Daga Bashir Yahuza Malumfashi
~~~~~~~
Idan kana neman marubucin Hausa da ke koyi sau da ƙafa da salon marigayi Abubakar Imam a wannan zamanin, to idan ka ga Zakariyya Haruna Ɗanladi sai ka shafa fatiha. Idan ka ɗauki littafinsa na TEKUN LABARAI kaɗai ya ishe ka misali? Marubuci ne da ya haɗa hulunan hazaƙa iri-iri. Marubucin ƙirƙira ne, mai barkwanci ne, ƙwararren Akawu ne, kamar kuma yadda ya kasance MAYEN KWAMFUTA, wanda ya naƙalci saddabarunta iri-iri. Jaridar TASKAR GIZAGO ta tattauna da shi, inda ya bayyana al’amura masu yawa game da harkar rubutu da marubuta.
~~~~~~~
TG: Kana ɗaya daga cikin marubutan Hausa a wanann zamani. Ko za ka gaya mana tarihinka a taƙaice?
ZAKARIYYA: Assalamu alaikum. Sunana dai Zakariyya Haruna, wanda ake wa laƙabi da Ɗanladi. An haife ni ne a Jihar Kano, Unguwar Gyaɗi-Gyaɗi, ranar 12 ga Yuli, 1981.
Na yi karatun zamani da na Muhammadiyya daidai gwargwado. Ina da matakin ilimi na Digiri Na Biyu a Fannin Gudanar da Kasuwanci (Master of Business Administration). Haka kuma ina da shaidar ƙwarewa ta Cikakken Akawu (Associate Chartered Accountant) kuma mamba na Ƙungiyar Ƙwararrun Akantoci ta Najeriya (Institute of Chartered Accountants of Nigeria – ICAN).

Ina satifiket da dama na ɓangaren rubutu da nazari da na manhajojin kwamfuta da sauransu. Suna da dama waɗannan.
TG: Tun yaushe ka fara rubutu kuma mene ne ya ja ra’ayinka ga harkar rubuce-rubuce?
ZAKARIYYA: Rubutu, na jima ina taɓawa. Tun lokacin muna firamare, kasancewa ta mai son karatu da sauraron rediyo da sauran labarun almara da na hikayoyi da sauransu. Haka dai sannu a hankali har mai karatu ya rikiɗe zuwa marubuci. Kodayake rubutun da nake ganin ya saka ni a gwadaben marubuci, shi ne wani littafi da na rubutu mai suna Furar Danƙo a shekara ta 2002. Daga kansa kuwa na ci gaba da rubutu iri daban-daban.
TG: Ya zuwa yanzu, littattafai nawa ka rubuta? Guda nawa aka buga a littafin takarda kuma nawa ka buga a intanet?
ZAKARIYYA: Kusan kullum ina rubutu. Ina rubuta labarin ƙirƙira a intanet. Sai dai littatafan da na rubuta cikakku dukaduka goma 11 ne. Daga ciki an wallafa guda 3 rak, watau Saura Ƙiris, Tekun Labarai da kuma Ɓarayin Zamani. Ana samun Tekun Labarai a shafukan sayar da littattafai na Okada da na Konga. Shi kuwa Ɓarayin Zamani ana iya samun shi kyauta a gidan archive.org. Na sake shi kyauta ne saboda jama’a su karanta su ƙaru da ilimin sanin hanyoyin kare kansu daga maha’intan da ke cutar mutane ta intanet. Kuma Alhamdu lillahi kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
Baya ga cikakkun littattafai, na rubuta gajerun labaru masu ɗimbin yawa. Suna iya kai wa ɗari da ɗoriya. Waɗannan gajerun labarun ina sakinsu ne a shafukan Intanet da sauran wurare, watau kamar dalilin gasa ko haɗakar rubutu da sauransu.
TG: Waɗanne irin matsaloli kake fuskanta a matsayinka na marubuci?
ZAKARIYYA: Yawancin rubuce-rubucena ina yin su bisa son rai ne. Wani lokaci yana iya zama tamkar bahaya. Idan ya taso wajibi ne a fitar da shi. Kuma ka san cewar aikin sa kai ya fi bauta ciwo. Don haka, koda akwai wasu matsalolin akan rufe ido a yi abin da ya dace.
To amma yawancin matsalolin marubuta sun haɗa da rashin lokacin aiwatar da bincike da rashin goyon bayan wasu daga al’umma da kuma matsalar kasuwa. Wanda idan marubuci don samun kasuwa yake a halin yanzu, to sai dai ya ɗora hannu a ka kurum. Muna fatan samun warwarewar matsalolin da suka baibaye marubuta nan ba da jimawa ba.
ZAKARIYYA: Tun daga fara rubutu, waɗanne irin nasarori ka samu ko kuma akasin su?
ZAKARIYYA: Nasarorin suna da ɗimbin yawa da gaske. Rubutu ya sa na san mutane da yawa ciki da wajen ƙasar nan. Haka nan na shiga gasar rubutu da yawa. Na yi nasara a cikinsu da dama. Aƙalla na shiga gasanni da suka kai 10 kuma na yi fice a mafi yawancinsu.
Misali, Gasar Duniyar Marubuta a 2013. Na yi na ɗaya a ɓangaren Wasan Kwaikwayo. Gasar Gusau Institute na yi na biyu a 2018. Gasar Pleasant Library na yi na uku a 2020, da sauransu.
Na samu kyaututtuka da dama ta silar rubutu.
Sannan ina aiki da mutane da dama duk albarkacin rubutu.
TG: A harkar rubuce-rubuce, waɗanne marubuta ne gwanayenka, da kake koyi da rubutunsu?
ZAKARIYYA: Gwanayena a rubutu suna da dama. Kusan duk wanda na karanta littafinsa ko wani rubutu nasa, nakan ɗosani wani abu daga gare shi yadda zan kattaba nawa idan buƙatar hakan ta taso. To amma manya daga ciki sun haɗa da Farfesa Ibrahim Malumfashi da Farfesa Yusuf Adamu da Bala Anas Babinlata da Ado Ahmad Gidan Dabino da Nazir Adam Salihi da Maimuna Idris Beli da kuma Rahama Abdulmajid.
A fannin waƙa da wasan kwaikwayo kuwa, Malam Nasiru G. Ahmad shi ne alƙiblata. Haka kuma, na kan yawaita aika masa rubuce-rubucena yana mini gyara, musamman ta fuskar salo da sarrafa harshe da kuma ƙa’idojin rubutu.
Shi kuwa marigayi Abubakar Imam, na ɗauke shi wata alƙibla da nake waiwaya duk lokacin da zan yi rubutun gajeren labari. Misali, littafin Tekun Labarai, na ari wani salo daga littafin Magana Jari Ce wajen ƙulla gajerun labaru cikin uwar labari ta yadda mai karatu zai yi ta shiga da fita cikin labarai ba tare da an ƙarƙare wanda aka fara tun farko ba.
TG: Ya zuwa yanzu wane sabon littafi kake kan rubutawa kuma zuwa yaushe zai fita ga al’umma?
ZAKARIYYA: Littatafin Tekun Labarai na uku da na huɗu nake son fitarwa ba da jimawa ba. Tuni na ƙulla zaruruwan labaran na kuma samar musu da take. Abin da ya rage kurum shi ne samun zama in rubuta su yadda ya dace. Waɗannan littatafai, ci gaban gajerun labaran littafi na ɗaya da biyu ne. Kowanne littafi akwai irin salon da ke cikinsa. Littafi na ɗaya ɗan sarki ne ke bai wa Sarki labari, littafi na biyu Waziran Sarki ne ke ba wa Sarki. Littafi na uku kuwa mutanen gari ne ke bai wa Sarki labari. Littafi na huɗu kuma mutanen gari ne ke bai wa junansu labari.
Bayan Tekun Labarai na uku da huɗu kuma akwai wani littafi mai suna Hanyar Jidda. Labari ne a kan wata ƙirƙirarriyar tafiya daga tashar motar Unguwa Uku zuwa Jidda da ke Saudi Arabiya, wadda tauraron labarin ya yi cikin shekaru takwas. Labarin na ƙunshe da abubuwan mamaki da tarihi da al’adu da soyayya da sauransu. Na rubuta labarin ne a bisa abin da ya faru a Sudan a shekarar 2006, tsakanin Gwamnatin Sudan da ‘yan Janjawid a yankin Darfur. In sha Allahu ba da jimawa ba za su fito.
TG: Wasu marubuta sun koma rubutun fim, ko kai ma kana da shirin rubuta wani littafi na faɗakarwa da za a maida zuwa fim?
ZAKARIYYA: Rubutun fim musamman wanda ba naka ba. Ma’ana, kai ne marubucin kuma kai ne Furodusa kamar yadda Ado Gidan Dabino MON ke yi a Daƙiƙa Talatin. In dai ba haka ba, to wajibi ne ka sadaukar da lokacinka kacokan, domin biya wa daraktoci da furodusoshi buƙatunsu. A halin yanzu ni ba ni da cikakken lokacin rubuta fim, musamman irin gaggawar da ake yi da azazazzalar masu rubutun da su yi su gama da gaggawa.
Kada ka manta. Ina aikin Akawu, wanda shi ma yana jan lokaci, ga kuma aikin harhaɗa manhajar kwanfuta (programming). Duk da haka, wasu na zuwa wajena neman shawarwari ko gyara a wasu rubuce-rubucen na fim. Nakan bayar da gwargwadon gudummuwar da ta dace idan an buƙaci haka.
TG: Mene ne babban burinka dangane da rubutu?
ZAKARIYYA: Ina da buri mai girma dangane da rubutu musamman cikin harshen Hausa. Ina fatan rubutun Hausa ya zama ya mamaye duniya ta kafafen intanet. Ya zamana an samar da manyan dandamalai kamar su Amazon KDP da su Watpad da Webnovel da sauransu.
Kuma Alhamdu lillahi, ya zuwa yanzu akwai yunƙuri a ciki da wajen ƙasar Hausa dangane da wannan manufa. Ni kaina ina daga cikin wasu tafiyoyin da ake wannan shirin. Ɗaya daga ciki kuwa, wata babbar ƙungiya ce da ke ƙoƙarin zamantar da harsunan Afirka. Sun ɗauki Hausa da Siwahili da kuma Bantu a matsayin waɗanda za a fara da su. Aikin da ake yi yanzu haka, sun ce zai ɗauki kimanin shekara guda ana yi. Ina fatan yadda aka fara da ni za a kammala da ni cikin nasara.
TG: Ko kana da wani kira ga gwamnati da marubuta ‘yan uwanka da kuma al’umma masu karanta littattafanka?
ZAKARIYYA: Kira ga gwamnatoci shi ne, kada a manta mafari. Marubuta su ne mafarin ci gaban adabi. Yadda ake yi musu shakulatin ɓangaro a wannan lokaci daidai yake da an ci moriyar ganga an jefar da kwaurenta. Ya kamata a ɓullo da sababbin hanyoyin ƙarfafa gwiwar marubuta yadda hazaƙarsu za ta ci gaba da kaifafa, su riƙa zaƙulo hanyoyin da za a warware matsalolin Arewaci da ma ƙasar Najeriya baki ɗaya.
Haka kuma gwamnatoci na iya kai wa marubuta ɗauki wajen tallafa musu da duk abin da ya dace domin su wallafa rubuce-rubucensu kuma su ci riba. Ba kamar yanzu ba da marubuta ke ta faɗi tashi suna aiki kan jiki kan ƙarfi amma haƙa ya kasa cin ma ruwa ta fuskar kasuwancin littatafan.
Marubuta ‘yan uwana kuwa, haɗin kai wajibi ne. Haɗin kai shi ne tushen nasara da isuwa ga biyan buƙata. Manyan marubuta su ci gaba da haƙurin tarbiyyantar da mu ƙanana ta hanyar shawarwari da ƙarfafa gwiwa. Mu kuwa ƙananan marubuta, wajibi ne mu kasance masu ladabi da biyayya da girmama na gaba. Ta haka ne burin da muke da shi na sauya alƙiblar rubutu zuwa na zamani zai kai ga gaci.













