• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, March 8, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Addini

Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

Daga Wali Ɗanmasani

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 22, 2023
in Addini
0
Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka
742
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Daga Fatuhu Mustapha

A tsakanin shekarun 1980 zuwa 1983, wata salon waƙa da labari ta karaɗe dukkanin lokuna da saƙuna na ƙasar Hausa da aka fi sani da Wakar Yaƙin Tabuka. Wannan waƙa an ɗauki salon wata tsohuwar waƙa ce ta Shehu Muhammad al Kashnawi al Masani da aka fi sani da Wali Ɗanmsani da ya kira ta da  Waƙar Yaƙin Badar.

Related posts

RAMADAN KARIM: 19-1447

RAMADAN KARIM: 19-1447

March 8, 2026
RAMADAN KARIM: 18-1447

RAMADAN KARIM: 18-1447

March 7, 2026

Ba dai taƙamaiman yaushe aka yi waƙar, kuma jami’an yaɗa irin waɗannan kasakasai irin su Musa na Saleh da su Rabi’u BK da Malam Ƙalarawi duka ba su iya bayar da wani gamsasshen bayani a kan waye ya yi waƙar ba.

Tun a wannan lokaci aka riƙa maganganu a kan gaskiyar abin da waƙar ta ƙunsa. Wasu na ganin kawai shaci faɗi ne amma abin bai faru ba, wasu kuma suna ganin hakan ya faru. Ba na mantawa, an taɓa saka wa Malam Aminuddeen Abubakar wakar, inda ya nuna farin cikinsa da abin, amma ya yi ƙarin haske da cewa, ba haka abin ya faru ba, amma abu ne mai kyau domin a zaburar da mutane a kuma nuna musu irin gwagwarmayar da aka sha wurin kafa Musulunci. Wannan ƙarin haske na Malam Aminuddeen (Allah Ya ji ƙan sa), shi ne ya kawo ƙarshen cece-kucen da aka yi a kan waƙar.

To amma me waƙar ta ƙunsa? Wannan waƙa mai haɗe da labari, ta ƙunshi gwagwarmayar da aka yi ne, tsakanin dakarun rundunar Musulunci ƙarƙashin jagorancin mai gayya mai aiki, Manzon Allah SallalLahu alaihi wa sallam, da dakarun tsohuwar Daular Byzantine. Kuma an fita yakin ne a lokacin hijira na da shekara 9, wannan kuma shi ne yaƙi na ƙarshe da Manzon Allah ya fita a rayuwarsa. Ya fita da runduna mafi girma da Musulunci ya taɓa tarawa a zamaninsa, domin masana sun ce ya fita da sama da mutum 30,000.

A wannan fita dai, shi ne karo na farko da ya bar Sayyadi Aliyu a gida, inda ya umarce shi da ya zama wakilinsa a Madina, sannan kuma har ya je ya dawo bai gamu da rundunar Byzantine ba, wanda hakan ya nuna ba a gwabza yaƙi ba. Sai dai ya shafe kimanin sama da wata guda a wurin, yana ƙoƙarin janyo hankulan shugabannin al’ummomin wurin da su amince su bai wa Musulunci haɗin kai.

Da yawa masana na ganin, Daular Byzantine ta karaya ne tun bayan da ta samu labarin irin fitar da Musulmi suka yi, da kuma irin tarin rundunar da suka fito da ita.

Tambaya ta biyu shi ita ce, shin abin da aka faɗa a waƙar, haka yake ko kuwa ba haka yake ba? Shin in haka yake, to tun da ba a yi yaƙin ba, ya abin ya faru? A ina abin ya faru? Ya aka yi Sayyadi Ali KarramalLahu wajahahu ya samu kansa a labarin? Bari mu amsa wannan tambayar domin mu warware matsalar:

Da farko dai ya kamata a sani, akwai nason gaskiya a wannan waƙa tasa, sai dai abin da ya faɗa, kaso 10 ne gaskiya, kaso 90 duk ƙari ne kawai, domin dai a nuna irin sadaukantar da kai na dakarun Musulunci. Domin ko shakka babu, an taɓa fita yaƙi da aka yi ɗauki ba daɗi da Sayyadi Ali a matsayin babban kwamandan dakarun Musulunci da wani babban kwamanda na Yahudawa da ake kira da Marhab bin Abi Zainab. Wannan suna Marhab shi ne ƙila bai ji sosai ba, sai ya kira shi da Ƙaura Ɗan Marwana. Wani abin sha’awa game da yadda ya wassafa waki’ar shi ne, yadda ya hausantar da abin, ya sanya kirari irin na Hausa, ya ɗauko muƙamai irin na dakarun ƙasar Hausa, ya sanya wa wasu dakaru da ya yi amfani da su a yaƙin, musamman Ƙaura Ɗan Marwana (Marhab bin Abu Zainab). Kowa ya san Ƙaura na nufin wani shahararren kwamandan yaƙi, kamar irin su Ƙaura Ama, Ƙaura Hasau na Maraɗi da sauransu.

Wannan yaƙi an yi shi shekara ta 7 bayan hijira, kuma shi ne yaƙin da ya kulle wa musulmi ƙofar talauci, ya ɗaga tattalin arzikin Madina. Har ma Nana A’isha (ra) tana cewa, “Musulmi ba su san yalwa da tarin arziki ba, sai bayan da aka yi Yaƙin Khaibar.” Wannan yaƙi shi ake kira da Yaƙin Khaibar!

Khaibar wani babban gari ne mai ƙarfin arziki da Yahudawan da suka baro Daular Rome suka kafa, kimanin kilomita 150 yamma da birnin Madina. Gari ne da ke da dausayi da dama a tare da shi, kuma ya haɓaka fiye da kowanne gari a jazirar Larabawa saboda arzikin noma da suke da shi. Kuma shi ne fito-na-fito na farko da ya afku a tsakanin Musulunci da Yahudawa. Wannan ya sanya nasarar da Musulunci ya samu a wannan yaƙi, ta buɗe ƙofofin wadata da ƙaruwar arziki a tsakanin Musulmi.

A wannan yaƙi Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallam) ya fita ne da soja 1600, a yayin da su kuma Yahudawa suke da soja 10,000 da kuma ‘yan haɗin gwiwarsu, wato Bani Gattafan, su 4000. Wato dai soja 14,000. Baya ga wannan, Yahudawa sun fi Musulmi ƙarfin tattalin arziki nesa ba kusa ba, sannan kuma suna da ganuwa da babu irinta duk faɗin jazirar Larabawa, wanda hakan ya sanya cin su da yaƙi, sai mai ƙarfin imani.

A haka rundunar Musulunci ta fita, ta kuma gwabza yaƙi da ta Yahudawa, sai dai masana tarihi sun tabbatar da cewa, a wannan fita, ba a fita da Aliyu Ɗan Abi Talib ba, saboda yana fama da ciwon ido. To amma saboda ƙarfin mayaƙa da yawa ga kuma ƙarfin arziki, ya sanya cin su da yaƙi ya faskara.

Masana sun ce akwai dalilin da ya sanya Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallam) bai fita da ƙatuwar runduna ba, ya yi haka ne saboda ya shammace su ya kai musu samame, ba tare da sun ankara ba. Daga ɓangaren Yahudawa, sun raina rundunar da Musulmi suka fito da ita, don haka suka ƙi haɗe kansu wuri ɗaya, wanda haka ya bai wa Musulmi damar yi musu ɗauki ɗaiɗai.

Inda aka shata daga, shi ne wurin yaƙar babban garinsu da ake kira Ƙamus, wanda shi ne mazaunar da manyan shugabannin suke ciki. Da farko dai an tura Muhammad bin Maslama, wani gogaggen kwamandan yaƙi, to amma bai samu nasarar shiga garin ba. Bayan ya komo sai aka tura Sayyadi Abubakar. Shi ma bai yi nasara ba, aka tura Sayyadi Umar, shi ma Allah bai yi zai iya buɗe garin ba.

Masana sun ce an shafe kwanaki 19 ana wannan batakashi amma babu nasara, kuma dukkanin ɓangarorin sun fara galabaita saboda rashin ruwa. Daga ɓangaren Musulmi kuma akwai ƙarancin abinci. Hakan ya sanya dole Musulmi su nemi wata hanya da za su kammala wannan yaƙi da suka fara.

A wannan lokacin ne aka nemi a samu wani sabon kwamnadan da ake ganin zai iya yin ta ta ƙare. Wannan shi ne dalilin da yan sanya Manzon Allah ya zaɓo Sayyadi Ali da ya jagoranci rundunar, domin a yi ta ta ƙare. Kuma a wannan gumurzu ne aka ce sun yi karon battar ƙarfe da Ƙaura Ɗan Marwana, wato Marhab bin Abi Zainab. Wanda aka ce uwarsa wata shahararriyar hatsabibiya ce da ta ƙware a ilmin tsafin nan na Kabbala. Kuma ita ce mai waƙar yake ambata a wannan faifai nasa.

Ambatar su Sayyadi Abubakar da Umar (RadhiyalLahu Taala Anhu) da ya yi, haka yake. Sun shiga fagen yaki, amma sai dai ya yi ƙarin gishiri da ajino har ma da onga a waƙar. Haka kuma babu wata shaida ta cewa shi Sarkin yana dara. Abin da ya tabbata shi ne, ya yi yunƙurin haɗa kai da sauran ƙabilun Yahudawa da ke Arebiya domin su yaƙi Musulunci, hakan ya sanya Musulmi suka yi musu riga malam masallaci, suka yi musu ƙofar rago.

An samu saɓani a kan waye ya yi daga da Ƙaura Ɗan Marwana. Ibni Hisham ya dage a kan Muhammad Masalama ne ya kashe shi, amma sauran Malaman Tarihi da na Hadisi duk sun ruwaito cewa, Ali Ɗan Abi Talib ne ya kashe shi. An ce a wannan daga sai da ya karya garkuwar Sayyadi Ali, sai wata ƙofa ya ɗauka ya yi garkuwa da ita. Sannan kuma Marhab ya yi nasarar saran Sayyadi Ali a ka, ya zama mayaki na biyu da ya taɓa yi masa rauni tun bayan raunin da Amr Ɗan Abi Wudd ya yi masa a Yaƙin Hunain. In kuwa haka ne, to ko shakka babu, wannan daga da Ali Ɗan Abi Talib aka yi, ba da Muhammadu bin Maslama ba.

To amma me ya sa Tabuka ta fi Khaybar shahara a tsakanin mutanen ƙasar Hausa?
Na farko dai saboda Musulunci bai taɓa haɗa runduna kamar wannan ba a zamanin Manzon Allah (SallalLahu alaihi wa sallam).

Na biyu Tabuka na nan har yanzu, amma Khaybar babu ita, tun bayan da Sayyadi Umar ya fasa su, ya rusa garin a zamanin mulkinsa.

Na uku, sunan Tabuka ya fi kama da Hausa fiye da sunan Khaybar, don haka Bahaushe zai fi sabawa da ya kira sunan fiye da wancan na Larabci.

Na huɗu, akwai rashin wadatar ilmin tarihi a tattare da wanda ya yi waƙar. Da alama ba malami ba ne na fiƙihu ko na fannoni, kawai dai almajiri ne da ya tsinci labarin kuma abin ya ba shi sha’awa.

Na biyar, irin wannan abubuwa ne da suke faruwa a wurare da ilmin addini bai wadata ba. Za ka samu malaman turmi da ke yaɗa irin waɗannan, saboda kishinsu da addini ba don suna da wani ƙwaƙƙwaran ilmi ba.

Daga ƙarshe, abin da ya samu wannan waƙa, shi ne dai ya samu waƙar Yaƙin Badara da aka ce Wali Ɗanmsani ne ya rubuta, domin ita ma, mafi akasarin abin da aka ce an yi a ciki, sun faru ne a Yaƙin Uhud ba Yaƙin Badar ba.

Da wannan masana irin Malam Ibrahim Yaro Yahaya suka musa cewa Ɗanmasani ne ya rubuta waccan waƙar, saboda sun nuni da cewa, ilmin Wali Ɗanmasani ya wuce a ce bai iya bambance Yaƙin Badar Badr da Yaƙin Uhud.

Wannan shi ne abin da na sani a game da Waƙar Yaƙin Tabuka

Previous Post

Ƙarin Albashi: ‘Yan Siyasa Za Su Fara Girbi Cikin Damina

Next Post

Janar Magashi Bai Mutu Ba

Related Posts

RAMADAN KARIM: 19-1447
Addini

RAMADAN KARIM: 19-1447

March 8, 2026
RAMADAN KARIM: 18-1447
Addini

RAMADAN KARIM: 18-1447

March 7, 2026
RAMADAN KARIM: 17-1447
Addini

RAMADAN KARIM: 17-1447

March 6, 2026
Next Post
Janar Magashi Bai Mutu Ba

Janar Magashi Bai Mutu Ba

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Gargaɗin Amurka kan Nijeriya na tada hankulan jama’a, kuma ya na yin illa ga tattalin arzikin ƙasa – Minista

Minista Ya Buƙaci Masu Sana’ar Talla A Kafafen Yaɗa Labarai Su Faɗakar Da Jama’a Game Da Shirye-Shiryen Tattalin Arziki Na Gwamnatin Tinubu

December 9, 2023
Nigerian Politicians: Leaders or Looters?

Nigerian Politicians: Leaders or Looters?

June 8, 2024
Dr. Buratai in Ibadan to Deliver Paper on National Security Tomorrow

Dr. Buratai in Ibadan to Deliver Paper on National Security Tomorrow

November 2, 2023
Hajj 2023: Uba Sani, Arrigassiyu bag awards

Hajj 2023: Uba Sani, Arrigassiyu bag awards

September 24, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • RAMADAN KARIM: 19-1447
  • FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)
  • RAMADAN KARIM: 18-1447

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

RAMADAN KARIM: 19-1447

RAMADAN KARIM: 19-1447

March 8, 2026
FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

FITILAR MATASA – Zannan Galadima (3)

March 7, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.