Gabatarwa: Cire tallafin mai da sabon Shugaban Ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi, shi ne babban abin da ya ɗauki hankalin al’ummar Najeriya. Kowa maganar yake. Shi kuwa fasihin marubuci, Khalid Imam, sai ya jero waɗannan baitocin):
Ya janye tallafin mai,
Ba shakka kan ya sauka,
Kasafi na kuɗin ƙasarmu,
In ka duba zai bayani.
Kan ya sanya ƙafarsa Daura,
Ya shelanta wa kowa,
Cewa boda da niyya,
Ya kulle kun ji ƙeta.
‘Yan uwansa a nan Arewa,
Ya cuta bai kula ba.
Sun ja daga da ASUU,
Har kotu ya kai ga doka.
“No work no pay” ya ce wai,
Alƙali yai wa doka,
Ya sa guduma ya doka,
A toshe kafa da dama.
Damar motsi da kuka,
Da fafutika da neman,
‘Yanci da haƙƙi na aiki,
Ya toshe kar mu manta.
Tallafin komai idonmu,
Ya cire su kakaf ku duba,
Na lantarki da taki,
Na noma ya cire kaf.
Buhun taki kuɗinsa,
Sai ya ma auren budurwa,
Buhun masara da ƙaura,
Saye sai wane babba.
Har ba ya tausayinmu,
Tallafin shaƙa ta iska,
Wadda kyauta ce ta Jalla,
Ita ce rak bai cire ba.
Ita ɗin ma da da iko,
Zai cire mu saya da tsada,
Jari a wajensa hujja,
Ba ya kishin talaka.
Tafiya ‘yar nan da can yau,
Tsada sam kar a tona,
Sauƙin tafiya guda yau,
Sayyada ka daɓa ka taka.
Sun janye tallafin mai,
Sai su janye har na iska,
Da mu ke shaƙa mu rayu,
In ikon na wajensu .
Matsi wahala dukansu,
Allah zai maganinsu,
Wahala ba ta kashe mu,
Rayuwarmu tana ga Jalla.
Rabbana ka zamo gare mu,
Garkuwa kogin wadata ,
Gatanmu Ilahu Kai ne,
Yau da gobe da jibi gata.
Tallafin jin ƙanKa ba mu,
Mu rayu cikin wadata,
Tallafinka Azimu tabbas,
Na rantse ba kamarsa.
Kunyata su ka ba mu Naka,
Su gan mu a raye tare,
Hidimarmu ta yau da gobe,
Ɗauke mana don Habibu.
Musɗafa angon Khadija,
Na A’isha har da Hafsa,
Fitilar da ta kore ƙarya,
Al-Aminu farin jakada.
Ni Imam Khalid ku shaida,
A nan zan sanya aya.
Komai rintsi Ilahu,
Kar ka juya wuya gare ni.
Ban da kowa ban da Kai ni,
Gatana ba samanKa,
Kai Ka yi ni Ka ban kulawa,
Godiyata ga ta gun Ka.
© Khalid Imam
2/6/2023













