• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, May 11, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Kuskure Kan Ingilishi: Wane Ne Ke Son Wulaƙanta Gwamnan Kano?

webmaster by webmaster
June 3, 2023
in Gizago
5
Kuskure Kan Ingilishi: Wane Ne Ke Son Wulaƙanta Gwamnan Kano?

Gwamna Abba Kabir Yusuf

269
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Cikin ‘yan kwanakin nan biyu, na lura da yadda wasu suke ta zuzuta tozarci ga sabon Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf saboda a fahimtarsu ya tafka kurakurai a yayin gabatar da jawabinsa da Ingilishi.

Abin da ma ya ƙara ba ni takaici, wasu ma fa ko Ingilishin ma na kirki ba su iya ba, kawai kiɗanta-na-jiyo ne, amma suka haƙiƙice suna yi wa Gwamna dariya da shegantaka. Ta kai ga wai har ana buga tambarin kalmomin turanci ga huluna da singileti. Haba jama’a, me yai zafi haka?

Shin wai me mutane suka ɗauki Ingilishi ne? Me ya sa ma muke guje wa magana da harshenmu da Allah Ya albarkace mu da shi? Me ya sa idan mutum ya yi kuskure a magana da harshenmu na gado, ba a kulawa amma da zarar mutum ya yi kuskure a yaren da ba nasa ba, sai a hayayyaƙo masa da tozarci?

Related posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026

Ni a ganina, lokaci ya yi da shugabanninmu za su fara martaba harsunanmu, su riƙa amfani da Hausa a duk lokacin da za su gabatar da jawabi ga al’ummarmu. Domin dai amfanin jawabin shi ne domin isar da saƙon da zai amfani al’umma. To ina amfanin mutum ya yi ta zuba Turanci alhali kaɗan ne daga mutanen da yake magana da su za su fahimta?

 

Lokaci ya yi da za mu zama ‘yantattu, mu ‘yanto kanmu daga bautar Turawa da Turanci. Lokaci ya yi da za mu fuskanci gaskiya da gaskiya. Naka sai naka, domin kuwa babu yadda wani shugaba a Amurka ko a Ingila ko a Faransa da zai kalli mutanensa ya ce zai yi masu jawabi da Hausa ko Ibo ko Yarabanci. To mu me zai sa mu raina kanmu?

Kashi 100 cikin 100 na al’ummar Kano da Hausa suke magana kuma da shi suke mu’amala da juna. To ina hikima a ce dole sai da Turanci shugabansu zai yi masu jawabi?

Na bi TURANCI da gudun famfalaƙi!

——

© Bashir Yahuza Malumfashi

Asabar 14-11-1444 (Hijriyya)

03-06-2023 (Miladiyya)

–

Previous Post

Tallafin Mai

Next Post

Wawason Dukiyar Al’umma: Gwamnatin Zamfara Ta Nemi Ba’asin Tsohon Gwamna Matawalle

Related Posts

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi
Gizago

Rantsuwa Da Ƙur’ani: Martani Ga Shugaban Hausawan Bogi

April 20, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Next Post
Wawason Dukiyar Al’umma: Gwamnatin Zamfara Ta Nemi Ba’asin Tsohon Gwamna Matawalle

Wawason Dukiyar Al'umma: Gwamnatin Zamfara Ta Nemi Ba'asin Tsohon Gwamna Matawalle

Comments 5

  1. Sulaiman Idris Soa says:
    3 years ago

    Allah ya karawa Jagoran Gizagawan Nigeria Lafiya

    Reply
    • Bashir Yahuza Malumfashi says:
      3 years ago

      Amin Amin Ya Allah. Jazakallahu khairan!

      Reply
  2. Dodo says:
    3 years ago

    Salallamin Salamatun Silamen Sakkwato. Barman da kokari

    Reply
    • Bashir Yahuza Malumfashi says:
      3 years ago

      Dodorido a kan shorido. Muna godiya. Mishodi.

      Reply
    • Bashir Yahuza Malumfashi says:
      3 years ago

      Barka kadai Dodo

      Reply

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (4)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (4)

February 3, 2026
A Review of Philip Chikwuedo Asiodu: A Legacy of Dedication and Service

A Review of Philip Chikwuedo Asiodu: A Legacy of Dedication and Service

January 11, 2026
ALLAH YA JI ƘAN DSP ABBA ƊANMALAM

ALLAH YA JI ƘAN DSP ABBA ƊANMALAM

December 21, 2024
Hassan Maina Kaina Ya Zama Babban Editan Africa Radio International Na Farko

Hassan Maina Kaina Ya Zama Babban Editan Africa Radio International Na Farko

October 9, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi
  • Yan ta’addan Daji Kafirai Ne – Sarkin Musulmi
  • Farewell Ashaka

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

Asibitoci A Najeriya Ba Su Da Bambanci Da Turakun Dabbobi

May 9, 2026
Yan ta’addan Daji Kafirai Ne  – Sarkin Musulmi

Yan ta’addan Daji Kafirai Ne – Sarkin Musulmi

May 8, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.