zaluntar waɗanda yake wa jagora. 2-Mutum mai bautar Allah da gaskiya, wanda bai shagaltar da rayuwarsa ga aikin assha ba, sai dai bautar Allah. 3-Matashi da ya rataya rayuwarsa ga masallaci, shi ne hidima da ibada da raya shi. 4-Mutane biyu da suka haɗu cikin zumunci da soyayya don Allah kawai. 5-Mutumin da ya guje wa riya, mai yin sadaka da hannun dama, alhali hagunsa bai san abin da ya bayar ba. 6-Mutumin da wata mace mai ɗaukaka da dukiya ta neme shi da alfasha, amma ya ƙiya saboda tsoron Allah. 7-Mutumin da ya kaɗaice cikin tunanin tsoron Allah har hawaye ya zubo masa.

Liman ya ci gaba da huɗuba, inda ya bayyana cewa zalunci iri uku ne, kamar haka:

1-Shirka, watau tara bautar Allah da wanin Allah (babban zalunci) ne. 2-Mutum ya zalunci wani mutum ko halitta a dukiyarsa ko jikinsa, da sauransu. 3-Mutum ya zalunci kansa da kansa, ta hanyar dulmiya cikin aikata saɓon Allah.

Malam ya gargaɗi mutane da su tuba daga aikata zalunci, su biya haƙƙin waɗanda suka zalunta tun a duniya, kafin a je lahira, inda babu abin biya, sai dai a ɗebi aikin ladar mutum a biya, ko kuma a ɗebi zunubin wanda aka zalunta a lafta wa mai zaluncin, idan bai da aikin ƙwarai.

Malam dai ya ja hankalin mutane da cewa lallai akwai hisabi ranar lahira, don haka mu ƙaurace wa zalunci.

Liman ya rufe huɗubarsa da addu’a ga al’umma da fatan mu gama da duniya lafiya. Haka kuma ya yi salati da sallama ga Manzon Allah, Annabi Muhammadu (saw).

Allah sa mu dace, Ya amintar da mu duniya da lahira, amin.

Previous Post

Buƙatarmu Mu Bunƙasa Rayuwar Mata, Matasa Da Kyautata Muhalli – Gwamnan Jigawa

Next Post

Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

Related Posts

Baffa Hotoro Ka Ci Amanar Ilimi
Addini

Baffa Hotoro Ka Ci Amanar Ilimi

November 29, 2025
Jama’a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban
Adabi

Jama’a Mu Fahimta: Musulunci Daban Ƙungiyanci Daban

November 28, 2025
Muhammadu (Saw): Haske Mai Haskakawa
Addini

Muhammadu (Saw): Haske Mai Haskakawa

November 21, 2025
Next Post
Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

Huɗubar Jumu'a Daga Limamin Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

NOMA YANKE TALAUCI: Ku Zo Mu Ziyarci Lungu Da Saƙon Gonar Ɗankano

NOMA YANKE TALAUCI: Ku Zo Mu Ziyarci Lungu Da Saƙon Gonar Ɗankano

August 22, 2023
FAUZIYYA ƊANLADI SULEIMAN: Tattaunawa Da Uwar Marayu Da Raunana

FAUZIYYA ƊANLADI SULEIMAN: Tattaunawa Da Uwar Marayu Da Raunana

September 3, 2023
TSOKACINMU NA YAU (04)

TSOKACINMU NA YAU (04)

March 4, 2025
Ɗan Iyan Galadiman Katsina Emerges Chairman of Arewa Consultative Forum

Ɗan Iyan Galadima Ya Zama Shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa Ta Arewa

June 19, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)
  • Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
  • Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.