• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, September 21, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

An Kama ‘Yan Sandan Bogi Da Motoci Biyu Maƙare Da Wiwi

BABBAN LABARI

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
October 2, 2025
in Babban Labari
0
An Kama ‘Yan Sandan Bogi Da Motoci Biyu Maƙare Da Wiwi

'Yan sandan bogi da aka kama da wiwi

82
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

An Kama ‘Yan Sandan Bogi Da Motoci Biyu Maƙare Da Wiwi
Daga Wakilinmu

‘Yan sandan bogi da aka kama da wiwi


                               •••••••
A makon nan ne jami’an sojoji da ke aiki a ƙarƙashin shirin tsaro na musamman mai taken “Operation Lafiya Nakowa” da ke Birget ta 6, a Jihar Taraba, suka kama wasu ‘yan sandan bogi guda biyu, suna tafe da motoci ƙirar Hilux, maƙare da tabar wiwi.

Related posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026

A jawabin manema labarai daga ofishin Laftana Umar Muhammad, Muƙaddashin Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Birget ta 6 ta Rundunar Sojojin Najeriya, ya bayyana cewa sojojin tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar NDLEA ne suka yi nasarar cafke ‘yan sandan na bogi, a sakamakon bayanin sirri da suka samu. Sun kama su ne a Marabar Takum da ke Ƙaramar Hukumar Wukari, Jihar Taraba.

Sojojin da suka yi aikin

Waɗanda aka kama dai an same su ne suna sanye da kayan aikin ‘yan sanda na mobayil, da motocin Toyota Hilux guda biyu cike da abubuwan da ake zargin tabar wiwi ce.

Binciken farko ya nuna cewa dukkan ‘yan sandan na bogi ne. An gano cewa an loda wa motocin tabar wiwi ce a Akure, Jihar Ondo, kuma suna kan hanyarsu ta zuwa Jihar Adamawa ne, a yayin da aka tare su.

Motar Hilux da aka kama

Binciken ya ƙara tabbatar da cewa ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, sunansa Monday George, kuma tsohon jami’in ɗan sanda ne mai muƙamin ASP, wanda aka kora daga aiki kuma shekararsa 71. A yayin da ɗayan kuma sunansa Ezeugo Destiny Uche, mai shekaru 41. Sai dai kuma waɗanda ke cikin motar Hilux ta biyu sun bar ta, suka gudu, a yayin da suka hango sojojin daga nesa.

‘Yan sandan bogi tare da wiwin da suka ɗauko

An ƙwato manyan ɗaurin tabar wiwi guda 1,134 daga motocin biyu. An miƙa duka waɗanda ake zargi da abubuwan da aka ƙwato ga ofishin NDLEA da ke Wukari don ƙarin bincike da gurfanar da su a gaban kotu.
___________

Previous Post

ALLAH YA JI ƘAN HAUWA ƘAMSHI

Next Post

MUHAMMADU (SAW)

Related Posts

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?
Babban Labari

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta
Babban Labari

Ƙauna: Budurwa Mai Bautar Dodo Ta Musulunta

September 3, 2026
KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya
Babban Labari

KATSINA_2026: Bikin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya

August 29, 2026
Next Post
MUHAMMADU (SAW)

MUHAMMADU (SAW)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Za Mu Inganta Rayuwa Da Ayyukan ‘Yan Jarida – Minista Idris

Za Mu Sake Dasa Wa Al’ummar Nijeriya Ɗabi’ar Yarda Da Kalaman Shugabanni – Minista Idris

October 18, 2023
ZAKARAN ADABI: BANKWANA NGUGI

ZAKARAN ADABI: BANKWANA NGUGI

May 30, 2025
Mun Yi Rashi: A Taya Mu Da Addu’a

Mun Yi Rashi: A Taya Mu Da Addu’a

February 7, 2026
Wike Sent Heads of FCT Agencies, Parastatals Packing

Wike Sent Heads of FCT Agencies, Parastatals Packing

September 28, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.