• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, January 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Dausayin Kauna

Zamantakewa: Kowace Mace Na Buƙatar Namiji Kusa Da Ita

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 11, 2023
in Dausayin Kauna
1
Ƙauna ita ce tushen zamantakewa
117
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Yusuf Dingyaɗi

Zamantakewa: Kowace Mace Na Buƙatar Namiji Kusa Da Ita

Related posts

Shin Wai Akwai So? (1)

Shin Wai Akwai So? (1)

June 5, 2025
MENE NE SO?

MENE NE SO?

April 27, 2025

Tun daga lokacin da ake ta ribbibin rubuce-rubuce a kan zancen wanki da mace za ta yi wa miji, nake tunani tare da neman gano, shin me ya kawo wannan ne?

Irin mu da Allah Ya yi wa rufin asiri na kasancewa da mata biyu fiye da shekaru 20 zuwa yau, sai mutum ya kalli meye zancen wanki a cikin hulɗa ta aure?

Na fi ganin wannan ga talauci, ƙurciya da rashin tunani a kan masu yaɗa wannan, don kuwa ƙima, ɗaukaka da daraja na auratayya sun fi ƙarfin zancen yi wa miji wanki.

Wani lokaci sai na yi rubutu in goge, mussaman dangane da matan da ke ganin kansu ‘Indepedent’ daga ikon mazaje saboda tsabar wayewa ko rayuwa ta zamani.

Hakan ya sanya na ɗan saurara, sai yanzu ma ake gaya mani cewa wasu da ke ta yaɗa wannan shaiɗancin, tun haihuwa har lokacin girmansu iyaye mazaje ke ɗauke da nauyinsu, tun daga abinci, sutura, motar hawa har gidan da suke barci; sakamakon mazajen aure sun yi kamfa saboda ganin halayarsu, da ganin irin rayuwar da suke ciki ta wayewa.

Sai dai, na tabbata akwai irin Malala a cikinsu, waɗanda idan suka yi wuf da NAMIJI, tabbata ba su sake SURUTU.

Fahimtarsu a kan Namiji ta game kowa, saboda sun samu matsala da namiji ɗaya ko biyu a aure ko hulɗa, dalilinsu kevnan a kan ɗaukar namiji ba ɗan goyo ba, ko kuma amincewa da zancen: ‘Duk wadda ta ɗauki Namiji Uba, tabbata za ta kwana marainiya.’ Kodayake sun fitar da nasu iyayen daga cikin lissafi saboda son kai da dabbanci da daƙiƙancin tunani irin na son kai.

Duk da wannan, akwai wasu mata da ƙaddara ce ta rayuwa ba fankama ko jahilci ya sanya suke kin namiji ba, wasu ma saboda wahalarvrayuwa da suka fuskanta a lokacin aure ko hulɗarsu; mussaman bayan sun fitar kutsu ta rayuwa. Sai dai hangen dala, ba shiga Kano ba.

Duk yadda matan bariki, ‘yan zamani da suke tinƙaho da Ilmi, wayewa ko kuɗi za su yi wa mazaje kuɗin goro; tabbata wasu daga cikinsu sunavda ɓoyayyun mazajen da ke yi musu hidima ko ta hulɗa ko ta aiki ko ma ta biyan buƙatunsu.

Wasu matan ma har girki suke yi suna kai wa wasu mazajen duk da irin cin fuskar da suke yi wa jinsinsu a hanyoyin sadarwa ko gabatar da ƙasidu a tarruruka.

Muhimmiyar shawara gare mu baki ɗaya, mu mutunta tare da girmama iyakokin juna, tare da tsare amana da gaskiya a kan zamantakewa tsakanin ma’aurata da ma hulɗa da juna.

Ba wata mace, mai lafiya da kuzari da za ta rayu babu namiji tare da ita; muddin har dai ta samu tarbiyya ta iyaye da kakanni.

Fata ɗaya da ya dace mu yi wa waɗanan matan, Allah Ya aza su a kan hanyar haƙuri da fahimtar addini da tarbiyya ta mutunci na rayuwa don kada su shiga wani mummunan yanayi na rayuwa.

~~~~~~~
Malam Yusuf Dingyadi, marubuci ne kuma ɗan jarida. Ya aiko muƙalar nan daga Sakkwato.
~~~~~~~

Previous Post

Jan Hankali Ga Matasan Soshalmidiya

Next Post

Na Wallafa Littattafai 89 A Shekara 25 – Sadiya Yakasai

Related Posts

Shin Wai Akwai So? (1)
Dausayin Kauna

Shin Wai Akwai So? (1)

June 5, 2025
MENE NE SO?
Dausayin Kauna

MENE NE SO?

April 27, 2025
KANA SON FAHIMTAR MATA?
Dausayin Kauna

KANA SON FAHIMTAR MATA?

November 9, 2023
Next Post
Na Wallafa Littattafai 89 A Shekara 25 – Sadiya Yakasai

Na Wallafa Littattafai 89 A Shekara 25 - Sadiya Yakasai

Comments 1

  1. Guna niyoss pkm says:
    7 months ago

    Sheguba kuma mune dawainiyarsu takomai ma Abu yana faruwa kanmu zasuyo

    Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (1)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (1)

December 26, 2025

Bakan Gizo

August 27, 2023
Littafin Tunawa Da Ɗanbarno: Ana Gayyatar Marubuta

Littafin Tunawa Da Ɗanbarno: Ana Gayyatar Marubuta

July 3, 2023
Ɗaliban Kebbi Sun Shaƙi Iskar ‘Yanci

Ɗaliban Kebbi Sun Shaƙi Iskar ‘Yanci

November 25, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)
  • Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
  • Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.