• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, July 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Buƙatarmu Mu Bunƙasa Rayuwar Mata, Matasa Da Kyautata Muhalli – Gwamnan Jigawa

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 13, 2023
in Babban Labari
0
Buƙatarmu Mu Bunƙasa Rayuwar Mata, Matasa Da Kyautata Muhalli – Gwamnan Jigawa

Gwamna Malam Namadi

23
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Buƙatarmu Mu Bunƙasa Rayuwar Mata, Matasa Da Kyautata Muhalli – Gwamnan Jigawa

Related posts

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

July 15, 2026
Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

July 11, 2026

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa babban ƙudurinsa shi ne ya ga ya samar da kyakkyawan yanayin muhalli, tare da bunƙasa rayuwar mata da matasa, ta hanyar samar da ayyukan yi da sana’o’in dogaro da kai,

Gwamnan ya bayyana haka ne, a yayin wata ƙwarya-ƙwaryar ziyarar aiki da ya kai a Hedkwatar Cibiyarb Inganta Muhalli ta Ƙasa, kamar yadda Babban-Sakataren Watsa Labarai, Malam Hamisu Gumel ya bayyana wa manema labarai.

A yayin ziyarar tasa, Gwamnan ya samu kyakkyawar tarba daga Daraktan hukumar, Dokta Maina Bukar da ma’aikatansa. Ya yaba da yadda hukumar ke gudanar da aikinta na inganta muhalli a faɗin ƙasar nan, wanda ya haɗa da magance zaizayar ƙasa da kwararowar hamada. Ya ce jiharsa ta Jigawa tana ɗaya daga cikin jihohi 11 na ƙasar nan da suke fuskantar wannan ƙalubale na sauyin yanayi da ke lalata muhalli.

Da yake ƙarin bayani ga Shugaban Hukumar, Gwamna Namadi ya lissafa irin tallafin da yake nema, waɗanda suka haɗa da dashen itatuwan marmari domin yaƙi da kwararowar hamada, bunƙasa noman rani domin samar da abinci da kuɗin shiga, ta hanyar samar da fanfunan ban ruwa masu aiki da hasken rana. Haka kuma ya buƙaci yadda za a horar da matasa da mata, ta hanyar koya masu sana’o’in hannu domin dogaro da kai.

Sauran buƙatun sun haɗa ba manoma horo na musamman da koyar da su dubarun noman zamani da ban ruwa ta amfani da rijiyoyin burtsatse da sauran hanyoyin bunƙasa rayuwar al’umma, wanda ya yi daidai da alƙawuran da gwamnan ya ɗauka a yayin yaƙin nan zaɓe.

Gwamnan ya jaddada muhimmancin samar da abubuwan bunƙasa rayuwar al’umma, waɗanda suka haɗa da samar da ingantaccen ruwan sha a wasu sassa na jihar. Ya ce gina rijiyoyin burtsatse a waɗannan yankuna zai yi matuƙar amfani, kasancewar ana samun ruwa ne a tsawon mita 90 a irin waɗannan yankuna.

Gwamna Namadi ya bayyana muhimmancin kula da kare muhalli. Don haka ya buƙaci a samar da hanyoyin rage gurbata muhalli, kamar samar da fitilun haskaka titi masu amfani da hasken rana, musamman a makarantu da sauran sassan jihar.

Ya bayyana buƙatar bayar da kula ta musamman ga ƙoramu da magudanun ruwa. Don haka ya ba da shawarar a riƙa yashe ƙoramu da koguna a kan kari domin sauƙaƙa gudanuwar ruwa. Ya roƙi wannan hukuma da ta sanar da gwamnati muhimmancin wannan, domin ɗaukar matakan da suka dace.

Da yake maida jawabi, Daraktan Hukumar ta National Agency for Great Green Wall (NAGGW), Dokta Maina ya gode wa Gwamnan saboda wannan ziyara. Ya ce lallai Jihar Jigawa na ɗaya daga cikin Jihohin da hukumar tasu za ta ba muhimmanci, musamman saboda babban ƙalubalen da suke fuskanta na ambaliya da kwararowar hamada. Ya ce hukumar za ta yi aikin haɗin gwiwa da jihar domin magance matsalolin, musamman wajen samar da shawarwari daga ƙwararru da tallafi ga yankunan da gwamnan ya zayyana.

Gwamnan na Jigawa ya yi godiya bisa ga kyakkyawar tarba da ya samu. Ya ce babu shakka idan aka samu haɗin gwiwa kuma aka yi aiki tare, hukumar za ta samu nasara sosai, wajen kare muhalli, bunƙasa noma da inganta rayuwar al’ummar jihar ta Jigawa.

Previous Post

Gizagawa Sun Yi Rashi A Katsina

Next Post

Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

Related Posts

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista
Babban Labari

Budurwa Mai Aikin Tausa Ta Mutu A Gidan Minista

July 15, 2026
Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo
Babban Labari

Jami’an Tsaro Sun Ceto Ɗalibai da Malaman Oyo

July 11, 2026
ACF Endowment Fund Sets Agenda for Transparency, Education and Empowerment in Northern Nigeria
Babban Labari

Asusun Tallafi na ACF Ya Tsara Sabuwar Hanyar Bunƙasa Ilimi da Ƙarfafa Al’ummar Arewa

June 25, 2026
Next Post

Huɗubar Jumu'a Daga Limamin Masallacin Unguwar Tumbu-Madallah

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Philip Chikwuedo Asiodu: A Legacy of Dedication and Service

Philip Chikwuedo Asiodu: A Legacy of Dedication and Service

December 16, 2025
WILL ATIKU’S EXIT FROM THE PDP BRING HIM VICTORY IN 2027?

WILL ATIKU’S EXIT FROM THE PDP BRING HIM VICTORY IN 2027?

July 19, 2025
A Review of Boko Haram and other Security Challenges in Nigeria

A Review of Boko Haram and other Security Challenges in Nigeria

April 20, 2024
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (4)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (4)

January 2, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • General Buratai to Marry Off His Daughter Today
  • Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya
  • Saƙon Godiya Da Bangajiya

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

General Buratai to Marry Off His Daughter Today

July 25, 2026
Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

Siyasar Gombe Ta Kacame Tsakanin Pantami Da Gwamna Yahaya

July 24, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.