Wata ganawar ƙeƙe-da-ƙeƙe, Shanshani ya gana da matashin nan mai fiƙira, Anarabul Mukhtar Mudi Spikin, dangane da yadda talakkan ƙasar nan ke neman dawwama a cikin ƙukumi. Ga yadda ta kwaranye a tsakaninsu:
Shanshani: Anarabil Spikin, me za ka ce game da tsarin gudanuwar mulkin ƙasar nan?
Spikin: Tsari ne da aka gina shi a kan azabtar da talakan ƙasar nan, wanda fitarsa sai dai Allah kurum.
Shanshani: Ban gane ba, kamar yaya za ka ce sai dai Allah?
Spikin: E, mana, yanzu dubi yadda Gwamnati ta cire tallafin mai don kuɗaɗen tallafin sun yi yawa, sannan wanda ake bai wa wannan kuɗaɗen don su kawo man, su na karkatar da shi, su ƙara siyar da shi a tsada, ko su tsallake su siyar da shi a wasu ƙasashen maƙotanmu, sun fi ƙarfin Gwamnati. Don haka ba yadda za ai da su, ba damar a tilasta su, sai dai a cire tallafin kawai, talaka ya gane kurensa.
Shanshani: Kuma haka ne fa. To yaya ke nan?
Spikin: Saurara ka ji kuma, domin haka ma dai a harkar abinci, yanzu ɗauko maƙudan kuɗaɗen da Gwamnati ta ranta wa masu kamfanin shinkafa, wai don mu dogara da kanmu har mu ciyar wa da kanmu, amma ku duba yadda suke tsala kuɗaɗen da har sai ka kasa bambance farashin shinkafar da aka biya wa kuɗin jirgin ruwa daga wata uwa duniya a kawo nan, da kuma wadda ake nomawa a gyara a nan. Kuma ba yadda Gwamnati za ta yi da su! Ko dai tsoron su take ji ko kuma aminanta ne, ko kuma a cikinta suke, don haka dole talaka ne zai sha wahalar biya. An kwashi kuɗinsa, sannan a zarge shi da tsadar abin da aka samu daga kuɗinsa.
Shanshani: Ikon Allah! To a nan abin zai tsaya kuwa?
Spikin: Ina fa abin zai tsaya iya nan? Akwai misalai da dama. A kowace harka a ƙasar nan, in ka lura wasu kawai ake azurtawa, ku kuma kuna ƙara talaucewa. Ɗauko harkar kajin gidan gona da kifi. Sai a tsala kuɗinsu da na abincinsu, sai ka gama ka ga wahalarka ta fi ribar yawa.
Shanshani: Umuhum!
Spikin: Yanzu fa ta kai a ƙasar nan manomi zai yi noma, amma saboda tsadar iri da taki, sai ka ga ba wani abu yake samu da zai iya riƙe shi ba. Ka bincika a kusan kowacce harka za ka ga akwai manya da ke kusa da Gwamnati, ko su ke cikin Gwamnati da su ake nemar wa kuɗi!
Shanshani: Ka ce harkar gwamnati ta koma kamar ƙungiyanci, irin abin da wasu ke kira da MAFIYANCI?
Spikin: To kamar haka ne, domin kullum kuma ƙara tatse talaka ake, da hauhawar farashin kayan masarufi, abinci, man fetur, kuɗin wuta da sauransu. Kuɗaɗen suna ƙara komawa wajensu, su ƙara kuɗancewa, ‘yan ƙasa su ƙara talaucewa.
Shanshani: Wai na ce ba, to yaya ke nan?
Spikin: Ai sai dai addu’a kawai. Iyaka mu dai ce Allah Ya kyauta!













